Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wt babi na 19 pp. 167-174
  • Ka Ci Gaba da Faɗan Maganar Allah da Gaba Gaɗi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Ci Gaba da Faɗan Maganar Allah da Gaba Gaɗi
  • Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ban da Dogara ga Namu Ƙarfi
  • Tarihin Wa’azi da Gaba Gaɗi
  • Ka Yi Koyi Da Yesu Ta Yin Wa’azi Da Ƙarfin Zuciya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ka “Faɗi Maganar Allah Da Ƙarfin Zuciya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Masu “Ɗauke Da Albishir Mai Daɗi”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
wt babi na 19 pp. 167-174

Babi Na Goma Sha Tara

Ka Ci Gaba da Faɗan Maganar Allah da Gaba Gaɗi

1. (a) Wace bishara ce almajiran Yesu suka yi shelarta, amma yaya wasu Yahudawa suka yi? (b) Waɗanne tambayoyi za mu iya yi?

KUSAN shekara 2,000 da ta shige, an naɗa Yesu Kristi, Ɗan Allah ya zama Sarki na dukan duniya a nan gaba. An kashe Yesu domin zuga ta magabta na addini, amma Jehovah ya ta da shi daga mutuwa. Yanzu ana iya samun rai na har abada ta wurin Yesu. Amma lokacin da almajiran Yesu suka yi shelar wannan bisharar, sai tsanani ya taso. Aka jefa wasun su cikin kurkuku, har aka yi musu dūka kuma aka dokace su kada su yi magana game da Yesu. (Ayukan Manzanni 4:1-3, 17; 5:17, 18, 40) Menene za su yi? Da me za ka yi? Da ka ci gaba da yin wa’azi da gaba gaɗi?

2. (a) Wane labari na musamman ne ake bukatar shelarsa a zamaninmu? (b) Su wa ke da hakkin yin wa’azin bisharar?

2 A shekara ta 1914, an ɗora Yesu Kristi a kan kujerar sarauta ta sama, na Mulkin Allah, ya yi sarauta ‘tsakanin magabtansa.’ (Zabura 110:2) A gaba kuma, Shaiɗan da aljanunsa an jefo su zuwa duniya. (Ru’ya ta Yohanna 12:1-5, 7-12) Ƙarshen kwanaki na wannan zamani ya soma. Yayin da wannan lokaci ya ƙare, Allah zai kawar da dukan zamanin Shaiɗan. (Daniel 2:44; Matta 24:21) Waɗanda suka tsira za su samu begen rai na har abada a duniya da za ta zama aljanna. Idan ka amshi wannan bisharar, za ka so ka gaya wa wasu. (Matta 24:14) Amma me za ka yi tsammaninsa?

3. (a) Yaya mutane suka aikata wajen saƙon Mulkin? (b) Wace tambaya ce dole mu fuskanta?

3 Yayin da ka yi shelar bisharar Mulkin, wasu za su yi na’am da ita, amma yawanci za su ƙi. (Matta 24:37-39) Wasu za su iya muku ba’a ko kuma yi hamayya da ku. Yesu ya ba da gargaɗi cewa hamayya tana iya fitowa daga naka dangi. (Luka 21:16-19) Tana iya zama daga wajen aikinka ko kuma a makaranta. A wasu ɓangarorin duniya, har gwamnati ma ta sa hani kan Shaidun Jehovah. Idan muka fuskanci irin yanayin nan, za ka so ka ci gaba da yin maganar Allah da gaba gaɗi kuma ka “tsaya da ƙarfi cikin imani”?—1 Korinthiyawa 16:13.

Ban da Dogara ga Namu Ƙarfi

4. (a) Don mu tabbatar mu bayin Allah ne masu aminci, menene ainihi ake bukata? (b) Me ya sa taron Kirista ke da muhimmanci sosai?

4 Abu na musamman a kasancewa bawa mai aminci na Jehovah shi ne ka dogara ga tanadinsa. Ɗaya cikin waɗannan taron ikilisiya ne. Nassosi sun aririce mu kada mu yi banza da su. (Ibraniyawa 10:23-25) Waɗanda suka ci gaba da zama Shaidu masu aminci na Jehovah sun ci gaba da ƙoƙari su kasance a taro da ’yan’uwa masu bauta a kai a kai. A wajen irin wannan taron muna ƙara saninmu na Nassosi. Muna kuma daɗa fahimtar sananniyar gaskiya, kuma muna ƙara wasa hanyoyin da za mu yi amfani da su. Muna jawo kusa kusa da ’yan’uwanmu Kiristoci a haɗaɗɗiyar bauta kuma muna samun ƙarfafa ta yin nufin Allah. Ruhun Jehovah yana tanadin ja-gora ta wurin ikilisiya, kuma ta wurin wannan ruhu ne Yesu yake tsakaninmu.—Matta 18:20; Ru’ya ta Yohanna 3:6.

5. Idan akwai hani kan Shaidun Jehovah, me ake yi game da taro?

5 Kana halartan dukan taro, kuma kana amfani da abin da ka ji aka tattauna? Wasu lokatai, idan akwai hani a kan Shaidun Jehovah, yana sa a yi taron a ƙananan rukuni a gidajen ’yan’uwa. Inda za a yi taron da kuma lokacin ana iya canja su kuma yana iya zama a lokacin da bai dace wajenka ba, ana yin wasu taron cikin dare. Amma duk da wahalar ko kuma haɗarin, ’yan’uwa maza da mata masu aminci suna ƙoƙari ƙwarai su kasance a kowanne taron.

6. Ta yaya za mu nuna muna dogara ga Jehovah, kuma yaya wannan zai taimake mu mu ci gaba da yin magana da gaba gaɗi?

6 Ana nuna dogara ga Jehovah ta wurin zuwa wajensa kullayaumi cikin addu’a daga zuci, muna nuna mun bukaci taimakon Allah. Kana yin haka? Yesu ya yi addu’a a kai a kai lokacin da yake hidimarsa a duniya. (Luka 3:21; 6:12, 13; 22:39-44) Kuma a dare kafin a rataye shi, ya aririci almajiransa: “Ku yi tsaro ku yi addu’a, domin kada ku shiga cikin jaraba.” (Markus 14:38) Idan mun fuskanci rashin son saƙon Mulkin, za mu iya fāɗawa cikin jarabar yin sanyin gwiwa a hidimarmu. Idan mutane sun yi mana ba’a ko kuma sun tsananta mana, za mu iya faɗa cikin jarabar mu ƙi yin wa’azi domin neman mu guje wa matsaloli. Amma idan muka yi addu’a ƙwarai domin ruhun Allah don ya taimake mu mu ci gaba da magana da gaba gaɗi, zai kāre mu daga waɗannan jarraba.—Luka 11:13; Afisawa 6:18-20.

Tarihin Wa’azi da Gaba Gaɗi

7. (a) Me ya sa labarin da ke Ayukan Manzanni ke da amfani gare mu musamman? (b) Ka amsa tambayoyi da aka tanadar a ƙarshen wannan izifi, ka nanata yadda abin da ke ciki zai amfane mu.

7 Labarin da ke cikin littafin Ayukan Manzanni mai amfani na musamman ne ga dukanmu. Yana magana game da yadda manzannin da wasu almajirai na farko—mutane da suke kama da mu—suka sha kan matsaloli kuma suka kasance da gaba gaɗi, shaidun Jehovah masu aminci. Bari mu bincika sashen labarin nan ta wurin tambayoyi da kuma nassosi da aka nuna. A yin haka, ka yi la’akari da yadda kake amfana daga abin da kake karantawa.

Manzannin masu ilimi ne sosai? Ko da me zai faru, su asalinsu marasa tsoro ne? (Yohanna 18:17, 25-27; 20:19; Ayukan Manzanni 4:13)

Me ya taimaki Bitrus ya yi magana da gaba gaɗi a gaban majalisar Yahudawa da suka hukunta Ɗan Allah? (Matta 10:19, 20; Ayukan Manzanni 4:8)

Menene manzannin suka yi na makonni kafin aka kawo su gaban Majalisar? (Ayukan Manzanni 1:14; 2:1, 42)

Yayin da masarauta suka dokaci manzannin su daina wa’azi game da sunan Yesu, yaya Bitrus da Yohanna suka amsa? (Ayukan Manzanni 4:19, 20)

Bayan aka sake su, daga wanene manzannin suka nemi taimako? Sun yi addu’a a daina tsananta su ne, ko kuma me? (Ayukan Manzanni 4:24-31)

Ta wurin me Jehovah ya yi tanadin taimako yayin da ’yan hamayya suka yi ƙoƙarin hana aikin wa’azin? (Ayukan Manzanni 5:17-20)

Ta yaya ne manzannin suka nuna sun fahimci dalilin da aka cece su? (Ayukan Manzanni 5:21, 41, 42)

Har lokacin da almajirai da yawa suka watse saboda tsanani, menene suka ci gaba da yi? (Ayukan Manzanni 8:3, 4; 11:19-21)

8. Waɗanne sakamako na ban mamaki ne ke akwai daga hidimar almajirai na farko, kuma yaya ya shafe mu?

8 Aikin wa’azin bisharar ba banza ba ne. An yi wa almajirai 3,000 baftisma a Fentakos na shekara ta 33 A.Z. “Masu-bada gaskiya kuma suka ƙara daɗuwa ga Ubangiji, taro mai-girma ne na maza da mata.” (Ayukan Manzanni 2:41; 4:4; 5:14) Da shigewar lokaci, har wani mai tsananta wa mutanen Allah, Shawulu na Tarsus, ya zama Kirista kuma yana wa’azin gaskiyar da gaba gaɗi. Aka zo ga saninsa da manzo Bulus. (Galatiyawa 1:22-24) Aikin da aka soma a ƙarni na farko bai tsaya ba. Ya ci gaba sosai cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe kuma ya kai dukan ɓangarorin duniya. Muna da gatar sa hannu ciki, kuma yayin da muke haka, za mu iya koya daga misalin shaidu masu aminci waɗanda suka yi hidima kafin mu.

9. (a) Waɗanne zarafi Bulus ya yi amfani da shi ya yi wa’azi? (b) A waɗanne hanyoyi kake shelar saƙon Mulkin ga wasu?

9 Yayin da Bulus ya koyi gaskiya game da Yesu Kristi, me ya yi? “Nan da nan kuwa ya yi ta wa’azin Yesu . . . , shi Ɗan Allah ne.” (Ayukan Manzanni 9:20) Ya nuna godiya ga alherin Allah dominsa, kuma ya fahimci cewa kowa na bukatar bisharar da shi ya samu. Bulus Bayahude ne, kuma bisa ga al’adar zamanin, ya je majami’u ya yi wa’azi. Ya kuma yi wa’azi gida gida kuma tattauna da mutane a kasuwa. Ya kuma kasance a shirye ya je sababbin yankuna ya yi wa’azin bisharar.—Ayukan Manzanni 17:17; 20:20; Romawa 15:23, 24.

10. (a) Yaya Bulus ya nuna cewa ko da yana da gaba gaɗi, yana da fahimi kuma a yadda yake wa’azi? (b) Ta yaya za mu kasance da irin halayen Bulus yayin da muke wa’azi ga dangi, abokan aiki, ko kuma abokan makaranta?

10 Bulus yana da gaba gaɗi amma kuma yana da fahimi, yadda ya kamata mu kasance mu ma. A wajen Yahudawa ya yi magana a kan alkawura da Allah ya yi ta wurin kakaninsu. A wajen Helenawa ya yi magana game da abubuwan da sun saba da su. A wasu lokatai yana wa’azi a kan yadda shi kansa ya koyi gaskiyar ne. Ya ce: “Ina kuwa yin abu duka sabili da bishara, domin in yi tarayya cikin samunta.”—1 Korinthiyawa 9:20-23; Ayukan Manzanni 22:3-21.

11. (a) Menene Bulus ya yi domin ya guje wa dinga yin arangama da ’yan adawa? (b) A wane lokaci ne cikin hikima za mu yi koyi da misalin Bulus, kuma ta yaya? (c) Daga ina ne ikon yake zuwa domin mu ci gaba da yin magana da gaba gaɗi?

11 Yayin da adawa ta sa Bulus ya je wani waje ya yi wa’azi na ɗan lokaci, ya yi hakan bai nace don ya dinga yin arangama da ’yan adawa ba. (Ayukan Manzanni 14:5-7; 18:5-7; Romawa 12:18) Amma bai taba jin kunyar bisharar ba. (Romawa 1:16) Ko da yake Bulus bai ji daɗin zagi—har da nuna ƙarfi—da ’yan adawa suka yi masa ba, ya ‘yi gaba gaɗi ta wurin Allahnmu’ don ya ci gaba da wa’azi. Ya ce: “Ubangiji ya tsaya wurina, ya kuwa ƙarfafa ni; domin ta wurina shela ta watsu sarai.” (1 Tassalunikawa 2:2; 2 Timothawus 4:17) Shugaban ikilisiyar Kirista, Yesu, yana ci gaba da tanadar da iko da muke bukata don yin aikin da aka annabta domin zamaninmu.—Markus 13:10.

12. Me ke nuna tabbaci na gaba gaɗin Kirista, kuma ta yaya ake iya haka?

12 Muna da kowane dalili na ci gaba da yin maganar Allah da gaba gaɗi yadda Yesu da wasu bayin Allah masu aminci suka yi a ƙarni na farko. Wannan ba ya nufin ƙin nuna damuwa ko kuma tilasta saƙon ga waɗanda ba sa so ba. Amma kada mu yi sanyin gwiwa domin mutane sun ƙi; ko a ce hamayya ta hana mu magana. Kamar Yesu, muna nuni ga Mulkin Allah cewa shi ne gwamnati ta dukan duniya. Muna magana da gaba gaɗi domin muna wakiltan Jehovah, Mamallakin Dukan Halitta, kuma domin saƙon da muke shelarsa ba daga wajenmu ba daga wajensa ne. Kuma ƙaunarmu ga Jehovah ce ta kamata ta motsa mu mu yi masa yabo.—Filibbiyawa 1:27, 28; 1 Tassalunikawa 2:13.

Maimaita Abin da Aka Tattauna

• Me ya sa yake da muhimmanci mu gaya wa kowa saƙon Mulkin yadda zai yiwu, amma me za mu yi tsammaninsa?

• Ta yaya za mu nuna cewa ba mu dogara ga ƙarfinmu a bauta wa Jehovah ba?

• Waɗanne darussa masu girma ne muka koya daga littafin Ayukan Manzanni?

[Hotuna a shafi na 173]

Kamar yadda yake a dā, bayin Jehovah a yau suna maganar Allah da gaba gaɗi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba