Ka Yi Tsayayya Da Ruhun Duniya Da Ke Canjawa
“Mu, ba ruhun duniya muka karɓa ba, amma ruhu da ke daga wurin Allah.”—1 Korinthiyawa 2:12.
1. A waɗanne hanyoyi ne aka ruɗe Hauwa’u?
“MACIJIN ya ruɗe ni.” (Farawa 3:13) Da waɗannan ’yan kalmomi, mace na farko, Hauwa’u, ta nemi ta bayyana dalilin tafarkin tawayenta ga Jehovah Allah. Abin da ta faɗa gaskiya ne, ko da yake ba ta da hujjar laifin da ta yi. Bayan haka, an hure manzo Bulus ya rubuta: “[Hauwa’u] aka ruɗe.” (1 Timothawus 2:14) An ruɗe ta ta yarda cewa rashin biyayya—cin haramtaccen ’ya’ya itacen—zai amfane ta, ya sa ta zama kamar Allah. Ba ta san wanda ya ruɗe ta ba. Ba ta sani ba cewa Shaiɗan Iblis ne yake magana ta wurin macijin.—Farawa 3:1-6.
2. (a) Ta yaya ne Shaiɗan ke ruɗin mutane a yau? (b) Menene “ruhun duniya,” kuma waɗanne tambayoyi ne za mu yi la’akari da su yanzu?
2 Tun daga lokacin Adamu da Hauwa’u, Shaiɗan ya ci gaba da ruɗin mutane. Hakika, yana “ruɗin dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Dabarunsa ba su canja ba. Ko da yake ba ya amfani da maciji na zahiri kuma ba, ya ci gaba da ɓoye kamaninsa. Ta wurin irin wasu liyafa, watsa labarai, da wasu hanyoyi, Shaiɗan ya ruɗe mutane su yarda cewa ba sa bukatar ko amfana daga ja-goranci mai kyau na Allah. Ƙoƙarin Iblis ya ruɗi mutane ya kawo ruhun tawaye da dokoki da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a ko’ina. Littafi Mai Tsarki ya kira wannan, “ruhun duniya.” (1 Korinthiyawa 2:12) Wannan ruhun ya rinjayi imani, ra’ayi da kuma halin waɗanda ba su san Allah ba. Yaya ake nuna ruhun nan, kuma ta yaya za mu iya ƙin tasirinta mai ɓatanci? Bari mu gani.
Ƙa’idodin Ɗabi’a Suna Suƙuƙucewa
3. Me ya sa “ruhun duniya” ya ci gaba da bayyana a zamaninmu?
3 A zamaninmu, “ruhun duniya” ya ci gaba da bayyana sosai. (2 Timothawus 3:1-5) Wataƙila ka lura da daɗa munin rashin ɗabi’a. Nassosi sun bayyana dalili da ya sa haka. Bayan an kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914, aka yi yaƙi a sama. An ci nasarar Shaiɗan da mala’ikunsa kuma aka jefar da su zuwa duniya. Shaiɗan ya ƙarfafa ƙoƙarinsa na ruɗin dukan duniya domin yana cike da fushi. (Ru’ya ta Yohanna 12:1-9, 12, 17) A kowacce hanya da zai iya, yana ƙoƙarin ya “ɓadda ko zaɓaɓu da kansu, da ya yiwu.” (Matta 24:24) Gurinsa shi ne, mutanen Allah. Yana ƙoƙarin ya lalace ruhaniyarmu domin mu rasa tagomashin Jehovah da kuma begen rai na har abada.
4. Yaya bayin Jehovah ke ɗaukan Littafi Mai Tsarki, kuma yaya duniya ke ɗaukansa?
4 Shaiɗan yana ƙoƙarin ɓata darajar Littafi Mai Tsarki, littafi mai tamani da ke koya mana game da Mahaliccinmu mai ƙauna. Bayin Jehovah suna ƙauna kuma suna daraja Littafi Mai Tsarki. Mun sani cewa shi ne hurarren Kalmar Allah, ba kalmar mutane ba. (1 Tassalunikawa 2:13; 2 Timothawus 3:16) Amma duniyar Shaiɗan na son mu yi tunani dabam. Alal misali, gabatarwan wani littafi da ke yi wa Littafi Mai Tsarki farmaki, ya ce: “Babu wani abu ‘mai-tsarki’ game da Littafi Mai Tsarki, ba kuwa ‘kalmar Allah’ ba ce. Ba mutane da Allah ya hure su ba ne suka rubuta shi, amma firistoci ne masu neman iko.” Waɗanda suka gaskata da irin da’awar nan sun faɗa cikin tunanin ƙarya cewa suna da ’yancin bauta ma Allah a hanya da sun ga dama—ko kuma su ƙi bauta masa gabaki ɗaya.—Misalai 14:12.
5. (a) Menene wani mawallafi ke da’awa game da addinai masu amfani da Littafi Mai Tsarki? (b) Yaya za a gwada wasu sanannen ra’ayin duniya da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa? (Haɗa da akwati a shafi na gaba.)
5 Farmaki na kai tsaye da na ɓoye a kan Littafi Mai Tsarki, tare da riya na addini ta waɗanda suke da’awar goyon bayanta, ya kai ga yawan ƙin addini, duk da addini da ke amfani da Littafi Mai Tsarki. A tsakanin masu watsa labarai da masana ma, an yi wa addini farmaki. Wani mawallafi ya lura: “Ra’ayin Yahudanci da Kiristanci da ta cika sanannun al’adun gargajiya ma ba ta dace ba. Duk kyaunsu, ana ganinsu kamar wani tsohon yayi mai kyau; duk rashin dacewarsu, ana musu ganin yayin dā, da yake suna hana ƙara ilimi, da kuma cin gaban kimiyya. A shekarun baya bayan nan ƙyamar ta kai ga ba’a da kuma ƙiyayya ta kai tsaye.” Wannan ƙiyayya ta asali daga waɗanda sun musunci bayyanuwar Allah ne da kuma waɗanda “suka zama wawaye.”—Romawa 1:20-22.
6. Wane ra’ayi ne duniya take da shi game da sha’anin jima’i da Allah ya haramta?
6 Don haka, ba abin mamaki ba ne cewa mutane suna bijirewa daga mizanan ɗabi’a na Allah. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta luwaɗi da “abin da ba ya kamata ba.” (Romawa 1:26, 27) Ya kuma furta cewa duk masu fasikanci da zina ba za su gaji mulkin Allah ba. (1 Korinthiyawa 6:9) Duk da haka, a ƙasashe da yawa, ba kawai an yarda da waɗannan sha’anin jima’i ba, amma ana ɗaukaka su a littattafai, jaridu, waƙoƙi, silima, da tsarin telibijin. Waɗanda suna furta rashin yardansu ga irin ayyukan nan ana musu ganin marasa azanci, masu sūka, kuma marasa wayewar kai. Maimakon ɗaukan mizanan Allah cewa ƙauna ce, duniya tana ɗaukansu cikas ne ga ’yancin kai da gamsarwa.—Misalai 17:15; Yahuda 4.
7. Waɗanne tambayoyi ya kamata mu yi wa kanmu?
7 A duniya da ke ƙara yin hamayya da Allah, yana da kyau mu lura da halayenmu da ƙa’idodinmu. Wasu lokatai ya kamata mu yi addu’a kuma mu bincika kanmu sosai don mu tabbatar cewa ba ma janyewa a hankali daga tunani da kuma mizanan Jehovah. Alal misali, za mu iya tambayar kanmu: ‘Ina jin daɗin wata hira da ya kamata na ƙi tun shekarun baya? Na soma yarda da ayyuka da Allah ya haramta ne? Ina ji kamar ina ɗaukan batutuwa ta ruhaniya da rashin muhimmanci fiye da yadda nake yi a dā ne? Yadda nake rayuwata ta nuna ina biɗan Mulkin da farko kuwa?’ (Matta 6:33) Irin tunanin nan zai taimake mu mu ƙi ruhun duniya.
“Kada Mu Zakuɗa”
8. Yaya mutum zai iya zakuɗa daga Jehovah?
8 Manzo Bulus ya rubuta wa ’yan’uwa Kiristoci haka: “Domin wannan fa ya kamata mu daɗa maida hankali musamman ga abin da aka ji, domin kada mu zakuɗa.” (Ibraniyawa 2:1) Jirgin ruwa da ya zakuɗa ba zai kai inda ya nufa ba. Idan matuƙin jirgin bai lura da iska da kuma rakuman ruwa ba, jirginsa zai bar hanya mai kyau kuma ya zakuɗa wurin haɗari kan duwatsu. Haka ne ma idan ba mu lura da gaskiya mai tamani na Kalmar Allah ba, za mu iya zakuɗa daga wurin Jehovah kuma mu lalace a ruhaniya. Ba ma bukatar mu ƙi gaskiyar sarai kafin mu sha irin wahalar nan ba. Hakika, ba mutane da yawa suka ƙi da Jehovah sarai da niyya ba. Sau da yawa, a hankali sukan shaƙu cikin wasu abubuwa da suke janye hankalinsu daga Kalmar Allah. Ba sa ma sanin haka, sai sun zakuɗa cikin zunubi. Irin mutanen nan ba sa farka daga barci har sai sun makara sarai kamar matuƙin jirgin ruwa da ke barci.
9. A waɗanne hanyoyi Jehovah ya albarkaci Sulemanu?
9 Ka yi la’akari da rayuwar Sulemanu. Jehovah ya ba shi ikon sarauta a kan Isra’ila. Allah ya yarda wa Sulemanu ya gina haikali kuma ya ja-gorance shi ya rubuta wasu littattafai na Littafi Mai Tsarki. Jehovah ya yi masa magana sau biyu kuma ya ba shi arziki, suna, da kuma sarauta ta salama. Mafi muhimmanci ma Jehovah ya albarkaci Sulemanu da hikima mai yawa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ya ba [Sulemanu] hikima da ganewa ƙwarai da gaske, da buɗaɗɗiyar zuciya, kamar yashin da ke a bakin teku. Hikimar [Sulemanu] fa ta fi hikimar dukan mutanen gabas, da dukan hikimar Masar.” (1 Sarakuna 4:21, 29, 30; 11:9) Babu shakka, za ka iya tunanin cewa, idan za a sami wani aminin Allah, lallai Sulemanu ne. Amma, Sulemanu ya zakuɗa zuwa ridda. Yaya hakan ya faru?
10. Wace doka Sulemanu ya ƙi yin biyayya da ita, kuma menene sakamakon?
10 Sulemanu ya sani ya kuma fahimci Dokar Allah sosai. Lallai zai lura da umurnin da ke game da waɗanda za su zama sarakuna a Isra’ila. A cikin umurnin, akwai wanda ya ce: “[Sarkin] ba kuwa za ya tara ma kansa mata ba, domin kada zuciyatasa ta karkata.” (Kubawar Shari’a 17:14, 17) Duk da wannan doka da take a bayyane, Sulemanu ya samo wa kansa mata ɗari bakwai, da ƙwaraƙwarai ɗari uku. Yawancin waɗannan mata suna bauta wa allolin arna. Ba mu san dalilin da ya sa Sulemanu ya kwashe mata da yawa haka ba, kuma ba mu san hujjar da ya ba da ba game da haka. Abin da muka sani shi ne bai yi biyayya da dokar Allah da take a bayyane ba. Sakamakonsa daidai da abin da Jehovah ya faɗi ne. Mu karanta: “Matan [Sulemanu] suka juyadda zuciyatasa zuwa bin waɗansu alloli.” (1 Sarakuna 11:3, 4) A hankali—sarai kuwa—hikimarsa ta ibada ta shuɗe. Ya zakuɗa. A kwana a tashi, burin Sulemanu ya faranta wa matansa arna rai sai ya sauya burinsa na yin biyayya ga Allah kuma faranta masa rai. Abin baƙin ciki ne, domin Sulemanu ne a farko ya rubuta kalmomin nan: “Ɗana, ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya zarge ni.”—Misalai 27:11.
Ruhun Duniya Yana da Iko Ƙwarai
11. Ta yaya abin da muke ciyar wa azancinmu ke shafan tunaninmu?
11 Misalin Sulemanu ya koya mana cewa yana da haɗari mu yi tunanin cewa domin mun san gaskiya, tasirin duniya ba zai shafe mu ba. Kamar yadda abinci ke aiki cikin jikinmu, haka ma abin da muke ci a azanci ke shafanmu. Abin da muke ciyar da azancinmu yana shafan tunaninmu da kuma halinmu. Da sanin wannan gaskiyar, ƙungiyoyi suna ɓatar da biliyoyin dala kowacce shekara su yi tallar kayayyakinsu. ’Yan talla suna amfani da abin armashi da hotuna masu kyau da na marmari domin su jawo masu ciniki. ’Yan talla sun sani cewa ganin talla sau ɗaya ko biyu kawai ba ya rinjayar mutane su yi hanzarin sayan kayayyakin nan ba. Amma, sau da sau da ’yan ciniki suke kallo, zai sa su so su bincika kayan. Talla tana nasara sosai—da ba haka ba, babu wanda zai zuba jarinta. Tana da tasiri ƙwarai a kan tunani da kuma halayen jama’a.
12. (a) Ta yaya Shaiɗan yake rinjayar tunanin mutane? (b) Menene ya nuna cewa za a iya rinjayar Kiristoci?
12 Kamar wanda yake talla, Shaiɗan yana gabatar da ra’ayinsa ta wurin yi musu ado, da sanin cewa a kwana a tashi zai iya jawo mutane zuwa hanyarsa. Ta wurin liyafa da kuma wasu hanyoyi, Shaiɗan yana ruɗin mutane su yarda da cewa nagarta mugunta ce mugunta kuma nagarta. (Ishaya 5:20) Kiristoci na farko ma sun fāɗa wa kamfen na Shaiɗan a yaɗa ƙarya. Littafi Mai Tsarki ya faɗakar: “Ruhu yana faɗi a sarari, cikin kwanaki na ƙarshe waɗansu za su ridda daga imani, suna maida hankali ga ruhohi na ruɗani da koyarwar aljanu, ta wurin riyar mutane masu-faɗin ƙarya, waɗanda an yi ma lamirinsu lalas sai ka ce da ƙarfe mai-wuta.”—1 Timothawus 4:1, 2; Irmiya 6:15.
13. Menene zama da miyagu, kuma ta yaya yin tarayya da su zai shafe mu?
13 Ba wani cikinmu da ruhun duniya ba zai iya shafa ba. Iska da kuma ikokin duniyar Shaiɗan suna da ƙarfi ƙwarai. Da hikima Littafi Mai Tsarki ya yi mana kashedi: “Kada ku yaudaru: zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” (1 Korinthiyawa 15:33) Zama da miyagu na iya nufin kome ko kuma kowa—da ke da ruhun duniya—har ma a cikin ikilisiya. Idan muna ganin cewa zama da miyagu ba zai ɓata mu ba, za mu kammala cewa zama da nagargaru ba zai taimake mu ba. Lallai hakan wauta ce ƙwarai! Littafi Mai Tsarki ya bayyana batun sarai haka: “Ka yi tafiya tare da masu-hikima, kai kuwa za ka yi hikima: Amma abokin tafiyar wawaye za ya ciwutu dominsa.”—Misalai 13:20.
14. A waɗanne hanyoyi za mu yi tsayayya da ruhun duniya?
14 Don a tsayayya wa ruhun duniya, dole ne mu yi tarayya da mutane masu hikima—waɗanda suke bauta wa Jehovah. Dole ne mu ciyar da azantanmu da abubuwan da za su gina bangaskiyarmu. Manzo Bulus ya rubuta: “ ’Yan’uwa, iyakar abin da ke mai-gaskiya, iyakar abin da ya isa bangirma, iyakar abin da ke mai-adalci, iyakar abin da ke mai-tsabta, iyakar abin da ke jawo ƙauna, iyakar abin da ke da kyakkyawan ambato; idan akwai kirki, idan akwai yabo, ku maida hankali ga waɗannan.” (Filibbiyawa 4:8) Mu mutanen da aka halitta da iya yin zaɓe, za mu iya zaɓan abubuwan da za mu so mu yi. Bari mu zaɓi mai da hankali ga abubuwan da za su jawo mu kurkusa da Jehovah.
Ruhun Allah Ya Fi Iko
15. Ta yaya Kiristoci a Koranti na dā suka bambanta da sauran mazauna birnin?
15 Ba kamar waɗanda ruhun duniya ya ruɗe su ba, ruhu mai tsarki na Allah ne ke ja-gorar Kiristoci na gaskiya. Ikilisiyar da ke a Koranti ne Bulus ya rubuta musu: “Mu, ba ruhun duniya muka karɓa ba, amma ruhun da ke daga wurin Allah; domin mu sansance da bayebayen da Allah ya ke ba mu a yalwace.” (1 Korinthiyawa 2:12) Birnin Koranti na dā, ruhun duniya ne ke rinjayarsa. Yawancin mazauna ciki malalata ne da aka sami furcin nan “zama ’yan Koranti” da yake nufin “a yi lalata.” Shaiɗan ya makantar da azantan mutanen. Ban da haka ma, ba su fahimci kome ba game da Allah na gaskiya. (2 Korinthiyawa 4:4) Duk da haka, ta wurin ruhunsa mai tsarki, Jehovah ya wayar da wasu ’yan Koranti, da ya sa suka iya samun sanin gaskiya. Ruhunsa ya motsa su su yi canje-canje a rayukansu domin su iya samun tagomashinsa da kuma albarka. (1 Korinthiyawa 6:9-11) Ko da yake ruhun duniya yana da ƙarfi, ruhun Jehovah ya fi ƙarfi.
16. Ta yaya za mu sami ruhun Allah mu kuma riƙe shi?
16 Haka ma yake a yau. Ruhun Jehovah ne ya fi iko a dukan sararin halitta, kuma yana ba da shi kyauta wa kowa da ya neme shi cikin bangaskiya. (Luka 11:13) Amma, ba tsayayya wa ruhun duniya kawai za mu yi ba don mu sami ruhun Allah. Dole ne mu yi nazarin Kalmar Allah a kai a kai mu kuma yi amfani da ita a rayuwarmu saboda ruhunmu—halinmu—ya yi daidai da tunaninsa. Idan mun yi haka, Jehovah zai ƙarfafa mu mu yi tsayayya wa kowanne dabaran da Shaiɗan zai yi amfani da shi ya halaka ruhaniyarmu.
17. A waɗanne hanyoyi ne abin da ya faru wa Lutu zai taimake mu?
17 Ko da yake Kiristoci ba na duniya ba ne, suna cikin duniya. (Yohanna 17:11, 16) Babu wani cikinmu da zai iya kauce wa ruhun duniya gabaki ɗaya, domin muna aiki ko kuma zama tare da waɗanda ba sa ƙaunar Allah ko hanyoyinsa. Yadda Lutu ya ji ne muke ji, wanda “ransa ya ɓaci ƙwarai” har ya sha azaba game da miyagun ayyuka da mutanen Saduma da yake zama cikinsu suke yi? (2 Bitrus 2:7, 8) Saboda haka, mu ƙarfafa. Jehovah ya kāre Lutu ya kuma ceci shi, kuma zai iya yi mana haka nan. Ubanmu mai ƙauna yana gani kuma ya san yanayinmu, kuma zai iya taimakonmu ya ba mu ƙarfin da muke bukata don mu riƙe ruhaniyarmu. (Zabura 33:18, 19) Idan muka dangana gare shi, dogara gare shi, kuma biɗe shi, zai taimake mu mu tsayayya wa ruhun duniya, ko yaya yanayinmu ke da wuya.—Ishaya 41:10.
18. Me ya sa za mu daraja dangantakarmu da Jehovah?
18 A duniya da take rabe daga Allah kuma Shaiɗan ya ruɗe ta, mu mutanen Jehovah mun sami albarkar sanin gaskiya. Saboda haka, muna samun farin ciki da salama da duniya ba ta da ita. (Ishaya 57:20, 21; Galatiyawa 5:22) Muna godiya ga wannan bege mai girma na rai na har abada a Aljanna, inda babu ruhun wannan duniya da ke shuɗewa. Saboda haka, bari mu daraja dangantakarmu da Allah kuma mu kasance a faɗake mu gyara wani nufi na zakuɗawa a ruhaniya. Bari mu matso kusa da Jehovah, zai taimake mu mu yi tsayayya wa ruhun duniya.—Yaƙub 4:7, 8.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• A waɗanne hanyoyi Shaiɗan ya ruɗi kuma yake yaudarar mutane?
• Ta yaya za mu kauce wa zakuɗa daga Jehovah?
• Menene ya nuna cewa ruhun duniya yana da iko ƙwarai?
• Ta yaya za mu sami kuma riƙe ruhun da ke daga wurin Allah?
[Akwati a shafi na 11]
HIKIMA TA DUNIYA DA HIKIMA TA IBADA
Babu cikakkiyar gaskiya—mutane “Maganar [Allah] ita ce gaskiya.”
suna da tasu gaskiya. —Yohanna 17:17.
Don a san nagarta daga “Zuciya ta fi kome rikici, cuta
mugunta, ka dogara ga gareta ƙwarai irin ta fidda
yadda kake ji. zuciya.”—Irmiya 17:9.
Ka yi abin da kake so. “Mutum kuwa ba shi da iko shi
shirya tafiyarsa.”—Irmiya 10:23.
Arziki ne mabuɗin farin ciki. “Son kuɗi asalin kowacce irin
mugunta ne.”—1 Timothawus 6:10.
[Hoto a shafi na 18]
Sulemanu ya zakuɗa daga bauta ta gaskiya kuma ya juya ga allolin ƙarya
[Hoto a shafi na 20]
Kamar mai talla, Shaiɗan yana gabatar da ruhun duniya. Kana tsayayya masa kuwa?