Ka Ƙi “Ruhun Duniya”
“Ba ruhun duniya muka karɓa ba, amma ruhun da ke daga wurin Allah” —1 KOR. 2:12.
1, 2. (a) Me ya sa a dā ake saka tsuntsayen kanari a mahaƙa a Britaniya? (b) Wane haɗari ne Kiristoci suke fuskanta?
ASHEKARA ta 1911, gwamnatin Britaniya ta kafa doka da aka shirya don a ceci ran mahaƙar kwal. Kowane mai haƙi yana bukatar ya ajiye tsuntsayen kanari biyu. Me ya sa? Idan wuta ta kama wajen haƙa kwal ɗin, masu aikin ceto za su ɗauki tsuntsayen kanari su shiga inda ake haƙa kwal. Tsuntsayen suna iya jin warin iska mai guba kamar iskar ƙuna. Idan iskar ta gurɓace, tsuntsayen za su nuna alama cewa da akwai matsala, har su faɗi daga inda suke. Wannan alamar tana da muhimmanci. Iskar ƙuna, iska ce da ba ta da kala kuma ba ta da ƙanshi amma tana kashe mutane ta wajen sa jajayen ƙwayoyin jininsu ya daina kai iskar shaƙa cikin jiki. Idan ba a gaya wa masu ceton game da haɗarin ba, suna iya sumewa kuma su mutu ba tare da sanin cewa sun shaƙa iska mai guba ba.
2 A hanya ta ruhaniya, Kiristoci suna fuskantar yanayi irin na masu haƙa kwal. Ta yaya? Sa’ad da Yesu ya ba almajiransa aikin wa’azin bishara a dukan duniya, ya san yana aika su zuwa cikin yanayi mai haɗari, wanda Shaiɗan da ruhun duniya ke rinjaya. (Mat. 10:16; 1 Yoh. 5:19) Yesu ya damu da almajiransa da ya sa daddare kafin ya mutu, ya yi addu’a ga Ubansa: “Ba na yin addu’a ka ɗauke su daga cikin duniya ba, amma domin ka tsare su daga Mugun.”—Yoh. 17:15.
3, 4. Wane kashedi ne Yesu ya yi wa almajiransa, me ya sa za mu mai da hankali ga wannan?
3 Yesu ya yi wa mabiyansa gargaɗi game da haɗarin abin da zai sa su yi sanyi a ruhaniya. Tun da yake muna zama a zamanin ƙarshe, kalmominsa suna da ma’ana na musamman a gare mu. Ya aririce almajiransa: “A kowane loto sai ku yi tsaro, kuna yin roƙo ku sami ikon da za ku tsere ma dukan waɗannan al’amuran da za su faru, ku tsaya kuma a gaban Ɗan mutum.” (Luk 21:34-36) Abin farin ciki, Yesu ya yi alkawari cewa Ubansa zai ba da ruhu mai tsarki don ya tuna musu abubuwa da suka koya kuma ya sa su kasance a faɗake su ƙarfafa.—Yoh. 14:26.
4 Mu kuma fa a yau? Za mu iya samun taimakon wannan ruhu mai tsarki? Idan haka ne, menene za mu yi don mu sami taimakonsa? Menene ruhun wannan duniyar, kuma yaya yake aiki? Ta yaya za mu ƙi ruhun wannan duniya?—Ka karanta 1 Korantiyawa 2:12.
Ruhu Mai Tsarki ko Ruhun Duniya?
5, 6. Menene ruhu mai tsarki zai iya yi mana, menene za mu yi don mu samu taimakonsa?
5 Ba mutane na ƙarni na farko ba ne kawai suka sami taimakon ruhu mai tsarki. Muna iya samunsa a yau, kuma ruhun Allah zai iya ba mu ƙarfin yin abin da yake da kyau kuma ya ƙarfafa mu a hidimarsa. (Rom. 12:11; Filib. 4:13) Zai sa mu kasance da halaye masu kyau kamar ƙauna, alheri, nagarta, waɗannan fannoni ne na “ɗiyan Ruhu.” (Gal. 5:22, 23) Amma, Jehobah Allah ba ya tilasta wa waɗanda ba sa so su samu ruhunsa mai tsarki.
6 Saboda haka, zai dace mu yi tambaya, ‘Menene zan yi don na samu ruhu mai tsarki?’ Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa da abubuwa da yawa da za mu iya yi. Wani mataki mai muhimmanci shi ne ka roƙi Allah ya ba ka ruhunsa. (Ka karanta Luka 11:13.) Wata hanya kuma ita ce yin nazari da kuma yin amfani da gargaɗin Kalmar Allah da ruhu ya hure. (2 Tim. 3:16) Hakika, ba kowa ba ne da yake karanta Littafi Mai Tsarki yake samun ruhun Allah. Amma sa’ad da Kirista ya yi nazarin Kalmar Allah, zai iya fahimtar abubuwan da ake nufi da ra’ayin hurarriyar Kalmar. Yana da muhimmanci mu fahimci cewa Jehobah ya naɗa Yesu wakilinsa da kuma wanda ta wurinsa Allah yake ba da ruhunsa. (Kol. 2:6) Saboda haka, ya kamata mu bi misalin Yesu da koyarwarsa. (1 Bit. 2:21) Idan mun ƙara yin ƙoƙari mu zama kamar Kristi, za mu ƙara samun ruhu mai tsarki.
7. Ta yaya ne ruhun duniya yake shafan mutane?
7 Akasin haka, ruhun duniya na sa mutane su nuna halin Shaiɗan. (Ka karanta Afisawa 2:1-3.) Ruhun duniya yana aiki a hanyoyi da yawa. Kamar yadda muke gani a ko’ina a yau, ruhun duniya na ƙarfafa yin tawaye ga mizanan Allah. Yana ɗaukaka “sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne.” (1 Yoh. 2:16) Yana sa a bi sha’awoyi na jiki kamar fasikanci, bautar gunki, sihiri, kishi, fushi, da maye. (Gal. 5:19-21) Yana ɗaukaka furcin ridda da ke lalata abin da yake da tsarki. (2 Tim. 2:14-18) Hakika, idan mutum ya bar ruhun duniya ya shige shi, hakan zai sa ya yi koyi da halayen Shaiɗan.
8. Wane zaɓi ne kowanenmu yake bukata ya yi?
8 Ba zai yiwu mu kaɗaita kanmu ba. Kowane mutum zai zaɓi abin da zai bari ya ja-goranci rayuwarsa, wato ruhu mai tsarki ko ruhun duniya. Waɗanda ruhun duniya ya sha kansu suna iya gujewa daga gare sa kuma su bari ruhu mai tsarki ya ja-goranci rayuwarsu. Amma, barin ruhun duniya ya ja-gorance mu yana iya yiwuwa. Ruhun duniya yana iya rinjayar waɗanda ruhu mai tsarki yake ja-gorarsu. (Filib. 3:18, 19) Bari mu tattauna yadda za mu iya guje wa ruhun duniya.
Fahimtar Alamu na Farko
9-11. Waɗanne alamu ne za su iya nuna cewa muna barin ruhun duniya ta rinjaye mu?
9 Masu haƙa kwal a Britaniya da aka ambata ɗazu suna amfani da kanari don su ba da alama da sauri cewa akwai iska da ta gurɓata. Idan mahaƙi ya ga tsuntsu ya faɗi daga inda aka aje shi, zai sani cewa yana bukatar ya aikata da sauri don ya tsira. A rayuwarmu ta Kirista, waɗanne alamu ne na farko suke nuna mana cewa ruhun duniya ne yake ja-gorarmu?
10 Sa’ad da muka fara sanin gaskiya ta Kalmar Allah kuma muka keɓe kanmu ga Jehobah, wataƙila muna ƙosa mu karanta Littafi Mai Tsarki. Wataƙila muna yin addu’a sosai a kai a kai. Kuma muna yin farin cikin zuwa taro na ikilisiya, muna ganin kowa kamar tushin wartsakewa na ruhaniya, kamar yadda ruwa yake ga mutum mai jin kishi. Hakan zai sa mu guji ruhun duniya.
11 Muna ƙoƙari mu karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana kuwa? (Zab. 1:2) Muna yin addu’o’inmu sosai kuma a kai a kai kuwa? Muna son zuwa taron ikilisiya, kuma mu halarci dukan taron kuwa? (Zab. 84:10) Ko kuma mun mance wasu daga cikin waɗannan ayyuka masu kyau? Hakika, muna da hakki da yawa da suke bukatar lokacinmu da kuzarinmu, kuma yakan yi wuya mu riƙe tsarin ayyuka na ruhaniya. Amma idan halayenmu masu kyau suka yi sanyi fa, zai iya yiwuwa cewa ruhun duniya ya rinjaye mu ne? Muna bukatar mu yi ƙoƙari mu dawo da halayenmu masu kyau da muke da su a dā.
‘Kada Ka Yi Nauyi’
12. A kan menene Yesu ya gaya wa almajiransa su mai da “hankali,” kuma me ya sa?
12 Menene kuma za mu yi don mu ƙi ruhun duniya? Sa’ad da Yesu ya aririci almajiransa su “yi tsaro,” ba da daɗewa ba ya riga ya yi musu gargaɗi game da wasu haɗari. Ya ce: “Ku yi hankali da kanku, kada ya zama zukatanku su yi nauyi da zarin ci da maye da shagulgula na wannan rai, har ranan nan ta hume ku, ba labari, kamar tarko.”—Luka 21:34, 35.
13, 14. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu game da cin abinci da shaye-shaye?
13 Ka yi tunanin wannan gargaɗi. Yesu ya hana cin abinci da abin sha ne? A’a! Yana sane da kalaman Sulemanu: “Na sani babu abin da ya fi masu [’yan adam], kamar su yi murna, su kāma aika nagarta dukan kwanakin ransu. Kowane mutum kuma shi ci, shi sha, shi ji daɗi cikin dukan aikinsa; wannan kyautar Allah ne.” (M. Wa. 3:12, 13) Duk da haka, Yesu ya san cewa ruhun duniya yana ɗaukaka rashin kama kai a waɗannan abubuwa.
14 Ta yaya za mu iya tabbata cewa ruhun duniya bai lalata mana ra’ayi game da zarin ci da yin maye ba? Za mu iya tambayar kanmu: ‘Yaya nake yi idan na karanta umurni daga cikin Littafi Mai Tsarki ko kuma a littattafanmu game da zarin ci? Ina yin banza da wannan gargaɗi ko kuma in ba da hujja na yin hakan?a Menene ra’ayi na game da shawarar da aka bayar game da giya, shan sa daidai yadda ya kamata da kuma guje wa “maye”? Ina ƙin bin shawara, don ina ganin cewa bai shafe ni ba? Idan wasu suka yi mini magana game da shaye-shayen da nake yi, ina ba da hujja ko kuma in yi fushi? Ina ƙarfafa wasu su ƙi bin wannan umurni na Littafi Mai Tsarki?’ Hakika, halin mutum alama ce da take nuna cewa yana ƙyale ruhun duniya ta rinjaye shi.—Ka gwada Rom. 13:11-14.
Ka Guji Yawan Alhini
15. Game da wane halin ’yan adam ne Yesu ya yi kashedi?
15 Wani mataki mai muhimmanci na ƙin ruhun wannan duniya ya ƙunshi yadda muke bi da alhini. Yesu ya san cewa da yake mu ajizai ne, muna da halin damuwa game da abin duniya. Ya gaya wa almajiransa: “Kada ku yi alhini.” (Mat. 6:25) Daidai ne mu damu game da batutuwa masu muhimmanci, kamar faranta wa Allah rai, kula da hakkinmu na Kirista, da yi wa iyalinmu tanadin abin biyan bukata. (1 Kor. 7:32-34) Menene za mu iya koya daga gargaɗin Yesu?
16. Ta yaya ruhun duniya yake shafan mutane da yawa?
16 Ruhun duniya mai yawan ɗaukaka sha’awar idanu na sa mutane su riƙa yin alhini da bai da kyau don zaman lafiyarsu. Za su so mu gaskata cewa kuɗi yana kawo kwanciyar rai kuma ana gwada darajar mutum da yawan dukiyarsa ba da halayensa na ruhaniya ba. Waɗanda aka ruɗe su da wannan ra’ayin za su yi ta aiki don su samu kuɗi kuma koyaushe suna damuwa game da sayan sababbi da manyan kaya. (Mis. 18:11) Wannan ra’ayin da bai dace ba game da abin duniya na kawo alhini da ke hana mutum samun ci gaba a ruhaniya.—Ka karanta Matta 13:18, 22.
17. Ta yaya za mu guji yawan alhini?
17 Za mu guji yawan alhini idan mun yi biyayya da umurnin Yesu: ‘Ku fara biɗan mulkin, da adalcin Allah.’ Yesu ya tabbatar mana cewa idan mun yi hakan, za a ƙara mana ainihin abubuwan da muke bukata. (Mat. 6:33) Ta yaya za mu nuna mun gaskata da wannan alkawarin? Hanya ɗaya ita ce ta wajen fara biɗan adalcin Allah, mu bi mizanan Allah na abin da ya dace game da batutuwan kuɗi. Alal misali, ba za mu yi ƙarya game da kuɗin haraji da muka karɓa ba ko kuma a sha’aninmu na kasuwanci ba. Za mu yi iya ƙoƙarinmu mu cika alkawarinmu, mu sa ‘zancenmu i ya zama i’ idan ya zo ga biyan bashi. (Mat. 5:37; Zab. 37:21) Faɗan gaskiya ba zai sa mutum ya yi arziki ba, amma yana kawo amincewar Allah, yana sa mutum ya kasance da lamiri mai tsabta, kuma ya rage yawan alhini.
18. Wane misali ne Yesu ya kafa mana, ta yaya muka amfana ta wajen yin koyi da shi?
18 Fara biɗan Mulki ya ƙunshi sanin abin da ya kamata ya fi muhimmanci a rayuwarmu. Ka yi la’akari da misalin Yesu. Wani lokaci yana saka tufafi mai tsada. (Yoh. 19:23) Ya ci abinci kuma ya sha inabi tare da abokane. (Mat. 11:18, 19) Dukiya da nishaɗi suna kama da kayan ƙanshi a rayuwarsa, ba ainihin abincin ba. Yin nufin Jehobah ne abincin Yesu. (Yoh. 4:34-36) Rayuwa tana da ma’ana idan muka bi misalin Yesu! Muna farin cikin taimakon gajiyayyu su sami ta’aziyya daga Nassosi. Muna samun taimako da ƙauna daga ikilisiya. Kuma muna faranta wa Jehobah rai. Sa’ad da muka saka abubuwa da suka fi muhimmanci a gaba, ba za mu riƙa damuwa ainun game da dukiya da nishaɗi ba. Za su zama bayi ko kayan aiki da suke taimakonmu wajen bauta wa Jehobah. Idan muna ƙwazo a aiki da ke tallafa wa Mulkin Allah, za mu guji ruhun wannan duniya.
Ka Ci Gaba da “Himmantuwar Ruhu”
19-21. Ta yaya za mu ci gaba da “himmantuwar ruhu” kuma me ya sa za mu yi hakan?
19 Muna yin abubuwa da muka yi tunaninsa. Sau da yawa tunani ne suke motsa ayyukan banza. Shi ya sa manzo Bulus ya tuna mana cewa muna bukatar mu tsare tunaninmu. Ya rubuta: “Waɗanda ke bisa tabi’ar jiki al’amuran jiki su ke tattali; amma waɗanda ke bisa tabi’ar ruhu, al’amuran ruhu ne.”—Rom. 8:5.
20 Ta yaya za mu guje wa ruhun duniya don kada ya sha kan tunaninmu da ayyukanmu? Dole ne mu kāre tunaninmu, mu yi ƙoƙari mu kawar da ra’ayin duniya yadda zai yiwu. Alal misali, sa’ad da muke zaɓan nishaɗi, ba za mu bar tsarin ayyuka na Talabijin da ke ɗaukaka lalata ko mugunta su ɓata zuciyarmu ba. Mun sani cewa ruhu mai tsarki na Allah ba zai kasance a cikin zuciya marar tsabta ba. (Zab. 11:5; 2 Kor. 6:15-18) Ƙari ga haka, muna sa ruhun Allah ya kasance cikin zuciyarmu ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai, yin addu’a, bimbini, da kuma halartar taro. Muna aiki tare da wannan ruhun sa’ad da muke aikin wa’azi na Kirista a kai a kai.
21 Babu shakka, dole ne mu ƙi ruhun wannan duniya da sha’awoyi da yake ɗaukakawa. Amma yin haka ya dace domin Bulus ya ce, “himmantuwar jiki mutuwa ce: amma himmantuwar ruhu rai ne da lafiya.”—Rom. 8:6.
[Hasiya]
a Zarin ci ra’ayi ne daga zuciya mai haɗama ko kuma yawan shaye-shaye. Ana sanin mai zarin ci ta halinsa game da abinci ba don yawan girmansa ba. Mutum na iya kasancewa marar jiki ko kuma tsiriri amma yana zarin ci. A wani bangare, yawan jiki ciwo ne, ko kuma idan yana jinin iyali zai iya kai ga yawan jiki. Batu mai muhimmanci a nan shi ne zarin ci, ko mutumin mai jiki ne ko marar jiki.—Ka duba “Questions From Readers” a fitowar Hasumiyar Tsaro na 1 ga Nuwamba, 2004.
Ka Tuna?
• Menene ya kamata mu yi don mu samu ruhu mai tsarki?
• A waɗanne hanyoyi ne ruhun wannan duniya zai shafe mu?
• Ta yaya za mu ƙi ruhun wannan duniya?
[Hoto a shafi na 21]
Kafin ka je aiki ko makaranta ka yi addu’a don ruhu mai tsarki
[Hotuna a shafi na 23]
Dole ne mu sa zuciyarmu ta kasance da tsabta, mu yi ayyukan kasuwanci mai kyau, kuma mu kasance da halaye masu kyau