Ka Yi Koyi Da Jehovah Yayin Da Kake Renon Yaranka
“Ba dukan iyaye suke wa yaransu horo ba?”—IBRANIYAWA 12:7, Contemporary English Version.
1, 2. Me ya sa iyaye suke wahalar yin renon yaransu a yau?
A WANI bincike da aka yi a Japan ’yan shekaru da suka shige ya nuna cewa rabin mutane da aka gana da su suna ganin hulɗa sosai tsakanin iyaye da yaransu kaɗan ne kawai, kuma iyaye suna ɓata yaransu ainun. A wani bincike a ƙasar kuma, kusan rubu’in mutane da aka gana da su sun yarda cewa ba su san yadda za su yi taɗi da yara ba. Wannan ba kawai a Gabashin Duniya ba ne. “Iyaye daga Canada sun yarda cewa suna shakkar yadda za su kasance iyaye nagari,” rahoton da jaridar The Toronto Star ta bayar ke nan. A ko’ina iyaye suna samunsa da wuya su yi renon yaransu.
2 Me ya sa iyaye suke wahala a renon yaransu? Babban dalili shi ne cewa muna zama cikin “kwanaki na ƙarshe,” kuma “miyagun zamanu” suna nan. (2 Timothawus 3:1) Ƙari ga haka, “tunanin zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa,” in ji Littafi Mai Tsarki. (Farawa 8:21) Matasa musamman sune abinci na Shaiɗan, mai kama da “zaki mai-ruri” da ke kama waɗanda ba su da basira. (1 Bitrus 5:8) Hakika da akwai abubuwan tangarɗa da yawa wa iyaye Kiristoci, sa’ad da suke son su fara renon yaransu “cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afisawa 6:4) Yaya iyaye za su iya taimakon yaransu su yi girma su zama masu bauta wa Jehovah da sun ƙware, da za su iya bambanta “nagarta da mugunta”?—Ibraniyawa 5:14.
3. Me ya sa reno daga iyaye da tsarewa yake da muhimmanci a goyon yara da kyau?
3 Sarki Sulemanu mai hikima ya lura da cewa “wauta tana nan ƙunshe a zuciyar yaro.” (Misalai 13:1; 22:15) Don a cire wautar nan daga zuciyarsu, yara suna bukatar horo mai kyau daga iyayensu. Ko da yake, matasa ba sa farin ciki game da gyaran nan. Hakika, sau da yawa suna ƙi da gargaɗi ko da wanene ya bayar. Saboda haka, dole ne iyaye su koyi su “goyi yaro cikin hanya da za shi bi.” (Misalai 22:6) Idan yara sun bi irin horon nan, zai iya zama musu rai. (Misalai 4:13) Lalle yana da muhimmanci iyaye su san abin da ke ƙunshe cikin renon yaransu!
Abin da Horo Yake Nufi
4. Menene ma’anar “horo” na musamman yadda Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da shi?
4 Domin suna tsoron kada a ce suna zaluntar yara—a jiki, ta maganar baƙi, ko kuma a jiye-jiye—wasu iyaye sun ƙi su hori yaransu. Ba ma bukatar mu ji irin wannan tsoron. Kalmar nan “horo” yadda Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da ita ba ta nufin zalunci ko ƙeta. Kalmar Helenanci don “horo” musamman tana nufin koyarwa, ilimantarwa, gyara, a wasu lokatai kuma, horo sosai cikin ƙauna.
5. Me ya sa yake da amfani a yi la’akari da hanyar Jehovah na yin sha’ani da mutanensa?
5 A yin wannan horon, Jehovah Allah ya bar misali mafi kyau. Da ya gwada Jehovah da uba, manzo Bulus ya rubuta: “Ba dukan iyaye suke wa yaransu horo ba?” . . . Ubanninmu bil Adam suna yi mana horo na ɗan lokaci, kuma suna yin haka yadda suka fi sani. Amma Allah yana yi mana horo don namu amfani, domin yana son mu kasance da tsarki.” (Ibraniyawa 12:7-10, Contemporary English Version) Hakika, Jehovah yana horan mutanensa domin su kasance da tsarki, ko kuma da tsabta. Za mu ƙara koyo sosai game da ba da horo ga yara ta yin la’akari da yadda Jehovah ke koyar da mutanensa.—Kubawar Shari’a 32:4; Matta 7:11; Afisawa 5:1.
Ƙauna—Motsawa Mai Ƙarfi
6. Me ya sa zai iya zama da wuya wa iyaye su yi koyi da ƙaunar Jehovah?
6 “Allah ƙauna ne,” in ji manzo Yohanna. Saboda haka, koyarwa da Jehovah yake tanadinsa ƙauna ce take motsa shi. (1 Yohanna 4:8; Misalai 3:11, 12) Wannan yana nufin cewa iyaye da suke da ƙauna zai zama musu da sauƙi ne su yi koyi da Jehovah a wannan hanyar? Ba haka ba. Ƙaunar Allah mai ƙa’ida ce. Wani da ya malanta Baheleni ya nuna cewa irin ƙaunar nan “ba koyaushe ba ne take daidai da nufin mutum.” Tsotsar zuciya ba ta mallakar Allah. Koyaushe yana la’akari da abin da ya fi kyau da mutanensa.—Ishaya 30:20; 48:17.
7, 8. (a) Wane misali na ƙauna ta ƙa’ida ce Jehovah ya bari a yin sha’ani da mutanensa? (b) Ta yaya iyaye za su yi koyi da Jehovah a taimaka wa yaransu su koyi iya bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki?
7 Ka yi la’akari da ƙaunar da Jehovah ya nuna yayin da yake sha’ani da Isra’ilawa. Musa ya yi amfani da kwatanci mai motsawa don ya kwatanta ƙaunar Jehovah ga al’ummar Isra’ila ƙarama. Mu karanta: “Kamar yadda gaggafa ta kan gyaggyarta sheƙarta, ta kan yi fuffuka bisa cakinta, ta kan buɗe fukafukanta, ta kwashe su, ta ɗauke su bisa kafaɗarta. Ubangiji kaɗai ya bishe [Yakubu].” (Kubawar Shari’a 32:9, 11, 12) Don ta koya wa ’ya’yanta tashi, gaggafa tana ‘gyara sheƙarta,’ tana fuffuka fukafukanta ta aririce su don su tashi. Sa’ad da ’yar tsuntsuwa ta sheƙa, inda da ma daga kan dutse mai tsawo ne, sai uwar ta “yi fuffuka bisa” ’ya’yanta. Idan ’yar tsuntsuwar kamar za ta faɗi ƙasa, sai uwar ta yi wuf ta tsare, ta ɗauke ta ‘bisa kafaɗarta.’ Cikin ƙauna haka, Jehovah ya kula da sabuwar haihuwa, al’ummar Isra’ila. Ya ba wa mutanen Dokar Musa. (Zabura 78:5-7) Sai Allah ya tsare al’ummar da kyau, a shirye yake ya taimake su idan mutanensa sun shiga wahala.
8 Ta yaya iyaye Kirista za su iya yin koyi da ƙaunar Jehovah? Na ɗaya, dole ne su koya wa yaransu ƙa’idodi da mizanai da ke cikin Kalmar Allah. (Kubawar Shari’a 6:4-9) Manufar ita ce a taimaki yaran su koyi tsai da shawara daidai da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ta haka, iyaye masu ƙauna suna fuffuka bisa yaransu kamar yadda yake, suna lura da yadda suke yin amfani da ƙa’idodin da suka koya. Yayin da yaran suke girma kuma suna samun ƙarin ’yanci, iyaye masu kulawa a shirye suke su “faɗā ƙasa” kuma su ‘kwashe yaransu bisa kafaɗarsu’ yayin da akwai haɗari. Wane irin haɗari?
9. Ga wane haɗari ne musamman iyaye masu ƙauna za su lura? Ka ba da misali.
9 Jehovah Allah ya faɗakar da Isra’ilawa game da sakamakon mugun tarayya. (Litafin Lissafi 25:1-18; Ezra 10:10-14) Yin tarayya da mutanen da ba su dace ba haɗari ne da ke ko’ina a yau. (1 Korinthiyawa 15:33) Ya kamata iyaye Kirista su yi koyi da Jehovah a wannan batu. Wata yarinya ’yar shekara 15 mai suna Lisa ta soma son wani yaro da ba shi da ɗabi’a irin ta iyalinta da kuma ta ruhaniya. “Nan da nan iyayena suka ga canji a halina kuma suka damu,” in ji Lisa. “A wasu lokatai sukan yi mini gyara, a wasu kuma, su ƙarfafa ni a hankali.” Suka zauna da Lisa suka saurare ta a hankali, ta haka suka taimake ta ta bi da abin da suka fahimci matsala ce—muradin son tsararta su amince da ita.a
Ku Riƙa Yin Taɗi
10. A waɗanne hanyoyi Jehovah ya bar misali mai kyau a yin magana da Isra’ilawa?
10 Don su yi nasara a renon yara, dole ne iyaye su yi ƙoƙari suna yin taɗi da yaransu. Ko da yake Jehovah ya san abin da ke zuciyarmu, yana ƙarfafa mu mu yi magana da shi. (1 Labarbaru 28:9) Bayan ya ba Isra’ilawan Doka, Jehovah ya naɗa Lawiyawa su koyar da su, sai kuma ya aika da annabawa su sa su tunani kuma su yi musu gyara. Ya kuma kasance a shirye ya saurari addu’o’insu.—2 Labarbaru 17:7-9; Zabura 65:2; Ishaya 1:1-3, 18-20; Irmiya 25:4; Galatiyawa 3:22-24.
11. (a) Ta yaya iyaye za su riƙa sadarwa da kyau tare da yaransu? (b) Me ya sa yake da muhimmanci iyaye su kasance masu sauraro da kyau yayin da suke magana da yaransu?
11 Ta yaya iyaye za su iya yin koyi da Jehovah sa’ad da suke magana da yaransu? Abu na farko duka shi ne, dole su ba su lokaci. Ya kamata iyaye su ma su guji yin amfani da furci na ba’a, irin su, “Shi ke nan kawai? Ca nake wani babban abu ne”; “Maganar banza”; “To, da me ka ke tsammani? Kai yaro ne tukuna.” (Misalai 12:18) Don a ƙarfafa yara su yi magana, iyaye masu hikima suna ƙoƙari su zama masu sauraro da kyau. Iyaye da suka yi banza da yaransu da suke ƙanana yaran za su yi banza da su yayin da suka yi girma. Koyaushe Jehovah a shirye yake ya saurare mutanensa. Kunnuwansa a buɗe suke ga waɗanda suka juya gare shi cikin addu’a da tawali’u.—Zabura 91:15; Irmiya 29:12; Luka 11:9-13.
12. Waɗanne halaye daga wajen iyaye zai iya sa ya zama da sauƙi yara su kusace su?
12 Ka yi la’akari kuma da yadda wasu fasalolin mutumtakar Allah ya sa ya zama da sauƙi wa mutanensa su kusace shi a sake. Alal misali, Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya yi zunubi ƙwarai da yin zina da Bath-sheba. Saboda mutum ne ajizi, Dauda ya yi wasu zunubai masu tsanani a rayuwarsa. Duk da haka, bai ƙi ya kusaci Jehovah ba kuma ya nemi gafararsa da kuma gyara. Babu shakka, alherin Allah da jinƙai sun sa ya zama da sauƙi wa Dauda ya juya ga Jehovah. (Zabura 103:8) Ta wurin nuna irin halayen nan na juyayi da jinƙai, iyaye za su iya buɗe hanyar yin magana da yaransu ko idan sun yi laifi ma.—Zabura 103:13; Malachi 3:17.
Ka Kasance da Laushin Hali
13. Menene kasancewa da laushin hali ya ƙunsa?
13 Yayin da suke sauraron yaransu, dole ne iyaye su kasance da laushin hali da ke nuna “hikima mai-fitowa daga bisa.” (Yaƙub 3:17) Manzo Bulus ya rubuta, ‘bari laushin halinku ya sanu ga dukan mutane.’ (Filibbiyawa 4:5) Menene yake nufi a kasance da laushin hali? Ma’ana ɗaya da aka bayar na kalmar Helenancin nan da aka fassara ‘laushin hali’ ita ce “ban da nace wa rubutun doka.” Ko da suna riƙe mizanan ɗabi’a da ta ruhaniya, ta yaya iyaye za su kasance da laushin hali?
14. Yaya Jehovah ya nuna laushin hali a bi da Lot?
14 Jehovah ya ba da misali mafi kyau wajen kasancewa da laushin hali. (Zabura 10:17) Lokacin da ya aririci Lot da iyalinsa su bar birnin Sodom da ke fuskantar halaka, Lot ya “yi nauwa.” Daga baya, sa’ad da mala’ikan Jehovah ya gaya masa ya gudu zuwa kan duwatsu, Lot ya ce: “Ba ni da iko in tsira zuwa dutsen . . . Ga shi, wannan birni [Zoar] kusa ne, in gudu gareshi, ƙanƙane ne kuwa: Ai! ka bari in yi can in tsira, ba ƙanƙane ba ne?” Me Jehovah ya ce game da wannan? Ya ce: “Ga shi, na amsa maka a kan wannan abu kuma, ba ni kaɓantadda birni wanda ka ambata.” (Farawa 19:16-21, 30) Jehovah a shirye yake ya yarda da roƙon Lot. Hakika, iyaye suna bukatar su bi mizanan da Jehovah Allah ya kafa cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Duk da haka, zai yiwu a bi muradin yara idan bai taka wata ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ba.
15, 16. Wane darasi iyaye za su koya daga misalin da ke a Ishaya 28:24, 25?
15 Kasancewa da laushin hali ya ƙunshi shirya zuciyar yara don su kasance a shirye su karɓi horo. A hanya ta misali, Ishaya ya sake gwada Jehovah da manomi, ya ce: “Babu fasawa mai-kabtu ya kan yi kabtu domin shi yi shuka? kullum ne ya kan buɗe hoggan gonarsa yana farfashewa? Lokacinda ya rigaya ya barbaje fuskarta, ba ya kan yayyafa algaru ba, ya zuzzuba riɗi, ya shuka alkama a jere, sha’ir a wurin da aka sanya masa, da tamba kuma a gefen?”—Ishaya 28:24, 25.
16 Jehovah yana “kabtu domin shi yi shuka” kuma yana “buɗe hoggan gonarsa yana farfashewa.” Ta haka yana shirya zukatan mutanensa kafin ya yi musu horo. A gyaran yaransu, ta yaya iyaye za su ‘kabta’ zuciyar yaransu? Wani uba ya yi koyi da Jehovah sa’ad da yake gyara ɗansa ɗan shekara huɗu. Sa’ad da ɗansa ya bugi yaro maƙwabci, uban da farko ya saurari hujjar ɗansa a hankali. Sai kuma, kamar yana ‘kabta’ zuciyar ɗansa, uban ya ba shi labarin wani ɗan yaro da ya sha wahala a hannun wani azzalumi. Da ɗan ya saurari labarin, sai yaron ya ce dole a hora azzalumin. Irin ‘kabtun’ nan ya gyara zuciyar yaron kuma ya sa ya zama da sauƙi ya ga cewa bugun yaro maƙwabci da ya yi halin azzalumci ne kuma ba daidai ba ne.—2 Samu’ila 12:1-14.
17. Wane darasi game da gyara ta iyaye aka tanadar a Ishaya 28:26-29?
17 Ishaya ya ci gaba da gwada gyaran da Jehovah yake yi da wani sashen aikin noma—sussuka. Manomi yana amfani da kayan aikin sussuka dabam dabam daidai yadda ƙarfin ƙaiƙayin gero. Ana amfani da sanda a dūkan ƙananan ɗaɗɗoya, amma ana amfani da babban gungumi ko wanda ake ɗora wa dabba don murtsuke hatsi mai tauri. Amma, ba zai murtsuke hatsi mai tauri ainun ba. Haka ma, sa’ad da Jehovah yake son ya cire wani abu da ba shi da kyau daga cikin mutanensa, yana bi da su a hanyoyi dabam dabam daidai da bukata da kuma yanayin. Ba ya ba da horo iri ɗaya kawai, ba azzalumi ba ne. (Ishaya 28:26-29) Wasu yara kallo kawai da iyayen za su yi musu ya ishe su, kuma ba a bukatar wani abu. Wasu suna bukatar tunasarwa a kai a kai, yayin nan kuma wasu suna bukatar rinjaya mai kyau. Iyaye da suke da laushin hali za su yi amfani da gyara da ta yi daidai da bukatun yaro.
Ka Sa Tattaunawa Cikin Iyali ta Zama da Daɗi
18. Ta yaya iyaye za su nemi lokaci don nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali kullum?
18 Hanya mafi kyau cikin hanyoyin koyar da yaranka ita ce nazarin Littafi Mai Tsarki na iyali a kai a kai da kuma tattauna Nassi na kowacce rana. Nazari na iyali abu mafi kyau ne idan ana yinsa a kai a kai. Idan an bar shi wai sai an sami lokaci ko kuma yi shi farat kawai, da kyar ya kasance a lokaci da ya fi dacewa. Saboda haka, dole ne iyaye su ‘nemi lokaci’ don nazari. (Afisawa 5:15-17) Zaɓan ainihi lokaci da ya fi dacewa yakan yi wuya. Wani uba ya lura cewa yayin da yaran suke girma, tsarin ayyukansu da ya bambanta ya sa ya zama da wuya a sami dukan iyalin a gida. Amma, iyalin koyaushe suna tare a daren taron ikilisiya. Saboda haka, uban ya shirya a yi nazari na iyali a waɗannan ranakun. Wannan ya taimake su. Duka yara ukun yanzu bayin Jehovah ne da sun yi baftisma.
19. Ta yaya iyaye za su yi koyi da Jehovah sa’ad da suke tafiyar da nazari na iyali?
19 Amma, bai isa a nazarta wasu abubuwa na Nassi kawai ba a sa’an nazarin. Jehovah ya koya wa Isra’ilawa da aka maido ta wurin firistoci, waɗanda suka ‘bayyana kuma suka sa ma’ana cikin’ Dokar, suka furta ‘fahimin karatun.’ (Nehemiah 8:8) Wani uba da ya yi nasara a taimakon dukan yaransa bakwai su yi ƙaunar Jehovah yakan koma ɗakinsa kafin lokacin nazari na iyali don ya shirya abin da zai yi daidai da bukatar kowanne yaro. Ya sa yaransa su more nazarin. “Nazarin yana yin daɗi,” in ji wani ɗansa da ya yi girma. “Idan muna wasan ƙwallo, aka ƙira mu don nazari na iyali, nan da nan mukan bar ƙwallon, mu gudu zuwa yin nazarin. Ɗaya cikin lokatai mafi daɗi ne a maraicen.”
20. Wace matsala ce mai yiwuwa a renon yara har ila za a bincika?
20 Mai Zabura ya sanar: “Ga shi, ’ya’ya gādo ne daga wurin Ubangiji: ɗiyan cikin kuma ladansa ne.” (Zabura 127:3) Renon yaranmu yana cin lokaci da kuma ƙoƙari, amma yin haka yadda ya dace yana nufin rai na har abada ne ga yaranmu. Lalle wannan lada ce mai kyau! To, sai mu ƙosa a yin koyi da Jehovah yayin da muke renon yaranmu. Amma, ko an ba iyaye hakkin “goye [yara] cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa,” ba dole ba ne cewa za su yi nasara. (Afisawa 6:4) Duk da kula mafi kyau, yaro zai iya zama ɗan tawaye ya daina bauta wa Jehovah. Sai me? Wannan ne zai zama jigon talifi na gaba.
[Hasiya]
a Labarai da ke cikin wannan talifin da kuma na gaba zai iya bambanta daga naka al’adun. Ka yi ƙoƙari ka fahimci ƙa’idodin da ke ciki, kuma ka yi amfani da su a naka al’adun.
Menene Amsarka?
• Ta yaya iyaye za su yi koyi da ƙaunar Jehovah da aka kwatanta a Kubawar Shari’a 32:11, 12?
• Menene ka koya daga hanyar da Jehovah ya sada da Isra’ilawa?
• Yadda Jehovah ya saurari roƙon Lot ya koya mana menene?
• Wane darasi ne na gyara yara ka koya daga Ishaya 28:24-29?
[Hoto a shafi na 20]
Musa ya gwada yadda Jehovah yake koyar da mutanensa ga yadda gaggafa ke rufa cakinsa
[Hotuna a shafi na 21]
Ya kamata iyaye su rifta lokaci don yaransu
[Hoto a shafi na 23]
“Ɗaya cikin lokatai mafi daɗi ne a maraicen”