Sauƙi Daga Wahala—Hanya Mafi Kyau
“Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa.”—MATTA 11:28.
1, 2. (a) Menene Littafi Mai Tsarki yake ɗauke da shi da zai taimaka a sauƙaƙa bala’i mai yawa? (b) Me ya sa koyarwar Yesu take da amfani?
WATAƘILA za ka yarda cewa wahala da yawa na da lahani; tana kawo baƙin ciki. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa dukan halittun ’yan Adam sun nawaita da mutane da yawa suna alla-alla su samu sauƙi daga rayuwar bala’i ta yau. (Romawa 8:20-22) Amma Nassosi sun nuna yadda za mu iya samu ɗan sauƙi daga wahala a yanzu ma. Wannan zai samu ta bin shawara da misalin wani saurayi da ya rayu ƙarnuka 20 da suka shige. Masassaƙi ne, amma ya fi son mutane. Ya yi magana da ta taɓa zuciyar mutane, ya biya bukatunsu, ya taimaki raunanu, kuma ya yi ta’aziyya ga masu baƙin ciki. Ƙari ga haka, ya taimaki mutane da yawa su kai ga manyanta ta ruhaniya. Da haka sun samu sauƙi daga bala’i mai yawa, yadda za ka iya samu.—Luka 4:16-21; 19:47, 48; Yohanna 7:46.
2 Wannan mutumin, Yesu na Nazarat, ba ilimi na duniya da wasu suke nema a Roma ta dā, Atina, ko Iskandariya ne ya yi masa ja-gora ba. Duk da haka, an san da koyarwarsa. Tana da jigo: gwamnati da Allah zai yi amfani da ita ya yi sarauta da kyau bisa duniya. Yesu ya kuma bayyana ƙa’idodi na musamman don rayuwa—ƙa’idodi da suke da amfani da gaske a yau. Waɗanda suka koya kuma suka yi amfani da abin da Yesu ya koyar suna more fa’idodi na nan da nan, har da sauƙi daga bala’i mai yawa. Ba za ka more wannan ba?
3. Wace gayyata mai girma ce Yesu ya miƙa?
3 Ƙila za ka yi shakka. ‘Wanda ya rayu da daɗewa haka zai iya kasancewa da wani amfani a rayuwata yanzu?’ To, ka saurari kalmomin Yesu na gayyata: “Ku zo gareni, dukanku da ku ke wahala, masu-nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina; gama ni mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai-sauƙi ce, kayana kuma mara-nauyi.” (Matta 11:28-30) Menene yake nufi? Bari mu bincika waɗannan kalmomi dalla-dalla mu ga yadda za su taimake ka ka samu sauƙi daga bala’i mai zaluntawa.
4. Su wanene Yesu ya yi wa magana, kuma ƙila me ya sa masu sauraronsa suka iske shi da wuya su yi abin da aka gaya musu?
4 Yesu ya yi wa mutane da yawa da suke ƙoƙari sosai su yi abin da ke na doka amma waɗanda suke ‘fama da nauyin kaya’ domin shugabanan Yahudawa sun sa addini ya zama kaya mai nauyi. (Matta 23:4) Sun nace a kan dokoki marasa iyaka a kan kusan dukan fannonin rayuwa. Ba za ka iske shi da ban wahala ba idan ka ci gaba da jin “kada ka” yi wannan ko wancan? Akasin haka, gayyatar Yesu ta kai mutane zuwa gaskiya, zuwa adalci, zuwa rayuwa mafi kyau ta wurin sauraransa. Hakika, hanyar sanin Allah na gaskiya ta ƙunshi saurarar Yesu Kristi, domin a cikinsa mutane za su—kuma iya—ganin yadda Jehovah yake. Yesu ya ce: “Wanda ya gan ni ya ga Uban.”—Yohanna 14:9.
Rayuwarka Tana da Matsi Ainun?
5, 6. Yaya yanayin aiki da kuɗin aiki na zamanin Yesu suke idan an gwada da namu a yau?
5 Ƙila za ka so wannan batun domin aikinka ko yanayin iyalinka yana dankare ka sosai. Ko kuwa wasu hakki kamar sun sha kanka. Idan haka ne, kana kamar waɗanda suke son gaskiya da Yesu ya sadu da su kuma ya taimake su. Alal misali, ka yi la’akari da matsalar neman abinci. Mutane da yawa suna fama da wannan a yau, haka da yawa suka yi a lokacin Yesu.
6 A dā can, lebura yana aiki tuƙuru na awoyi 12 a rana, kwana 6 a mako, don sule ɗaya kawai a rana. (Matta 20:2-10) Yaya wannan yake idan an gwada da kuɗin aikinka ko na abokananka? Yana da wuya a gwada kuɗin aiki na dā da na zamanin nan. Hanya ɗaya da za a gwada ta ita ce ta yin la’akari da abin da kuɗi zai iya saya. Wani masani ya ce a zamanin Yesu kuɗin burodi da aka yi da garin alkama da ya kai lita guda kuɗin aiki na awa guda ne a rana. Wani masani kuma ya ce moɗa guda na ruwan anab mai kyau kuɗin aikin awa biyu ne. Za ka gani daga wannan bayani cewa mutane a lokacin can suna aiki sosai kuma mai wuya na dogon lokaci don su biya bukatun rayuwa. Suna bukatar sauƙi da hutawa, yadda muke bukata. Idan an ɗauke ka a aiki, za a matsa maka ka yi aiki tuƙuru. Sau da yawa ma ba ma samun lokaci mu tsai da shawara mai kyau. Za ka yarda cewa kana bukatar hutawa.
7. Yaya mutane suka amsa saƙon Yesu?
7 A bayyane, mutane da yawa masu sauraro can dā da suke ‘wahala, da fama da nauyin kaya’ za su so gayyatar Yesu. (Matta 4:25; Markus 3:7, 8) Ka tuna cewa Yesu ya daɗa alkawarin nan, “ni kuwa in ba ku hutawa.” Wannan alkawarin har ila na cika a yau. Zai cika a gare mu idan muna ‘wahala da fama da nauyin kaya.’ Zai iya cika ga waɗanda muke ƙauna, da yanayinsu ya yi kama da haka.
8. Ta yaya renon yara da tsufa ke daɗa matsa mana?
8 Akwai wasu abubuwa da suke nawaita mutane. Renon yara ƙalubale ne mai girma. Zama yaro ma zai iya kasancewa da ƙalubale. Mutane manya da yara da suke fuskantar matsaloli na azanci da lafiyar jiki adadinsu na ƙaruwa. Ko da yake mutane za su iya rayuwa da daɗewa, tsofaffi suna da matsala ta musamman da za su yi fama da ita, duk da hanyoyin magani.—Mai-Wa’azi 12:1.
Yin Aiki a Ƙarƙashin Karkiyar
9, 10. A lokatan dā, mecece karkiya take alamtawa, me ya sa Yesu ke gayyatar mutane su ɗauki karkiyarsa a kansu?
9 Ka lura cewa cikin kalmomi da aka ɗauko daga Matta 11:28, 29, Yesu ya ce: “Ku ɗauka ma kanku karkiyata, ku koya daga wurina.” Can dā, talaka zai ji kamar yana aiki a ƙarƙashin karkiya. A lokatan dā, karkiya alama ce ta bauta ko rashin ’yanci. (Farawa 27:40; Leviticus 26:13; Kubawar Shari’a 28:48) Leburori da yawa da Yesu ya sadu da su suna aiki da gaske da karkiya a kafaɗarsu, suna ɗaukan kaya mai nauyi. Karkiyar tana iya zama da sauƙi a kan kafaɗa ko kuma ta goge kafaɗar dangane da yadda aka yi ta. Da yake shi masassaƙi ne, ƙila Yesu ya yi karkiya, kuma ya san yadda zai yi wadda take da “sauƙi.” Wataƙila ya saka fata ko zani a gefen da ake ajiyewa a kafaɗa don ta zama da sauƙi.
10 Yayin da Yesu ya ce, “Ku ɗauka ma kanku karkiyata,” ƙila yana kamanta kansa da wanda yake yin karkiya mai kyau da za ta kasance da “sauƙi” ga wuya da kafaɗar ma’aikaci. Saboda haka, Yesu ya daɗa: “Kayana kuma mara-nauyi.” Wannan ya nuna cewa karkiyar na da kyau a yi amfani da ita, kuma aikin ba na bawa ba ne. Hakika, ta wajen gayyatar masu sauraronsa su ɗauka karkiyarsa, Yesu bai ba su sauƙi na nan da nan daga dukan yanayin zalunci na lokacin ba. Duk da haka, sabon ra’ayi da ya bayyana ya kawo ɗan hutawa. Gyarar da za su yi ga yanayin rayuwarsu da hanyar yin abubuwa zai sauƙaƙa musu kuma. Mafi muhimmanci, bayyananne da tabbacaccen bege zai taimaka musu su iske rayuwa da ɗan sauƙi.
Za Ka Iya Samun Hutawa
11. Me ya sa Yesu ba maganar sauya karkiya kawai yake yi ba?
11 Ka lura fa, Yesu ba cewa yake mutane za su sauya karkiya da juna ba. Roma har ila za ta mallaki ƙasar, yadda gwamnati ta yau take mallakar inda Kiristoci ke zama. Biyar harajin Roma na ƙarni na farko ta ci gaba. Matsalolin lafiyar jiki da tattalin arziki suna ci gaba. Ajizanci da zunubi suna ci gaba da shafan mutane. Duk da haka, za su samu hutawa ta wurin karɓan koyarwar Yesu, yadda za ta zama tamu a yau.
12, 13. Menene Yesu ya nuna zai kawo hutawa, yaya wasu suka yi?
12 Muhimmin bayani na kwatanci na karkiyar Yesu ya zama a bayyane game da aikin almajirantarwa. Babu shakka cewa aikin Yesu na musamman koyar da wasu ne, yana nanata Mulkin Allah. (Matta 4:23) Saboda haka, yayin da ya ce, “Ku ɗauka ma kanku karkiyata,” babu shakka wannan ya ƙunshi bin sa a wannan aikin. Labarin Lingila ya nuna cewa Yesu ya motsa mutane masu zukatan kirki su canza sana’arsu, damuwa ta musamman a rayuwar mutane da yawa. Ka tuna yadda ya kira Bitrus, Andarawus, Yaƙub, da Yohanna: “Ku biyo ni, ni kuwa in sanya ku ku zama masūnan mutane.” (Markus 1:16-20) Ya nuna wa waɗannan masūnta yadda za su samu gamsuwa idan sun yi aiki da ya saka farko a rayuwarsa, su yi haka a ƙarƙashin ja-gorarsa da taimakonsa.
13 Wasu Yahudawa masu sauraransa sun fahimci koyarwarsa kuma sun yi amfani da ita. Ka yi tunani yadda bakin tekun da muka karanta game da shi a Luka 5:1-11 yake. Masūnta huɗu sun yi aiki duka dare ba su kama kome ba. Farat ɗaya, tarunsu ya cika! Wannan bai faru haka kawai ba; Yesu ya sa hannu. Yayin da suka duba bakin kogi, suka ga babban garken mutane suna son su saurari koyarwar Yesu. Wannan ya bayyana abin da Yesu ya gaya wa mutane huɗun: ‘Daga nan gaba za ku kama mutane.’ Menene suka amsa? “Suka zo da jiragensu a wajen gāɓa, suka rabu da abu duka, suka bi shi.”
14. (a) Ta yaya za mu samu wartsakewa a yau? (b) Wace bishara mai wartsakewa ce Yesu ya sanar?
14 Za ka iya amsa hakanan. Har ila ana aikin koyar da mutane gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Kusan miliyan shida na Shaidun Jehovah a dukan duniya sun amsa gayyatar Yesu su ‘ɗauka wa kansu karkiyarsa’; sun zama “masūnan mutane.” (Matta 4:19) Wasu sun mai da shi aikinsu na dukan lokaci; wasu suna iyakacin ƙoƙarinsu na ɗan lokaci. Duka suna iske shi da wartsakewa, saboda haka rayuwarsu ba ta da yawan bala’i. Ya ƙunshi yin abin da suke jin daɗinsa, gaya wa wasu bishara—“bishara ta mulkin.” (Matta 4:23) Abu mai daɗi ne koyaushe a yi magana game da labari mai daɗi amma musamman wannan bisharar. Littafi Mai Tsarki na ɗauke da abubuwa na musamman da muke bukata don mu huɗubantar da mutane da yawa cewa za su iya rayuwa da ba ta da yawan bala’i.—2 Timothawus 3:16, 17.
15. Ta yaya za ka amfana daga koyarwar Yesu game da rayuwa?
15 Har ila, har ma mutane da ba da daɗewa ba suka soma koya game da Mulkin Allah sun amfana daga koyarwar Yesu game da yadda za su yi rayuwa. Mutane da yawa za su iya faɗa da gaske cewa koyarwar Yesu ta wartsake su kuma taimake su canza rayuwarsu gabaki ɗaya. Za ka tabbata wannan ta fito da wasu cikin ƙa’idodi na rayuwa da ke cikin labarin rayuwar Yesu da hidimarsa, musamman Lingila da Matta, Markus, da Luka suka rubuta.
Hanyar Samun Hutawa
16, 17. (a) A ina za ka samu wasu muhimman koyarwa na Yesu? (b) Menene ake bukata don a samu hutawa ta wurin amfani da koyarwar Yesu?
16 A rani na shekara ta 31 A.Z., Yesu ya ba da lacca sananne a duniya har zuwa yau. Ana kiransa Huɗuba Bisa Dutse. An rubuta shi cikin Matta surori 5 zuwa 7 da Luka sura 6, kuma sun taƙaita koyarwarsa da yawa. Za ka samu wasu koyarwar Yesu a wani waje cikin Lingila. Abubuwa da yawa da ya faɗa sun bayyana kansu, ko da yin amfani da su zai kasance da kalubale. Me ya sa ba za ka karanta waɗannan surori a hankali, kuma ka yi tunani a kansu ba? Bari ikon ra’ayoyinsa ya shafi tunaninka da halinka.
17 Hakika, za a iya tsara koyarwar Yesu a hanyoyi dabam dabam. Bari mu tsara muhimman koyarwa don mu sa ɗaya kowacce rana a wata, da makasudin yin amfani da su a rayuwarka. Ta yaya? To, kada ka wuce darussan da sauri sauri. Ka tuna da masarauci mai arziki wanda ya tambaye Yesu Kristi: “Me zan yi domin in gaji rai na har abada?” Lokacin da Yesu ya maimaita farillai masu muhimmanci na Dokar Allah, mutumin ya ce yana yin waɗannan abubuwa. Duk da haka, ya fahimci cewa yana bukatar ya yi gyara. Yesu ya gaya masa ya ƙara sa ƙoƙari ya yi amfani da ƙa’idodin Allah a hanyoyi masu kyau, ya zama almajiri mai ƙwazo. A bayyane, mutumin ba ya son ya yi hakan. (Luka 18:18-23) Saboda haka, wanda yake son ya koyi koyarwar Yesu a yau na bukatar ya tuna cewa da bambanci tsakanin yarda da su da kuma bin su da gaske, da haka tana sauƙaƙa bala’i.
18. Ka kwatanta yadda za ka yi amfani mai kyau da akwati da ke cikin nan.
18 Don a soma bincike kuma a yi amfani da koyarwar Yesu, ka duba darasi na 1 da ke cikin akwati. Yana maganar Matta 5:3-9. Hakika, kowanne cikinmu za mu iya ba da lokaci sosai a yin bimbini a kan gargaɗi na ban al’ajabi da ke cikin waɗannan ayoyi. Amma, a duba dukansu, menene ka kammala game da hali? Idan da gaske kana son ka magance sakamakon matsi ainu a rayuwarka, menene zai taimake ka? Ta yaya za ka gyara yanayinka idan ka mai da hankali sosai ga al’amura na ruhaniya, kana tunanin wannan? Akwai wasu damuwa a rayuwarka da ka ke bukatar ka daina ɗaukansu da muhimmanci, don ka mai da hankali sosai ga batu na ruhaniya? Idan ka yi haka, zai daɗa ga farin cikinka yanzu.
19. Menene za ka yi ka samu ƙarin basira da fahimi?
19 Yanzu akwai wani abu da za ka yi. Me ya sa ba za ka tattauna waɗannan ayoyi da wani bawan Allah ba, wataƙila abokiyar aurenka, dangi na kusa, ko wani aboki? (Misalai 18:24; 20:5) Ka tuna cewa wannan basarauce mai arziki ya tambayi wani—Yesu—game da batu na musamman. Da amsa mai kyau zai ƙara zatonsa na farin ciki da rayuwa ta har abada. Ɗan’uwa mai bi da ka tattauna waɗannan ayoyi da shi ba zai yi daidai da Yesu ba; duk da haka, taɗi game da koyarwar Yesu zai amfane ku duka. Ka yi ƙoƙari ka yi hakan babu ɓata lokaci.
20, 21. Wane tsari za ka bi don ka koya game da koyarwar Yesu, kuma yaya za ka kimanta ci gabanka?
20 Ka sake duba akwati da ke cikin nan, “Koyarwa da Za ta Taimake Ka.” An tsara wannan koyarwa don ka bincika aƙalla koyarwa ɗaya kowacce rana. Da farko za ka iya karanta abin da Yesu ya faɗa cikin ayoyi da aka nuna. Sai ka yi tunani game da maganarsa. Ka yi tunanin yadda za ka yi amfani da ita a rayuwarka. Idan kana jin kana yin haka, ka yi bimbini ka ga abin da za ka ƙara yi don ka rayu bisa wannan koyarwa ta Allah. Ka yi amfani da shi a ranar. Idan ka iske shi da wuya ka fahimta ko ba ka san yadda za ka yi amfani da ita ba, ka yi ta wata rana. Amma ka tuna cewa, ba sai ka san shi sosai ba kafin ka ci gaba. Washegari za ka iya bincika wata koyarwa. A ƙarshen mako, za ka iya bincika yadda ka yi nasara a yin amfani da koyarwar Yesu guda huɗu ko biyar. Ka daɗa a mako na biyun, kowacce rana. Idan ka kasa a yin amfani da wasu koyarwar, kada ka fid da rai. Kowanne Kirista zai fuskanci wannan. (2 Labarbaru 6:36; Zabura 130:3; Mai-Wa’azi 7:20; Yaƙub 3:8) Ka ci gaba zuwa mako na uku da na huɗun.
21 Bayan wata ɗaya ko fiye da haka, ƙila ka bincika duka darussa 31. Hakika, yaya za ka ji game da haka? Ba za ka fi farin ciki ba, wataƙila ka ƙara wartsakewa? Ko idan gyara kaɗan kaɗai ka yi, mai yiwuwa bala’in zai ɗan sauƙaƙa, ko aƙalla za ka iya bi da matsi da kyau, kuma za ka samu hanyar ci gaba. Kada ka manta cewa akwai wasu darussa masu kyau na koyarwar Yesu da ba a lissafa su ba. Me ya sa ba za ka nemi wasu ba kuma ka yi ƙoƙarin yin amfani da su?—Filibbiyawa 3:16.
22. Menene zai faru in mun bi koyarwar Yesu, wane ƙarin abu ya kamata mu bincika?
22 Za ka gani cewa karkiyar Yesu, ko da ba ta da nauyi, da gaske tana da kyau. Kayan koyarwarsa da na almajiranci ba su da nauyi. Bayan fiye da shekara 60 na abin da ya gani, manzo Yohanna, abokin Yesu da yake ƙauna, ya ce: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” (1 Yohanna 5:3) Za ka iya kasancewa da irin wannan tabbaci kai ma. In ka ci gaba da yin amfani da koyarwar Yesu, za ka ƙara iske cewa abin da ke sa rayuwa ta kasance da matsi ga mutane da yawa a yau ba zai na sa ka wahala ba. Za ka gani cewa ka ɗan sauƙaƙa. (Zabura 34:8) Amma, akwai wani fanni na karkiyar Yesu mai sauƙi da kake bukatar ka bincika. Yesu ya kuma ambata cewa shi “mai-tawali’u ne, mai-ƙasƙantar zuciya.” Ta yaya wannan ya daidaita cikin koyo da muke yi daga Yesu da kuma yin koyi da shi? A talifi na gaba, za mu bincika wannan.—Matta 11:29.
Menene Amsarka?
• Me ya sa za mu dogara da Yesu sa’ad da muke neman sauƙi daga bala’i mai yawa?
• Mecece karkiya ta ke alamta, kuma me ya sa?
• Me ya sa Yesu ya gayyaci mutane su ɗauki karkiyarsa?
• Ta yaya hutawa ta ruhaniya za ta zama taka?
[Bayanin da ke shafi na 8]
A shekara ta 2002, jigon shekara na Shaidun Jehovah zai zama: “Ku zo gareni . . . ni kuwa in ba ku hutawa.”—Matta 11:28.
[Box/Hoto a shafi nas 6, 7]
Koyarwa da Za ta Taimake Ka
Waɗanne abubuwa masu kyau za ka samu a Matta surori 5 zuwa 7? Waɗannan surori ke ɗauke da koyarwa da Ƙwararren Malami, Yesu, ya gabatar a dutsen Galili. Don Allah ka karanta ayoyi da ke gaba, ka yi amfani da naka Littafi Mai Tsarki, kuma ka yi wa kanka tambayoyin da suka danganci waɗannan.
1. 5:3-9 Menene wannan yake gaya mini game da halina? Yaya zan yi ƙoƙarin samun farin ciki mai yawa? Ta yaya zan fi mai da hankali ga bukatuna na ruhaniya?
2. 5:25, 26 Me ya fi koyi da halin ƙyashi da mutane da yawa suke da shi kyau?—Luka 12:58, 59.
3. 5:27-30 Menene kalmomin Yesu suka nanata game da sha’awar jima’i? Ta yaya guje irin wannan zai daɗa ga farin cikina da kwanciyar rai?
4. 5:38-42 Me ya sa zan yi ƙoƙari na guje zafin hali na mutanen zamani?
5. 5:43-48 Yaya zan amfana daga sarƙuwa da abokan tarayya da kyau waɗanda ƙila ina ɗaukansu abokan gaba? Menene wataƙila wannan zai yi ya rage ko kawar da jayayya?
6. 6:14, 15 Idan wani lokaci ba na son na gafarta, kishi ko fushi ne ainihin dalilin? Yaya zan canza wannan?
7. 6:16-18 Na fi damuwa da yadda nake a waje fiye da yadda nake a ciki? Menene ya kamata na ƙara sani?
8. 6:19-32 Menene zai zama sakamakon idan na damu ainun da kuɗi da dukiya? Tunani game da menene zai taimake ni in daidaita game da wannan?
9. 7:1-5 Yaya nake ji yayin da nake tare da mutane da suke kushe wasu kuma suke zarginsu, koyaushe suna neman laifi? Me ya sa yake da muhimmanci na guje zama haka?
10. 7:7-11 Idan naciya yana da kyau yayin da na ke roƙon Allah abu, game da wasu fannonin rayuwa fa?—Luka 11:5-13.
11. 7:12 Ko da na san Ƙa’idar Ja-gora, sau nawa ne nake amfani da wannan gargaɗi a yadda nake bi da wasu?
12. 7:24-27 Tun da yake ni nake da hakkin ja-gorar rayuwa ta, yaya zan kasance a shirye in bi da matsaloli da damuwa da za su sha mini kai? Me ya sa ya kamata na yi tunani game da wannan yanzu?—Luka 6:46-49.
Ƙarin koyarwa da zan bincika:
13. 8:2, 3 Yaya zan yi wa tsiyayyu juyayi, yadda Yesu ya yi sau da yawa?
14. 9:9-38 Wane waje ne nuna jinƙai yake da shi a rayuwata, yaya zan ƙara nuna shi?
15. 12:19 A koyo daga annabci game da Yesu, ina ƙoƙari na guje yin musun jayayya?
16. 12:20, 21 Wane abu mai kyau zan yi kada na nawaita wasu ta maganganu ko ayyukata?
17. 12:34-37 Menene nake maganarsa yawancin lokacin? Na san cewa yayin da na matsa lemo, ruwan lemo zai fito, to me ya sa ya kamata na yi tunanin abin da nake a ciki, cikin zuciya ta?—Markus 7:20-23.
18. 15:4-6 Daga kalami da Yesu ya yi, menene na koya game da kula da tsofaffi?
19. 19:13-15 Menene nake bukatar na ɗauka lokaci na yi?
20. 20:25-28 Me ya sa ba shi da kyau a yi iko don kawai ana da ikon? Ta yaya zan yi koyi da Yesu a wannan?
Ƙarin abin tunani da Markus ya rubuta:
21. 4:24, 25 Me ya sa yadda nake bi da wasu yake da muhimmanci?
22. 9:50 Idan abubuwa da nake faɗa kuma nake yi suna da kyau, wane amfani mai kyau ƙila zai kawo?
A ƙarshe, ka yi la’akari da koyarwa kalilan da Luka ya rubuta:
23. 8:11, 14 Idan na bar damuwa, arziki, da jin daɗi suka mallaki rayuwata, menene zai iya zama sakamakon?
24. 9:1-6 Ko da Yesu yana da ikon warkar da masu ciwo, menene ya saka gaba da wannan?
25. 9:52-56 Ina saurin yin fushi? Ina guje wa halin ramako?
26. 9:62 Ta yaya ya kamata na ɗauka hakkin yin magana game da Mulkin Allah?
27. 10:29-37 Yaya zan nuna cewa ni maƙwabci ne, ba marar damuwa da wasu ba?
28. 11:33-36 Waɗanne canje-canje zan yi don rayuwata ta fi zama da sauƙi?
29. 12:15 Wace dangantaka take tsakanin rayuwa da dukiya?
30. 14:28-30 Idan na ɗauki lokaci na auna shawarwari da hankali, me zan guje wa, kuma da wane amfani?
31. 16:10-12 Waɗanne fa’idodi zan samu daga rayuwa ta riƙe aminci?
[Hotuna a shafi na 4]
Aikin ceton rai a ƙarƙashin karkiyar Yesu na wartsakewa