Annabcin Yusha’u Yana Taimakonmu Mu Bi Allah
“Za su bi Ubangiji.”—YUSHA’U 11:10.
1. Wane wasan kwaikwayo na alama yake cikin littafin Yusha’u?
KANA jin daɗin wasan kwaikwayo da ’yan wasan, mutane ne masu ban sha’awa? Littafin Yusha’u na Littafi Mai Tsarki na ɗauke da wasan kwaikwayo na alama.a Wannan wasan kwaikwayon game da yanayin iyalin annabin Allah, Yusha’u ne, kuma yana da dangantaka ta aure na alama da Jehobah ya yi da al’ummar Isra’ila ta dā ta wurin alkawari na Dokar Musa.
2. Menene tarihin Yusha’u?
2 Tushen wannan wasan kwaikwayon yana cikin littafin Yusha’u sura ta 1. Kamar dai Yusha’u ya rayu ne a yankin ƙabilu goma na Isra’ila (kuma ana kiransa Ifraimu domin ya yi fice). Ya yi annabci a lokacin sarakuna bakwai na ƙarshe na Isra’ila da kuma Sarki Yahuza, Azariya, Yotam, Ahaz, da Hezekiya. (Yusha’u 1:1) Da haka Yusha’u ya yi annabci na aƙalla shekaru 59. Ko da an kammala littafi mai ɗauke da sunansa ba da daɗewa ba bayan shekara ta 745 K.Z., yana da amfani a yau da yake mutane da yawa suna biɗan tafarki kamar wanda aka annabta a wannan kalmomi: “Za su bi Ubangiji.”—Yusha’u 11:10.
Abin da Taƙaitaccen Bayani Ya Nuna
3, 4. Ka ɗan ba da bayanin abin da yake cikin littafin Yusha’u sura ta 1 zuwa ta 5.
3 Ɗan taƙaitaccen bayani a Yusha’u sura ta 1 zuwa ta 5 za su ƙarfafa ƙudurinmu mu bi Allah ta wajen kasancewa da bangaskiya da kuma biɗan tafarki da ya yi daidai da nufinsa. Ko da mazauna masarautar Isra’ila sun zama masu alhakin zina na ruhaniya, Allah zai yi musu jinƙai idan suka tuba. An kwatanta wannan da yadda Yusha’u ya bi da matarsa, Gomer. Bayan ta haifa masa ɗa, ta yi cikin shege ta haifi ’ya’ya biyu. Duk da haka, Yusha’u ya sake aurenta, yadda Jehobah ya kasance a shirye ya yi wa Isra’ilawa da suka tuba jinƙai.—Yusha’u 1:1–3:5.
4 Jehobah yana da magana da Isra’ila domin ba sa bin gaskiya, babu ƙaunar alheri, ko sanin Allah a ƙasar. Zai hukunta Isra’ila mai karuwanci da kuma masarautar Yahuza mai taurin kai. Amma sa’ad da mutanen Allah suke cikin ‘ƙunci’ za su nemi Jehobah.—Yusha’u 4:1–5:15.
An Soma Wasan Kwaikwayon
5, 6. (a) Yaya yawan yadda fasikanci ya yaɗu a masarautar ƙabilu goma na Isra’ila? (b) Me ya sa gargaɗin da aka yi wa Isra’ila ta dā yake da muhimmanci a gare mu?
5 “Tafi,” Allah ya gargaɗi Yusha’u, “ka auro karuwa, ka haifi ’ya’yan karuwanci, gama ƙasar tana yin fasikanci sosai, wato ta bar bin Ubangiji.” (Yusha’u 1:2) Yaya yawan yadda fasikanci ya yaɗu a Isra’ila? An gaya mana: “Ruhun karuwanci ya ɓad da [mutanen masarautar ƙabila goma], sun rabu da Allahnsu don su yi karuwanci. . . . ’Ya’yanku mata suke karuwanci, surukanku mata suke yin zina. . . . Mazan da kansu sukan shiga wurin karuwai. Sukan miƙa sadaka tare da karuwai a Haikali.”—Yusha’u 4:12-14.
6 Fasikanci na ruhaniya da kuma na zahiri ya yaɗu a Isra’ila. Saboda haka Jehobah zai ‘hukunta’ Isra’ila. (Yusha’u 1:4; 4:9) Wannan gargaɗin yana da ma’ana a gare mu domin Jehobah zai hukunta waɗanda suke yin lalata kuma suke saka hannu a bauta marar tsarki a yau. Amma waɗanda suke bin Allah kuma suke cika mizanansa don bauta mai tsarki sun san cewa “ba wani fasiki . . . [da] ke da gādo a mulkin Almasihu da na Allah.”—Afisawa 5:5; Yakubu 1:27.
7. Menene auren da Yusha’u ya yi da Gomer yake nunawa?
7 Babu shakka, Gomer budurwa ce sa’ad da Yusha’u ya aure ta, kuma mace ce mai aminci a lokacin da “ta haifa masa ɗa namiji.” (Yusha’u 1:3) Yadda aka nuna a wasan kwaikwayo na alama, ba da daɗewa ba bayan an ’yantar da Isra’ila daga bauta a ƙasar Masar a shekara ta 1513 K.Z., Allah ya yi alkawari da su kamar na wa’adin aure mai tsarki. Da yake ta yarda da wa’adin, Isra’ila ta yi alkawari za ta kasance da aminci ga ‘mijinta’ Jehobah. (Ishaya 54:5) Hakika, aure mai tsarki da Yusha’u ya yi da Gomer yana kwatanta aure na alama da Isra’ila ta yi da Allah. Amma abubuwa sun canja!
8. Ta yaya aka kafa masarautar ƙabilu goma ta Isra’ila, kuma ta yaya take bauta?
8 Matar Yusha’u “ta kuma ɗauki ciki, ta haifi ’ya mace.” Wataƙila Gomer ta haifi wannan yarinya da wanda ke bin bayanta ta wurin zina. (Yusha’u 1:6, 8) Da yake Gomer alama ce ta Isra’ila, kana iya tambaya, ‘Ta yaya Isra’ila ta zama karuwa?’ A shekara ta 997 K.Z., ƙabilu goma na Isra’ila suka ware kansu daga ƙabilun Yahuza da Biliyaminu. Aka kafa bautar ɗan maraƙi a masarautar ƙabilu goma na Isra’ila don kada mutanen su je Yahuza su bauta wa Jehobah a haikalinsa da ke Urushalima. Bautar allahn ƙarya Ba’al da ta ƙunshi jima’i ta kahu ta yi jijiya a Isra’ila.
9. Menene ya faru da Isra’ila kamar yadda aka annabta a Yusha’u 1:6?
9 Da Gomer ta haifi ’yarta ta biyu ta karuwanci, Allah ya gaya wa Yusha’u: “Ka raɗa mata suna Ba-jinƙai, gama ba zan ƙara yi wa jama’ar Isra’ila jinƙai ba, har da zan gafarta mata.” (Yusha’u 1:6) Jehobah ‘bai gafarta musu ba’ da yake Assuriyawa sun kwashi Isra’ilawa zuwa bauta a shekara ta 740 K.Z. Amma Allah ya yi wa masarautar ƙabilu biyu ta Yahuza jinƙai kuma ya cece su ba da baka ba, ba kuwa da takobi, ko da yaƙi, ko da dawakai, ko da sojojin dawakai ba. (Yusha’u 1:7) A cikin dare ɗaya a shekara ta 732 K.Z., mala’ika guda ya kashe sojojin Assuriya guda 185,000, waɗanda suke yi wa Urushalima, babban birnin Yahuza barazana.—2 Sarakuna 19:35.
Hukuncin Jehobah Bisa Isra’ila
10. Menene karuwancin Gomer ya kwatanta?
10 Gomer ta bar Yusha’u ta zama “karuwa,” tana yin fasikanci da wani mutum. Wannan ya kwatanta yadda masarautar Isra’ila ta soma tarayya na siyasa da al’ummai masu bautar gumaka kuma suka dogara da su. Maimakon ta yabi Jehobah don ni’imarta, Isra’ila ta yabi allolin al’ummai kuma ta taka alkawarinta da Allah ta wajen saka hannu a bautar ƙarya. Shi ya sa Jehobah ya hukunta al’umma mai karuwanci a ruhaniya!—Yusha’u 1:2; 2:2, 12, 13.
11. Menene ya faru da Dokar alkawari sa’ad da Jehobah ya ƙyale aka kwashi Isra’ila da Yahuza zuwa bauta?
11 Wace wahala Isra’ila ta sha domin ta bar Mijinta? Allah ya “kai ta cikin jeji” na Babila, al’ummar da ta ci Assuriya wadda ta kwashi Isra’ilawa bauta a shekara ta 740 K.Z. (Yusha’u 2:14) Sa’ad da Jehobah ya kawo ƙarshen masarautar ƙabilu goma, bai manta da wa’adin aure da ya yi da ƙabilu 12 na Isra’ila na asali ba. Sa’ad da Allah ya ƙyale Babiloniyawa suka halaka Urushalima a shekara ta 607 K.Z., kuma ya ƙyale aka kwashi mutanen Yahuza zuwa bauta, bai kawar da Dokar Musa da ta halalta aurensa na alama da ƙabilu 12 na Isra’ila ba. An kawar da wannan dangantakar bayan shugabannin Yahuza suka ƙi Yesu Kristi kuma suka kashe shi a shekara ta 33 A.Z.—Kolosiyawa 2:14.
Jehobah ya Yi wa Isra’ila Gargaɗi
12, 13. Menene ma’anar kalmomin Yusha’u 2:6-8, kuma yaya waɗannan kalmomi suka shafi Isra’ila?
12 Allah ya yi wa Isra’ila gargaɗi ta “daina karuwancinta,” amma tana so ta bi samarinta. (Yusha’u 2:2, 5) “Don haka” in ji Jehobah “zan shinge hanyarta da ƙaya, zan gina mata garu don kada ta sami hanyar fita. Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba. Za ta neme su, amma ba za ta same su ba. Sa’an nan za ta ce, ‘zan koma wurin mijina na fari, gama zamana na dā ya fi na yanzu!’ ‘Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai, da azurfa, da zinariya da yawa waɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba’al da su ba.”—Yusha’u 2:6-8.
13 Ko da Isra’ila ta nemi taimakon “samarinta” wato al’ummai, babu wani cikinsu da ya taimake ta. An kewaye ta kamar dajin ƙaya da ba a shiga, domin haka ba su iya taimakonta ba. Bayan da Assuriya ta yi wa Samariya babban birnin Isra’ila kwanton ɓauna na shekara uku, sai ta miƙa kai a shekara ta 740 K.Z., kuma ba a sake kafa masarautar ƙabila goma ba. Wasu ne kawai cikin Isra’ilawa da aka kwashe zuwa bauta za su fahimci yadda yanayin yake da kyau sa’ad da kakaninsu suka bauta wa Jehobah. Waɗannan da suka rage za su ƙi bautar Ba’al kuma su sake sabonta dangantakarsu da Jehobah.
Kallon Wasan a Wata Hanya
14. Me ya sa Yusha’u ya sabonta soyayyarsa da Gomer?
14 Don ka fahimci alaƙa da ke tsakanin iyalin Yusha’u da dangantakar Isra’ila da Jehobah, ka yi la’akari da waɗannan kalmomi: “Ubangiji kuma ya ce mini, ‘Ka sāke tafiya, ka ƙaunaci karuwa wadda take tare da kwartonta.’ ” (Yusha’u 3:1) Yusha’u ya yi biyayya da wannan umurnin ta wajen sake aurar Gomer daga mutumin da take zama da shi. Bayan haka Yusha’u ya gargaɗi matarsa: “Ki keɓe kanki kwanaki da yawa domina, kada ki yi kwartanci, ki kwana da wani.” (Yusha’u 3:2, 3) Gomer ta amince da horon kuma Yusha’u ya sabonta soyayyarsa da ita. Ta yaya wannan ya yi daidai da sha’anin da Allah yake yi da mutanen Isra’ila da Yahuza?
15, 16. (a) A wane yanayi ne Allah zai yi wa al’ummar da ya hukunta jinƙai? (b) Ta yaya Yusha’u 2:18 ta cika?
15 Ko da an kwashi Isra’ila da Yahuza bauta zuwa Babila, Allah ya yi amfani da annabawansa ya yi musu “magana.” Don Allah ya yi musu jinƙai, mutanensa suna bukatar su nuna sun tuba kuma sun koma ga Mijinsu, yadda Gomer ta koma wurin mijinta. Sa’annan Jehobah zai amince da al’ummarsa da take kama da mace da ya yi wa horo kuma ya ɗauke ta daga “jeji” na Babila kuma ya dawo da ita Yahuza da Urushalima. (Yusha’u 2:14, 15) Ya cika wannan alkawari a shekara ta 537 K.Z.
16 Allah ya kuma cika wannan alkawarin: “A waccan rana zan yi alkawari da namomin jeji, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe saboda Isra’ila. Zan kuma kakkarya baka da takobi, in kuma sa yaƙi ya ƙare a ƙasar, sa’an nan za su yi zamansu lami lafiya.” (Yusha’u 2:18) Raguwar Yahudawa da suka dawo ƙasarsu sun yi zama cikin kwanciyar hankali, ba su ji tsoron dabbobi ba. Wannan annabci ya cika a shekara ta 1919 A.Z., sa’ad da aka ’yantar da waɗanda suka rage a Isra’ila ta ruhaniya daga “Babila Babba,” daular duniya na addinan ƙarya. Yanzu suna zama cikin kwanciyar hankali kuma suna more rayuwa cikin aljanna na ruhaniya da abokansu, waɗanda suke da begen zama a duniya har abada. Waɗannan Kiristoci na gaskiya ba su da hali irin na dabba.—Wahayin Yahaya 14:8; Ishaya 11:6-9; Galatiyawa 6:16.
Ka Riƙa Tunawa da Darussan
17-19. (a) Waɗanne halaye na Allah aka aririce mu mu yi koyi da su? (b) Yaya ya kamata jinƙan Jehobah da juyayinsa su shafe mu?
17 Allah mai jinƙai ne da kuma juyayi, kuma haka mu ma ya kamata mu zama. Darassin da surorin littafin Yusha’u na farko suka koyar ke nan. (Yusha’u 1:6, 7; 2:23) Yadda Allah ya kasance a shirye ya yi wa Isra’ilawa da suka tuba jinƙai ya jitu da karin magana da aka hure: “Ba za ka taɓa cin nasara a zamanka ba muddin kana ɓoye laifofinka. Ka hurta zunubanka ka tuba, sa’an nan Allah zai yi maka jinƙai.” (Karin Magana 28:13) Kalmomin mai zabura na da ban ƙarfafa ga miyagu da suka tuba: “Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah, zuciya mai ladabi da biyayya, ba za ka ƙi ba, ya Allah.”—Zabura 51:17.
18 Annabcin Yusha’u ya nuna cewa Allah da muke bauta wa mai juyayi ne kuma mai jinƙai. Ko idan wasu sun bijire daga hanyoyinsa na adalci, suna iya tuba kuma su juyo wajensa. Idan sun yi hakan, Jehobah zai marabce su. Ya yi wa waɗanda suka tuba cikin al’ummar Isra’ila da ya yi aure na alama da ita jinƙai. Ko da sun yi wa Jehobah rashin biyayya da kuma ‘sa Mai Tsarki na Isra’ila yin fushi, yakan tuna su mutane ne kawai.’ (Zabura 78:38-41) Ya kamata irin wannan jinƙai ya motsa mu mu ci gaba da bin Jehobah Allahnmu mai juyayi.
19 Ko da zunubai kamar su kisa, sata, da zina sun zama ruwan dare gama gari a Isra’ila, Jehobah ya “ba ta magana.” (Yusha’u 2:14; 4:2) Ya kamata zuciyarmu ta motsa kuma dangantakarmu da Jehobah ta ƙarfafa yayin da muka yi tunani game da jinƙansa da kuma juyayi. Saboda haka, bari mu tambayi kanmu: ‘Ta yaya zan yi koyi sosai da jinƙan Jehobah kuma in kasance da juyayi sa’ad da nake sha’ani da wasu? Idan wani Kirista da ya yi mini laifi ya nemi gafara, ina kasancewa a shirye in gafarta masa yadda Allah yake yi?’—Zabura 86:5.
20. Ka ba da misali da ya nuna cewa ya kamata mu amince da begen da Allah ya yi alkawarinsa.
20 Allah ya ba da bege na gaskiya. Alal misali, ya yi alkawari: “Zan ba ta . . . kwarin Akor, wato wahala, ƙofar bege.” (Yusha’u 2:15) Ƙungiyar Jehobah ta dā wadda take kama da mace tana da tabbataccen bege cewa za a mai da ta ƙasarsu, inda “kwarin Akor” yake. Cikar wannan alkawari a shekara ta 537 K.Z., ya ba mu dalilin farin ciki ga bege da Jehobah ya kafa a gabanmu.
21. Yaya sani yake taimakonmu mu ci gaba da bin Allah?
21 Don mu ci gaba da bin Allah, muna bukatar mu ƙara saninsa kuma mu yi amfani da sanin a rayuwarmu. Isra’ila ba ta da sanin Jehobah. (Yusha’u 4:1, 6) Duk da haka, wasu sun ɗauki koyarwar Allah da tamani, suka aikata cikin jituwa da shi, kuma aka albarkace su. Yusha’u yana ɗaya daga cikin waɗannan. Da kuma mutane 7,000 na zamanin Iliya da ba su bauta wa Ba’al ba. (1 Sarakuna 19:18; Romawa 11:1-40) Yin godiya game da koyarwar Allah zai taimake mu mu ci gaba da bin Allah.—Zabura 119:66; Ishaya 30:20, 21.
22. Yaya ya kamata mu ɗauki ridda?
22 Jehobah yana bukatar mutane da suke shugabanci tsakanin mutanensa su ƙi ridda. Amma, Yusha’u 5:1 ta ce: “Ku ji wannan, ya ku firistoci! Ku saurara, ya mutanen Isra’ila! Ku kasa kunne, ya gidan sarki! Gama za a yi muku hukunci, domin kun zama tarko a Mizfa, da ragar da aka shimfiɗa a bisa Tabor.” Shugabanni masu ridda tarko ne da kuma raga ga Isra’ilawa, suna jarabarsu su yi bautar gumaka. Dutsen Tabor da kuma wani wuri da ake kira Mizfa cibiyar irin wannan bautar ƙarya ne.
23. Ta yaya ka amfana daga nazari na Yusha’u sura ta 1 zuwa ta 5?
23 Annabcin Yusha’u ya nuna mana cewa Jehobah Allah ne mai jinƙai, wanda yake ba da bege kuma yake yi wa waɗanda suke bin umurninsa, suke kuma ƙin ridda albarka. Kamar Isra’ilawa na dā da suka tuba, bari mu nemi Jehobah kuma mu yi ƙoƙari mu faranta masa rai. (Yusha’u 5:15) Ta yin haka, za mu sami alheri kuma mu sami farin ciki da salama da babu na biyunsu da waɗanda suke bin Allah cikin aminci suke samu.—Zabura 100:2; Filibiyawa 4:6, 7.
[Hasiya]
a An nuna wasan kwaikwayo na alama a Galatiyawa 4:21-26. Game da wannan, ka duba littafin nan Insight on the Scriptures Littafi na 2, shafuffuka na 693-694, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Ta Yaya Za Ka Amsa?
• Menene auren Yusha’u ga Gomer ke nunawa?
• Me ya sa Jehobah ya hukunta Isra’ila?
• Wane darasi a Yusha’u sura ta 1 zuwa ta 5 ya burge ka?
[Hoto a shafi na 4]
Ka san wadda matar Yusha’u take nunawa?
[Hoto a shafi na 5]
Assuriyawa sun ci mazauna Samariya a shekara ta 740 K.Z.
[Hoto a shafi na 6]
Mutane masu farin ciki sun koma ƙasarsu