Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 12/1 pp. 13-17
  • “Hanyoyin Ubangiji Masu Gaskiya Ne”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Hanyoyin Ubangiji Masu Gaskiya Ne”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Yana Bukatar Bauta Marar Riya
  • Allah Yana Nuna wa Mutanensa Ƙauna ta Aminci
  • Ka Yi Begen Jehobah Kullayaumi
  • Hanyoyin Jehobah Koyaushe Masu Adalci Ne
  • Masu Zunubi Suna Iya Komawa ga Jehobah
  • Ka Ci Gaba da Bin Hanyoyin Jehobah na Adalci
  • Darussa Daga Littafin Hosea
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Annabcin Yusha’u Yana Taimakonmu Mu Bi Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ka Bi Allah, Ka Sami Alheri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Hosiya
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 12/1 pp. 13-17

“Hanyoyin Ubangiji Masu Gaskiya Ne”

“Hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne, masu adalci kuwa za su yi tafiya a cikinsu.”—YUSHA’U 14:9.

1, 2. Yaya Jehobah ya kafa Isra’ila, kuma menene ya faru da su?

JEHOBAH ya kafa Isra’ila bisa adalci a zamanin annabi Musa. Amma, a farkon ƙarni na takwas K.Z., yanayinsu ya daɗa muni ƙwarai da Allah ya kama su da laifi mai tsanani. Wannan ya bayyana a cikin Yusha’u sura ta 10 zuwa ta 14.

2 Zuciyar Isra’ila ta zama mai riyya. Mutanen masarautar ƙabila goma sun “shuka mugunta” kuma sun girbe rashin adalci. (Yusha’u 10:1, 13) Jehobah ya ce: “lokacin da Isra’ila ke yaro, na ƙaunace shi, daga cikin Masar na kirawo ɗana.” (Yusha’u 11:1) Ko da yake Allah ya ceci Isra’ilawa daga hannun Masarawa, sun biya shi da ƙarya da yaudara. Shi ya sa Jehobah ya yi musu wannan gargaɗi: “Ku koma wurin Allahnku, ku yi alheri, ku yi adalci.”—Yusha’u 12:6.

3. Menene zai faru da Samariya mai tawaye, amma yaya Isra’ilawa za su sami jinƙai?

3 Samariya mai tawaye da sarkinta za su kai ƙarshensu cikin bala’i. (Yusha’u 13:11, 16) Sura ta ƙarshe ta annabcin Yusha’u ta fara ne da wannan roƙo: “Ya mutanen Isra’ila, ku komo wurin Ubangiji Allahnku.” Idan Isra’ilawa za su tuba, Allah zai yi musu jinƙai. Hakika, suna bukatar su sani cewa “hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne,” kuma su bi ta.—Yusha’u 14:1-6, 9.

4. Waɗanne ƙa’idodi ne za mu bincika daga annabcin Yusha’u?

4 Wannan sashe na annabcin Yusha’u na ɗauke da ƙa’idodi da yawa da za su taimake mu mu bi Allah. Za mu bincika waɗannan: (1) Jehobah yana bukatar bauta marar riyya, (2) Allah na nuna wa mutanensa ƙauna ta aminci, (3) muna bukatar mu kasance da bege ga Jehobah kullayaumi, (4) hanyoyin Jehobah koyaushe masu adalci ne, da (5) masu zunubi za su iya koma wa ga Jehobah.

Jehobah Yana Bukatar Bauta Marar Riya

5. Wane irin hidima ne Allah yake bukata a gare mu?

5 Jehobah yana bukatar mu yi masa hidima marar riya a hanya mai tsarki. Amma, Isra’ila ta zama ‘kurangar inabi mai lalacewa.’ Mazaunan Isra’ila sun ‘ƙara bagadansu’ domin amfani da su wajen bautar gumaka. Waɗannan ’yan ridda har sun ƙara ginshiƙai, wataƙila salon dālā da aka tsara domin bauta marar tsarki. Jehobah zai farfasa waɗannan bagadan ya kuma halaka irin waɗannan ginshiƙan.—Yusha’u 10:1, 2.

6. Don mu bi Allah, dole ne mu kawar da wane hali?

6 Riya ba ta da wuri a tsakanin bayin Jehobah. Amma, menene ya faru da Isra’ilawa? ‘Zuciyarsu ta munafunci ce’! Ko da yake a dā sun kasance jama’a da take keɓe ga Jehobah, ya same su da laifin riya. Menene za mu koya daga wannan? Idan mun keɓe kanmu ga Allah, dole ne mu kasance marasa riya. Karin Magana 3:32 ta yi kashedi: “Ubangiji yana ƙin mutanen da ke aikata mugunta, amma yakan rungumi adalai ya amince da su.” Domin mu bi Allah, dole mu nuna ƙauna “daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya.”—1 Timoti 1:5.

Allah Yana Nuna wa Mutanensa Ƙauna ta Aminci

7, 8. (a) A wane yanayi ne za mu more ƙauna ta aminci ta Allah? (b) Menene ya kamata mu yi idan mun yi zunubi mai tsanani?

7 Idan mun bauta wa Jehobah ban da riya kuma a hanya ta adalci, za mu sami ƙaunarsa ta alheri ko kuma ƙauna ta aminci. An gaya wa Isra’ilawa masu taurin kai: “Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe albarkun ƙauna, ku yi kautun saurukanku, gama lokacin neman Ubangiji ya yi, domin ya zo, ya koya muku adalci.”—Yusha’u 10:12.

8 Da Isra’ilawa za su tuba su biɗi Jehobah! Da zai yi farin cikin ‘koya musu adalci.’ Idan mun yi zunubi mai tsanani, bari mu biɗi Jehobah, mu yi addu’a gare shi domin gafara kuma mu nemi taimako na ruhaniya daga wurin dattawa Kiristoci. (Yakubu 5:13-16) Bari kuma mu biɗi ja-gorar ruhu mai tsarki na Allah, domin “wanda ya yi shuka a kwaɗayin son zuciyarsa, ta son zuciya zai girbi ruɓa. Wanda ya yi shuka a Ruhu, ta Ruhu zai girbi rai madawwami.” (Galatiyawa 6:8) Idan mun ‘yi shuka a ruhu,’ za mu ci gaba da morar ƙauna ta aminci ta Allah.

9, 10. Ta yaya Yusha’u 11:1-4 suka yi magana game da Isra’ila?

9 Za mu kasance da tabbaci cewa Jehobah ko da yaushe yana bi da mutanensa cikin ƙauna. Da tabbacin haka a Yusha’u 11:1-4, da suka ce: “A lokacin da Isra’ila ke yaro, na ƙaunace shi, daga cikin Masar na kirawo ɗana. . . . Sai ƙara miƙa wa Ba’al sadaka suke yi, suna ƙona turare ga gumaka. Ko da ya ke ni ne na koya wa Ifraimu [Isra’ilawa] tafiya. Na ɗauke su a hannuna, amma ba su sani ni ne na lura da su ba. Na bishe su da linzamin alheri da ragamar ƙauna, na zama musu kamar wanda ke ɗauke musu karkiya daga muƙamuƙansu. Na sunkuya, na ciyar da su.”

10 A nan an kwatanta Isra’ila da yaro ƙarami. Jehobah cikin ƙauna ya koya wa Isra’ila tafiya, yana ɗaukansu a hannunsa. Ya yi ta bishe su da “ragamar ƙauna.” Lallai wannan kwatanci ne mai sosa rai! Ka yi tunanin kai mahaifi ne kana taimakon ɗanka ƙarami ya yi taƙunsa na farko. Ka miƙa hannunka. Wataƙila za ka yi amfani da ragama da ɗanka zai kama domin kada ya faɗi. To, haka ƙaunar Jehobah take a gare ku. Yana farin ciki ya yi muku ja-gora da “ragamar ƙauna.”

11. Ta yaya Allah ya zama ‘mai ɗaga karkiya’?

11 Da yake sha’ani da Isra’ilawa, Jehobah ya “zama musu kamar wanda ke ɗauke musu karkiya daga muƙumuƙansu, [ya] sunkuya, [ya] ciyar da su.” Allah ya aikata kamar wanda ya ɗaga ko kuma ture karkiyar da nisa domin dabba ya ci abinci cikin walwala. Sai lokacin da mutanen Isra’ila suka karya karkiyarsu na biyayya ga Jehobah ne suka faɗa cikin karkiyar zalunci na abokan gabansu. (Maimaitawar Shari’a 28:45, 48; Irmiya 28:14) Kada mu faɗa cikin hannun babban abokin gābanmu, Shaiɗan, kuma mu sha azabar karkiyarsa ta zalunci. Maimakon haka, bari mu ci gaba da bin Allahnmu mai ƙauna cikin aminci.

Ka Yi Begen Jehobah Kullayaumi

12. Bisa ga Yusha’u 12:6, menene ake bukata domin mu ci gaba da bin Allah?

12 Don mu ci gaba da bin Allah, dole ne mu yi begensa kullayaumi. An gaya wa Isra’ilawa: “Sai ku koma wurin Allahnku, ku yi alheri, ku yi adalci, ku saurari Allahnku kullayaumin.” (Yusha’u 12:6) Mazaunan Isra’ila suna iya nuna tabbaci sun tuba ta komawa ga Jehobah ta wajen nuna ƙauna ta alheri, ta wajen yin adalci, da kuma yin ‘bege ga Jehobah kullayaumi.’ Ko yaya yawan yadda muka yi tafiya da Allah, dole ne mu ƙuduri aniya mu nuna ƙauna ta alheri, mu yi adalci, kuma mu yi begen Allah kullayaumi.—Zabura 27:14.

13, 14. Ta yaya Bulus ya yi amfani da Yusha’u 13:14, wane dalilin yin begen Jehobah ne wannan ya ba mu?

13 Annabcin Yusha’u game da Isra’ilawa ya ba mu dalili na musamman na yin bege ga Allah. Jehobah ya ce: “Zan fanshe su daga ikon lahira. Zan fanshe su daga mutuwa. Ya mutuwa, ina annobanki? Ya kabari, ina halakarka?” (Yusha’u 13:14) Jehobah bai ceci Isra’ilawa daga mutuwa a wancan lokacin ba, amma zai haɗiye mutuwa har abada kuma ya kawar da nasararta.

14 Da yake magana da ’yan’uwansa shafaffu, Bulus ya yi ƙaulin annabcin Yusha’u kuma ya rubuta: “Sa’ad da kuma marar ruɓa ya maye mai ruɓan nan, marar mutuwa kuma ya maye mai mutuwan nan, a sa’an nan ne fa maganan nan da ke rubuce za a cika ta, cewa, ‘An shafe mutuwa da aka ci nasararta.’ ‘Ke mutuwa, ina nasararki? Ke mutuwa, ina ƙarinki?’ Ai, zunubi shi ne ƙarin mutuwa, shari’a kuwa ita ce sanadin ƙarfin zunubi. Godiya tā tabbata ga Allah wanda ke ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.” (1 Korantiyawa 15:54-57) Jehobah ya tashi Yesu daga matattu, wanda hakan ya ba da tabbaci mai ƙarfafawa cewa Allah zai tashe mutane da yake tunawa da su. (Yahaya 5:28, 29) Wannan dalili mai kyau ne na yin bege ga Jehobah! Amma, wani abu, ban da begen tashin matattu na motsa mu mu bi Allah.

Hanyoyin Jehobah Koyaushe Masu Adalci Ne

15, 16. Menene aka annabta game da Samariya, yaya annabcin ya cika?

15 Tabbacinmu cewa ‘hanyoyin Jehobah masu adalci ne’ na taimakonmu mu ci gaba da bin Allah. Mazaunan Samariya ba su yi tafiya bisa hanyoyin Allah masu adalci ba. Saboda haka, dole ne su fuskanci sakamakon zunubinsu da kuma rashin bangaskiya ga Jehobah. An annabta cewa: “Samariya za ta ɗauki hakkin zunubinta, gama ta tayar wa Allahnta. Za a kashe mutanenta da takobi. Za a fyaɗa jariranta a ƙasa, a kuma tsage matanta masu ciki.” (Yusha’u 13:16) Tarihi ya nuna cewa Assuriyawa sukan yi irin wannan ɗanyen aiki.

16 Samariya ce babban birnin masarautar ƙabila goma na Isra’ila. Duk da haka, ana iya amfani da sunan nan Samariya ga dukan yankin wannan masarauta. (1 Sarakuna 21:1) Sarki Shalmanasa na Biyar ya yi wa birnin Samariya kwanton ɓauna a shekara ta 742 K.Z. Sa’ad da Samariya daga ƙarshe ta miƙa wuya a shekara ta 740 K.Z., an kwashi manyan mutanenta zuwa bauta a Mesofotamiya da Midiya. Babu tabbacin ko nasarar cin Samariya ga Shalmanasa na Biyar ne ko magajinsa Sargon na Biyu. (2 Sarakuna 17:1-6, 22, 23; 18:9-12) Bugu da ƙari, tarihi na Sargon ya yi magana game da kwasan Isra’ilawa 27,290 zuwa wurare da suke yanki na saman Yufiretis da Midiya.

17. Maimakon mu rena mizanan Allah, me ya kamata mu yi?

17 Mazaunan Samariya sun sha wahala sosai don ƙin biyayya da hanyoyi masu adalci na Jehobah. Mu Kiristoci da suka keɓe kansu mu ma za mu fuskanci sakamako mai tsanani idan muka zama masu yin zunubi, da kuma rena mizanan Allah na adalci. Kada mu bi irin wannan mugun tafarki! Maimakon haka, bari mu bi gargaɗin manzo Bitrus: “Kada shan wuyar ko ɗaya cikinku ya zama na horon laifin kisankai ne, ko na sata, ko na mugun aiki, ko kuma na shisshigi. Amma in wani ya sha wuya a kan shi Kirista ne, to, kada ya ji kunya, sai dai ya ɗaukaka Allah saboda wannan suna.”—1 Bitrus 4:15, 16.

18. Ta yaya za mu ci gaba da “ɗaukaka Allah”?

18 Muna “ɗaukaka Allah” ta wajen tafiya bisa hanyoyinsa na adalci maimakon yin abubuwa yadda muke so. Kayinu ya yi kisan kai domin ya bi hanyar kansa kuma ya ƙi ya bi gargaɗin Jehobah cewa zunubi yana so ya faɗa masa. (Farawa 4:1-8) Bal’amu ya karɓi kuɗi daga sarkin Mowab don la’antar Isra’ila amma ƙoƙarinsa ya citura. (Littafin Ƙidaya 24:10) Allah ya halaka Balawi Kora da wasu domin yin tawaye ga ikon Musa da Haruna. (Littafin Ƙidaya 16:1-3, 31-33) Ba ma so mu bi “halin Kayinu” na kisa, mu “ɗunguma cikin bauɗewar Bal’amu,” ko mu halaka ta “irin tawayen Kora.” (Yahuza 11) Amma, idan mun yi kuskure, annabcin Yusha’u yana ƙarfafa mu.

Masu Zunubi Suna Iya Komawa ga Jehobah

19, 20. Isra’ilawa da suka tuba sun miƙa waɗanne hadayu?

19 Har waɗanda suka yi tuntuɓe ta wurin yin zunubi mai tsanani za su iya komawa ga Jehobah. A Yusha’u 14:1, 2, an yi wannan roƙo: “Ya mutanen Isra’ila, ku komo wurin Ubangiji Allahnku, gama zunubinku ya sa kun yi tuntuɓe. Ku komo wurin Ubangiji, ku roƙe shi, ku ce, ‘Ka gafarta mana zunubanmu, ka karɓe mu saboda alherinka, mu kuwa za mu yabe ka da bakinmu.’ ”

20 Isra’ilawa da suka tuba sun miƙa wa Allah hadayar ‘bijimin leɓunansu.’ Waɗannan hadayu ne na yabo. Bulus ya yi maganar wannan annabci sa’ad da ya aririci Kiristoci su “yi ta yabon Allah ta wurinsa, sadakar da muke miƙawa ke nan, wato mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa.” (Ibraniyawa 13:15) Gata ce mai girma mu bi Allah kuma mu miƙa irin waɗannan hadayu a yau!

21, 22. Wane maidowa Isra’ilawa da suka tuba za su samu?

21 Isra’ilawa da suka yi watsi da tafarkinsu na tawaye suka koma ga Allah sun miƙa masa ‘bijimin leɓunansu.’ Saboda haka, sun sami komawa ta ruhaniya, kamar yadda Allah ya yi alkawari. Yusha’u 14:4-7 suka ce: “Zan [Jehobah] warkar musu da riddarsu. Zan kuma ƙaunace su sosai, gama fushina zai huce. Zan zama kamar raɓa ga Isra’ila, Isra’ila za ta yi fure kamar lili, saiwarta za ta shiga kamar itacen al’ul. Tohonta zai buɗo, kyanta zai zama kamar itacen zaitun, ƙanshinta kuwa kamar itacen al’ul na Lebanon. Waɗanda za su komo, za su zauna a inuwarta, za su yi noman hatsi da yawa, za su yi fure kamar kurangar inabi. Ƙanshinsu zai zama kamar ruwan inabi na Lebanon.”

22 Isra’ilawa da suka tuba za su sami warkewa ta ruhaniya kuma za su sake more ƙaunar Allah. Jehobah zai zama kamar raɓa mai wartsakarwa a gare su saboda zai albarkace su a yalwace. Mutanensa da aka maido za su sami daraja “kamar itacen zaitun,” kuma za su bi hanyoyin Allah. Tun da mun ƙuduri aniyar bin Jehobah Allahnmu, menene ake bukata a gare mu?

Ka Ci Gaba da Bin Hanyoyin Jehobah na Adalci

23, 24. Littafin Yusha’u ya kammala da wane annabci na ban ƙarfafa, ta yaya wannan ya shafe mu?

23 Don mu ci gaba da bin Allah, dole ne mu nuna “hikiman nan ta Sama” kuma mu aikata cikin jituwa da hanyoyinsa na adalci. (Yakubu 3:17, 18) Ayar ƙarshe ta annabcin Yusha’u ta ce: “Duk wanda ke da hikima, bari ya fahimci abubuwan nan. Duk wanda ke da ganewa, bari ya san abubuwan nan, gama hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne, masu adalci kuwa za su yi tafiya a cikinsu, amma masu zunubi za su yi tuntuɓe a kansu.”—Yusha’u 14:9.

24 Maimakon hikima ta duniya da mizanan wannan duniya su yi mana ja-gora, bari mu ƙuduri aniyar bin hanyoyin Allah masu adalci. (Maimaitawar Shari’a 32:4) Yusha’u ya yi hakan na shekaru 59 ko kuma fiye da haka. Ya gabatar da saƙonnin Allah da aminci, ya sani cewa waɗanda suke da hikima za su fahimci waɗannan kalmomi. Mu kuma fa? Muddin Jehobah ya ƙyale mu mu ba da shaida, za mu ci gaba da neman waɗanda za su amince da alherinsa cikin hikima. Kuma muna masu farin cikin yin wannan, cikin haɗin kai da “amintaccen bawan nan mai hikima.”—Matiyu 24:45-47.

25. Menene bincika annabcin Yusha’u ya kamata ya taimake mu yi?

25 Bincika annabcin Yusha’u ya kamata ya taimake mu mu ci gaba da bin Allah muna hangar rai madawwami a sabuwar duniya ta Allah. (2 Bitrus 3:13; Yahuza 20, 21) Bege ne kuwa mai kyau! Wannan begen zai zama da gaske idan muka nuna ta kalmomi da kuma ayyuka cewa mun tabbata da abin da muke cewa: “Hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne.”

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Idan mun yi wa Allah bauta mai tsarki, yaya zai bi da mu?

• Me ya sa ya kamata mu yi begen Jehobah kullayaumi?

• Me ya sa ka tabbata cewa hanyoyin Jehobah masu gaskiya ne?

• Ta yaya za mu ci gaba da bin hanyoyin Jehobah na adalci?

[Hoto a shafi na 14]

Ka amince da taimakon dattawa Kiristoci

[Hoto a shafi na 15]

Annabcin Yusha’u yana ba mu dalilin yin bege ga alkawarin Jehobah na tashin matattu

[Hotuna a shafi na 17]

Ka ci gaba da bin Allah da hangar rai madawwami

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba