Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 3/15 pp. 8-12
  • Ka Karɓi Ruhun Allah Ba Na Duniya ba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Karɓi Ruhun Allah Ba Na Duniya ba
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Me Ya Sa Ruhun Duniya Yake Ko’ina?
  • Shin Ruhun Duniya Yana Rinjayarka Ne?
  • Ka Koya Daga Misalin Yesu
  • Za Mu Iya Yin Nasara da Duniya
  • Ka Ƙi “Ruhun Duniya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Me Ya Sa Ruhun Allah Zai Yi Mana Ja-gora?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Yi Tafiya Bisa Ga Ruhu Kuma Ka Yi Rayuwar Da Ta Jitu Da Keɓe Kanka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Wane Irin Hali Ne Kake Da Shi?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 3/15 pp. 8-12

Ka Karɓi Ruhun Allah Ba Na Duniya ba

“Ba ruhun duniya muka karɓa ba, amma ruhun da ke daga wurin Allah; domin mu sansance da bayebayen da Allah ya ke ba mu a yalwace.” —1 KOR. 2:12.

1, 2. (a) A wane azanci ne Kiristoci na gaskiya suke yaƙi? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika?

KIRISTOCI na gaskiya suna yaƙi! Abokin gābanmu yana da ƙarfi, makiri ne, kuma yana dagewa a yaƙi. Yana da makami mai ci sosai da ya sa ya mallaki yawancin ’yan Adam. Amma ba ma bukatar mu ji cewa ba mu da begen yin nasara. (Isha. 41:10) Muna da abin da za mu kāre kanmu da shi da zai iya jimre wa kowane farmaki da aka kai mana.

2 Yaƙinmu ba na zahiri ba ne amma na ruhaniya. Shaiɗan Iblis ne abokin gābanmu, kuma “ruhun duniya” ne ainihin makamin da yake amfani da shi. (1 Kor. 2:12) Ainihin abin da za mu kāre kanmu da shi ga farmakin Shaiɗan shi ne ruhun Allah. Don mu yi nasara a wannan yaƙin kuma mu kasance da dangantaka na kud da kud da Allah, muna bukatar mu roƙi Allah ya ba mu ruhunsa kuma mu nuna ɗiyar ruhunsa a rayuwarmu. (Gal. 5:22, 23) Amma, mene ne ruhun duniya, kuma yaya yake kasancewa da rinjaya sosai? Yaya za mu san cewa ko ruhun duniya yana rinjayarmu? Mene ne za mu iya koya daga wurin Yesu game da samun ruhun Allah da kuma yin tsayayya da ruhun duniya?

Me Ya Sa Ruhun Duniya Yake Ko’ina?

3. Mene ne ruhun duniya?

3 “Sarkin duniya” Shaiɗan, ne tushen ruhun wannan duniyar, kuma ruhun yana gāba da ruhu mai tsarki na Allah. (Yoh. 12:31; 14:30; 1 Yoh. 5:19) Hali ne na musamman na duniya, kuma wannan ruhun yana motsa al’ummar ’yan Adam yin saɓani da nufin Allah da kuma ƙudurinsa.

4, 5. Ta yaya ruhun da Shaiɗan yake ɗaukaka ya yaɗu a ko’ina?

4 Ta yaya ruhun da Shaiɗan yake ɗaukaka ya yaɗu a ko’ina? Da farko, Shaiɗan ya ruɗi Hauwa’u a lambun Adnin. Ya rinjaye ta cewa kasancewa a bare daga Allah zai kyautata rayuwarta. (Far. 3:13) Shi mugun maƙaryaci ne! (Yoh. 8:44) Sa’annan ta wurin matar, ya sa Adamu ya yi rashin aminci ga Jehobah. Domin zaɓin da Adamu ya yi, aka sayar da ’yan Adam ga zunubi, da hakan mutane suka gāji ruhun Shaiɗan na rashin biyayya.—Karanta Afisawa 2:1-3.

5 Shaiɗan ya kuma rinjayi mala’iku da yawa, waɗanda suka zama aljanu. (R. Yoh. 12:3, 4) Wannan cin amana da aka wa Allah ya faru kafin Rigyawa na zamanin Nuhu. Waɗannan mala’ikun sun gaskata cewa zai fi kyau su bar matsayinsu a sama kuma su bi sha’awoyinsu da bai dace ba a duniya. (Yahu. 6) Da taimakon waɗannan aljanun, da yanzu suka sake zama ruhu, Shaiɗan yana “ruɗin dukan duniya.” (R. Yoh. 12:9) Abin baƙin ciki, yawancin ’yan Adam ba su san cewa aljanu suna rinjayarsu ba.—2 Kor. 4:4.

Shin Ruhun Duniya Yana Rinjayarka Ne?

6. Ta yaya ruhun duniya zai iya shafanmu?

6 Mutane da yawa ba su san yadda Shaiɗan yake rinjayar mutane ba, amma an koya wa Kiristoci na gaskiya daga Littafi Mai Tsarki yadda yake yin hakan. (2 Kor. 2:11) Hakika, ruhun duniya ba zai rinjaye mu ba sai dai mun ƙyale shi ya yi hakan. Bari mu bincika tambayoyi huɗu da za su taimaka mana mu san ko ruhun Allah ne yake rinjayarmu ko kuma na duniya ne.

7. Wace hanya guda ce Shaiɗan yake ƙoƙari ya nisanta mu daga wurin Jehobah?

7 Mene ne nishaɗin da na zaɓa yake nunawa game da ni? (Karanta Yaƙub 3:14-18.) Shaiɗan yana ƙoƙari ya nisanta mu daga wurin Allah, ta wurin rinjayarmu mu so zalunci. Iblis ya san cewa Jehobah ya ƙi jinin wanda yake son zalunci. (Zab. 11:5) Saboda haka, Shaiɗan yana ƙoƙari ya yi amfani da littattafai, fina-finai, kaɗe-kaɗe, wasanni na na’ura, waɗanda wasu cikinsu suna zuga masu wasannin su yi mugun lalata da zalunci don su biya bukatar sha’awoyinsu na jiki. Shaiɗan yana farin ciki muddin wani sashe na zuciyarmu tana ƙaunar miyagun abubuwa, ko ma idan har ila muna ƙaunar abin da yake da kyau.—Zab. 97:10.

8, 9. Waɗanne tambayoyi game da nishaɗi ne ya kamata mu yi wa kanmu?

8 A wani ɓangare kuma, waɗanda suke da ruhun Allah suna motsawa su kasance da tsarki, lumana, da kuma cike da jin ƙai. Ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Shin nishaɗin da na zaɓa zai ƙarfafa ni na kasance da halaye masu kyau?’ Hikima daga bisa “marar-riya ce.” Waɗanda ruhun Allah yake musu ja-gora ba sa wa maƙwabtansu wa’azi cewa su kasance da tsarki da kuma salama amma kuma su riƙa jin daɗin kallon mugunta da lalata a ɓoye cikin gidajensu.

9 Jehobah yana bukatar mu bauta masa shi kaɗai. Shaiɗan zai iya so mu bauta masa ko sau ɗaya ne kawai, kamar yadda ya bukaci Yesu ya yi. (Luk 4:7, 8) Za mu iya tambayar kanmu: ‘Nishaɗin da na zaɓa yana ba ni zarafin bauta wa Allah shi kaɗai? Zaɓin da na yi yana sa ya kasance mini da wuya ko kuma da sauƙi na ƙi ruhun duniya? Zai dace na canja irin nishaɗin da na zaɓa a nan gaɓa?’

10, 11. (a) Wane hali ne ruhun duniya yake ƙarfafawa game da abubuwan mallaka? (b) Kalmar da ruhun Allah ya hure tana ƙarfafa wane irin hali?

10 Mene ne ra’ayi na game da abubuwan mallaka? (Karanta Luka 18:24-30.) Ruhun duniya yana ɗaukaka “sha’awar idanu” ta wurin ƙarfafa haɗama da son abin duniya. (1 Yoh. 2:16) Kuma yana sa wasu su ƙudurta zaman mawadata. (1 Tim. 6:9, 10) Wannan ruhun zai sa mu gaskata cewa tara abin duniya zai sa mu samu kāriya na dindindin. (Mis. 18:11) Amma dai, idan muka ƙyale yadda muke son kuɗi ya fi yadda muke ƙaunar Allah, Shaiɗan zai yi nasara. Ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Shin na mai da hankali ga neman abin duniya da kuma jin daɗin rayuwa?’

11 Akasin haka, Kalmar da ruhun Allah ya hure, ta ƙarfafa mu mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi kuma mu yi aiki sosai don tanadar da abin biyan bukata na kanmu da kuma na iyalinmu. (1 Tim. 5:8) Ruhun Allah yana taimakon waɗanda suka same shi su yi koyi da halin karimci na Jehobah. An san irin waɗannan mutanen da ba da kyauta ba masu karɓa kawai ba. Suna daraja mutane fiye da abubuwa kuma suna raba abin da suke da shi sa’ad da za su iya yin hakan. (Mis. 3:27, 28) Kuma ba sa ƙyale neman kuɗi ya fi bauta wa Allah muhimmanci.

12, 13. Akasin ruhun duniya, ta yaya ruhun Allah zai iya shafe mu a hanya mai kyau?

12 Wanne irin ruhu ne hali na yake nunawa? (Karanta Kolosiyawa 3:8-10, 13.) Ruhun duniya yana ƙarfafa ayyukan jiki. (Gal. 5:19-21) Ainihin gwaji ga irin ruhun da ke rinjayarmu yana zuwa ne sa’ad da abubuwa ba sa tafiya daidai, ba sa’ad da babu wata matsala ba, kamar sa’ad da wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta yi banza da mu, ta ɓata mana rai, ko kuma ta yi mana laifi. Ƙari ga haka, a asirce a gidajenmu, zai iya kasance a bayane irin ruhun da ke rinjayarmu. Zai dace mu bincika kanmu. Ka tambayi kanka, ‘Fiye da watanni shida da suka wuce, shin hali na ya daɗa zama kamar na Kristi ko kuwa na koma ga irin furci da ɗabi’a marar kyau?’

13 Ruhun Allah zai iya taimaka mana mu “tuɓe tsohon mutum tare da ayyukansa” kuma mu yafa “sabon mutum.” Hakan zai taimaka mana mu zama masu ƙauna da kuma kirki sosai. Za mu so mu gafarta wa juna, ko idan akwai ƙwaƙƙwarar dalilin yin ƙara. Ba za mu ƙara aikata ga abin da muke jin cewa rashin gaskiya ne da “ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage.” Maimakon haka, za mu yi ƙoƙari mu zama “masu-tabshin zuciya.”—Afis. 4:31, 32.

14. Yaya mutane da yawa a duniya suke ɗaukan Kalmar Allah?

14 Shin ina daraja da kuma ƙaunar mizanan ɗabi’a na Littafi Mai Tsarki? (Karanta Misalai 3:5, 6.) Ruhun duniya yana nuna halin tawaye da Kalmar Allah. Waɗanda wannan ruhun yake rinjayarsu ba sa amincewa da sashen Littafi Mai Tsarki da suke ganin yana da wuya, sun fi son al’adu da falsafa na ’yan Adam. (2 Tim. 4:3, 4) Wasu ba sa daraja Kalmar Allah gabaki ɗaya. Irin waɗannan mutane suna yin shakkar muhimmancin Littafi Mai Tsarki da kuma gaskiyarsa, sun kasance da hikima a idanunsu. Sun rage darajar mizanansa masu tsarki game da zina da luwaɗi da kuma kashe aure. Suna koyar cewa “mugunta nagarta; nagarta kuma mugunta” ne. (Isha. 5:20) Shin wannan ruhun ya shafe mu ne? Muna dogara ne ga hikimar ’yan Adam, har da ra’ayoyinmu, sa’ad da muke fuskantar matsaloli? Ko kuwa muna ƙoƙari mu bi shawarar Littafi Mai Tsarki?

15. Maimakon mu dogara ga hikimarmu, mene ne ya kamata mu yi?

15 Ruhun Allah yana sa mu daraja Littafi Mai Tsarki. Kamar wani marubucin zabura, muna ɗaukan kalmar Allah a matsayin fitila ga sawayenmu da kuma haske ga tafarkinmu. (Zab. 119:105) Maimakon mu dogara ga hikimarmu, muna dogara ga rubutacciyar Kalmar Allah don ta taimaka mana mu rarrabe nagarta daga mugunta. Muna koya ba kawai mu daraja Littafi Mai Tsarki ba amma kuma mu yi ƙaunar dokar Allah.—Zab. 119:97.

Ka Koya Daga Misalin Yesu

16. Mene ne kasancewa da “nufin Kristi” ya ƙunsa?

16 Don mu samu ruhun Allah, dole ne mu koya “nufin Kristi.” (1 Kor. 2:16) Kasancewa ‘da hankali ɗaya da junanmu bisa ga Kristi Yesu’ yana bukatar mu san yadda yake koyarwa da kuma aikatawa, sa’annan kuma mu yi koyi da shi. (Rom. 15:5; 1 Bit. 2:21) Ka yi la’akari da wasu hanyoyin da za mu iya yin hakan.

17, 18. (a) Mene ne muka koya daga wurin Yesu game da addu’a? (b) Me ya sa ya kamata mu “yi ta roƙo”?

17 Ka yi addu’a don ka samu ruhun Allah. Kafin ya fuskanci gwaji, Yesu ya yi addu’a don ruhun Allah ya taimaka masa. (Luk 22:40, 41) Mu ma muna bukatar mu roƙi Allah don ya ba mu ruhunsa mai tsarki. Jehobah yana ba da ruhunsa a sake ga dukan waɗanda suka roƙe shi cikin bangaskiya. (Luk 11:13) Yesu ya ce: “Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku. Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema na tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.”—Mat. 7:7, 8, Littafi Mai Tsarki.

18 Sa’ad da kake neman ruhun Jehobah da kuma taimakonsa, kada ka yi saurin daina roƙo. Muna iya bukatar mu yi addu’a a kai a kai kuma mu daɗe muna yin hakan. A wani lokaci, Jehobah yana ƙyale masu roƙonsa su nuna yawan yadda suke damuwa da kuma tabbatacciyar bangaskiyarsu kafin ya amsa addu’o’insu.a

19. Mene ne Yesu yake yi a ko da yaushe, kuma me ya sa za mu yi koyi da shi?

19 Ka yi biyayya ga Jehobah da dukan zuciyarka. A ko da yaushe Yesu yana yin abin da yake faranta wa Ubansa rai. Akwai lokacin da ra’ayin Yesu game da yadda za a bi da wani yanayi ya yi dabam da abin da Ubansa yake so. Duk da haka, da aminci ya gaya wa Ubansa: “Ba nawa nufi ba, naka za a yi.” (Luk 22:42) Ka tambayi kanka, ‘Ina yi wa Allah biyayya ko sa’ad da yin hakan ba shi da sauƙi?’ Yin biyayya ga Allah yana da muhimmanci don samun rai. Muna bukatar mu yi masa biyayya sarai domin shi ne ya halicce mu kuma shi ne Tushe da Wanda yake kiyaye ranmu. (Zab. 95:6, 7) Babu abin da ya fi yin biyayya. Ba za mu samu amincewar Allah idan ba mu yi masa biyayya ba.

20. Mene ne Yesu ya mai da hankali a kai a rayuwarsa, kuma yaya za mu iya yin koyi da shi?

20 Ka san Littafi Mai Tsarki sosai. Sa’ad da yake yin tsayayya da farmakin da Shaiɗan ya kai wa bangaskiyarsa kai tsaye, Yesu ya yi ƙaulin Nassosi. (Luk 4:1-13) Sa’ad da yake fuskantar ’yan addini masu yi masa hamayya, Yesu ya yi amfani da Kalmar Allah a matsayin ikonsa. (Mat. 15:3-6) Yesu ya mai da hankali ga sani da bin dokar Allah a dukan rayuwarsa. (Mat. 5:17) Ya kamata mu ma mu ci gaba da yin tunani game da Kalmar Allah da ke ƙarfafa bangaskiya. (Filib. 4:8, 9) Samun lokaci don nazari na kanmu da na iyali yana iya yi wa wasunmu wuya. Amma, maimakon mu nemi lokaci, muna iya keɓe lokaci.—Afis. 5:15-17.

21. Wane shiri ne za mu iya yin amfani da shi don ya taimaka mana mu san Kalmar Allah da kyau kuma mu bi ƙa’idodinsa?

21 “Bawan nan mai-aminci, mai-hikima” ya taimaka mana mu samu lokaci don nazari na kanmu da na iyali ta wurin shirya Bauta ta Iyali da yamma a kowane mako. (Mat. 24:45) Shin kana yin amfani da wannan shirin da kyau? Don ka san nufin Kristi, shin kana iya haɗa abin da Yesu ya koyar a kan batutuwa da ka zaɓa a sashe na nazarinka? Kana iya yin amfani da littafin nan Watch Tower Publications Index don ka samu bayani a kan batun da kake son ka bincika. Alal misali, daga shekara ta 2008 zuwa 2010, wannan mujalla ta wa’azi na ɗauke da tsarin talifofi 12 mai jigo “Abin da Muka Koya Daga Wurin Yesu.” Kana iya yin amfani da waɗannan talifofi sa’ad da kake nazari. Somawa daga shekara ta 2006, Awake! na ɗauke da talifin nan “How Would You Answer?” da yanzu ake kira “For Family Review” [Don Bita ta Iyali.] An shirya wannan tambayar don ta taimaka maka ka ƙara da kuma zurfafa iliminka na Kalmar Allah. Zai dace ka haɗa waɗannan talifofin a tsarin Bautarka ta Iyali a lokaci lokaci.

Za Mu Iya Yin Nasara da Duniya

22, 23. Mene ne ya wajaba mu yi don mu yi nasara da duniya?

22 Don ruhun Allah ya yi mana ja-gora, dole ne mu ƙi ruhun duniya. Yin hakan ba shi da sauƙi. Yaƙin zai iya zama mai wuya sosai. (Yahu. 3) Amma za mu iya yin nasara! Yesu ya gaya wa almajiransa: “A cikin duniya kuna da wahala; amma ku yi farin ciki, na yi nasara da duniya.”—Yoh. 16:33.

23 Mu ma za mu iya yin nasara da duniya idan mun ƙi ruhunta kuma muka yi iyakar ƙoƙarinmu don mu samu ruhun Allah. Hakika, ‘Idan Allah na wajenmu, wa ke gāba da mu?’ (Rom. 8:31) Ta wajen samun ruhun Allah da kuma bin ja-gorarsa yadda aka tsara cikin Littafi Mai Tsarki, za mu samu gamsuwa, salama, farin ciki, da tabbacin rai madawwami a sabuwar duniya da ta yi kusa.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani, ka duba shafuffuka na 170 zuwa 173 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?

Ka Tuna?

• Me ya sa ruhun duniya ya yaɗu sosai a ko’ina?

• Waɗanne tambayoyi huɗu ne ya kamata mu yi wa kanmu?

• Waɗanne abubuwa uku ne muka koya daga Yesu game da samun ruhun Allah?

[Hoton da ke shafi na 8]

Ta yaya waɗansu mala’iku suka zama aljanu?

[Hoton da ke shafi na 10]

Shaiɗan yana yin amfani da ruhun duniya don ya rinjayi mutane, amma za mu iya ’yantar da kanmu daga rinjayarsa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba