Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 12/1 pp. 8-12
  • Ka Bi Allah, Ka Sami Alheri

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bi Allah, Ka Sami Alheri
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Taƙaitaccen Bayani
  • Yadda Tuba ta Gaskiya Take Bayyana
  • Hadaya Zalla Ba Ta Faranta wa Jehobah Rai
  • Jehobah Yana Baƙin Ciki Sa’ad da Masu Bauta Masa Suka Bar Shi
  • Yadda Za Mu Sami Alheri
  • Darussa Daga Littafin Hosea
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Annabcin Yusha’u Yana Taimakonmu Mu Bi Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • “Hanyoyin Ubangiji Masu Gaskiya Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Hosiya
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 12/1 pp. 8-12

Ka Bi Allah, Ka Sami Alheri

“Sun shuka iska don haka za su girbe guguwa.”—Yusha’u 8:7.

1. Ta yaya za mu bi Jehobah?

TAFIYA cikin yanki mai haɗari za ta kasance mai lafiya idan gwanin ja-gora ya shige gaba. Zai kasance hikima ce mu bi wannan mai ja-gora maimakon mu yi gaban kanmu. A wasu fasaloli wannan ya kwatanta yanayin da muke ciki. A alamance, Jehobah yana yi mana ja-gora cikin hamada ta wannan muguwar duniya. Za mu kasance masu hikima idan muka bi shi maimakon mu yi wa kanmu ja-gora. Ta yaya za mu bi Allah? Ta wurin bin umurni da ya tanada cikin Kalmarsa.

2. Menene za a tattauna a wannan talifin?

2 Talifin da ya gabata ya tattauna wasan kwaikwayo na alama da ke cikin Yusha’u sura ta 1 zuwa ta 5. Kamar yadda muka fahimta wannan wasan kwaikwayon ya ƙunshi darussa da za su taimake mu mu bi Allah. Bari yanzu mu tattauna muhimman abubuwa a sura ta 6 zuwa ta 9. Zai taimaka idan muka fara da taƙaita abin da waɗannan surori huɗu suka ƙunsa.

Taƙaitaccen Bayani

3. Ka ɗan ba da labarin abubuwan da ke cikin Yusha’u sura ta 6 zuwa ta 9.

3 Jehobah ainihi ya aiki Yusha’u ya yi annabci bisa masarautar ƙabilu goma ta arewa ta Isra’ila. An san wannan al’umma kuma da Ifraimu sunan ƙabila da ta yi fice amma ta juya wa Allah baya. Yusha’u sura ta 6 zuwa ta 9 sun nuna cewa mutanen suna nuna rashin aminci ta wurin ƙeta alkawarin Jehobah da kuma aikata mugunta. (Yusha’u 6:7) Sun koma ga yin abota da mutanen duniya maimakon su koma ga Jehobah. Domin sun ci gaba da shuka abin da ke mugun, za su girbe abin da ke mugu. A wata sassa, hukunci yana bisa kansu. Amma annabcin Yusha’u na ɗauke da saƙo mai daɗaɗa rai. An tabbatar wa mutanen cewa za su iya komawa ga Jehobah kuma zai yi musu jinƙai idan suka tuba da zuciya ɗaya.

4. Waɗanne darussa masu amfani ne za mu bincika daga annabcin Yusha’u?

4 Daga waɗannan surori huɗu na annabcin Yusha’u, za mu sami ƙarin bayani da zai taimake mu mu bi Allah. Bari mu bincika darussa huɗu masu muhimmanci: (1) Ayyuka ne suke nuna tuba ta gaskiya ba kalmomi ba kawai; (2) hadayu zallarsu ba sa faranta wa Allah rai; (3) Jehobah yana yin fushi idan bayinsa suka juya masa baya; (4) domin mu girbe abin da ke nagari, dole ne mu shuka nagarin abu.

Yadda Tuba ta Gaskiya Take Bayyana

5. Ka faɗi abu mafi muhimmanci da aka faɗa a cikin Yusha’u 6:1-3.

5 Annabcin Yusha’u ya koya mana abubuwa da yawa game da tuba da jinƙai. Yusha’u 6:1-3 sun ce: “Mutane sun ce, ‘Zo, mu koma wurin Ubangiji, gama shi ne ya yayyaga, shi ne kuma zai warkar. Shi ne ya yi mana rauni, shi ne kuma zai ɗaure raunin da maɗauri. Bayan kwana biyu zai rayar da mu. A rana ta uku kuwa zai tashe mu mu yi zamanmu a gabansa. Mu nace domin mu san Ubangiji zuwansa tabbatacce ne kamar wayewar gari. Zai zo wurinmu kamar ruwan sama, kamar ruwan bazara da ke shayar da ƙasa.”

6-8. Mecece matsalar tuban Isra’ila?

6 Waye ne ya yi maganar da ke cikin waɗannan ayoyi? Wasu suna cewa Isra’ilawa marasa aminci ne suka yi wannan maganar, sun daɗa cewa mutanen marasa biyayya suna nuna sun tuba amma da gaske suna wasa ne da jinƙan Allah. Wasu kuma suna cewa annabi Yusha’u ne yake magana, yana roƙon mutanen su koma ga Jehobah. Ko da wanene ya yi wannan magana, muhimmiyar tambaya ita ce, Shin mutanen masarautar ƙabilu goma na Isra’ila sun koma ne ga Jehobah, sun tuba da gaske? A’a. Jehobah ya ce ta bakin Yusha’u: “Me zan yi da ke ya Ifraimu? Me zan yi da ke, ya Yahuza? Ƙaunarku tana kama da ƙāsashi, kamar kuma raɓar da ke watsewa da wuri.” (Yusha’u 6:4) Wannan shaida ce ga ƙanƙancin yanayin ruhaniya na mutanen Allah! Ƙauna ta alheri, ko kuma ƙauna ta aminci, ta rage kaɗan kamar raɓa ta safiya mai watsewa da wuri idan rana ta fito. Ko da yake mutanen sun nuna cewa sun tuba, Jehobah bai ga dalilin yi musu jinƙai ba. Mecece matsalar?

7 Tuba ta Isra’ila ba ta gaskiya ba ce daga zuciyarta. Yusha’u 7:14 ta faɗi rashin farin cikin Jehobah game da mutanensa: “Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba, sa’ad da suke kuka a gadajensu.” Aya ta 16 ta daɗa cewa: “Sun juya mini baya, suna bin gunkin nan Ba’al.” Mutanen ba su shirya su koma ga bautar Jehobah mai martaba ba ta wurin yin gyara da ake bukata domin su gyara dangantakarsu da shi. Hakika ba sa son su bi Allah.

8 Da wata matsala kuma game da tuba ta Isra’ila. Mutanen sun ci gaba da yin zunubi, wato, zunubai iri-iri da suka haɗa da zamba, kisa, sata, bautar gumaka da kuma ƙulla abota da wasu al’ummai. A Yusha’u 7:4 an kwatanta mutanen da “tanda,” hakika domin yadda muradinsu na mugunta yake da zafi. A irin wannan mummunan yanayi na ruhaniya, mutanen sun cancanci a yi musu jinƙai kuwa? Ko kaɗan! Yusha’u ya gaya wa ’yan tawayen cewa Jehobah zai “tuna da muguntarsu” zai “hukunta su saboda zunubansu.” (Yusha’u 9:9) Babu jinƙai!

9. Menene Kalmomin Yusha’u suka koya mana game da tuba da kuma jinƙai?

9 Yayin da muke karanta kalmomin Yusha’u, menene muka koya game da tuba da kuma jinƙai? Misali na gargaɗi na Isra’ilawa marasa aminci ya koya mana cewa domin mu amfana daga jinƙai na Jehobah, dole ne mu tuba daga zukatanmu. Ta yaya ake nuna irin wannan tuba? Ba a yi wa Jehobah wayo ta wurin kalmomi da kuma hawaye. Ana ganin tuba ta gaskiya ta ayyuka. Domin a yi masa jinƙai, mai zunubi dole ne ya kawar da tafarkinsa na zunubi kuma ya daidaita rayuwarsa da mizanai masu girma na bauta mai ɗaukaka ta Jehobah.

Hadaya Zalla Ba Ta Faranta wa Jehobah Rai

10, 11. Yadda take game da Isra’ila, me ya sa hadayu zalla ba ta faranta wa Jehobah rai?

10 Yanzu bari mu tattauna darasi na biyu da zai taimake mu mu bi Jehobah. Wato: Hadaya zalla ba ta faranta wa Allah rai. Yusha’u 6:6 ta ce: “Ƙauna [Jehobah ya]ke so, ba sadaka ba, sanin Allah kuma fiye da hadayu na ƙonawa.” Ka lura cewa Jehobah yana farin ciki da ƙauna ta alheri ko kuma ƙauna ta aminci, wato hali na zuciya da kuma saninsa. Wataƙila kana mamaki: ‘Me ya sa wannan ayar ta ce Jehobah ba ya son “sadaka” da kuma “hadayu na ƙonawa”? Waɗannan ba bukatu ba ne a cikin Dokar Musa?’

11 An bukaci sadaka da hadayu a cikin Doka, amma mutanen zamanin Yusha’u suna da wata matsala mai tsanani. A bayyane yake cewa akwai wasu Isra’ilawa da suke yin irin waɗannan hadayun domin su nuna su masu ibada ne. Sa’an nan kuma sun ci gaba da yin zunubi. Ta wajen zunubansu suna nuna cewa ba sa ƙauna ta aminci. Kuma sun nuna cewa sun ƙi sanin Allah, domin ba sa rayuwa bisa saninsa. Idan mutanen ba su da zukatan kirki, kuma ba sa rayuwa da ta dace, menene amfanin hadayunsu? Hadayunsu ma abin ɓacin rai ne ga Jehobah Allah.

12. Yusha’u 6:6 na ɗauke da wane gargaɗi ga mutanen da suke zama a yau?

12 Kalmomin Yusha’u suna ɗauke da darasi na gargaɗi ga masu zuwa coci a yau. Suna ba da hadayu ga Allah ta wurin ayyuka na addini. Duk da haka bautarsu ba ta shafar rayuwarsu ta yau da kullum. Irin waɗannan mutane suna faranta wa Allah rai kuwa idan zukatansu ba sa motsa su su biɗi cikakken sanin Allah kuma su yi amfani da wannan sani wajen guje wa ayyukan zunubi? Kada kowa ya yi tunanin cewa ayyukan addini kaɗai za su faranta wa Allah rai. Jehobah ba ya farin ciki da mutane da suke ƙoƙari su sami tagomashinsa ta ayyuka na addini maimakon rayuwa bisa Kalmarsa.—2 Timoti 3:5.

13. Waɗanne irin hadayu ne muke miƙawa, amma me ya kamata mu tuna game da amfaninsu?

13 Mu Kiristoci na gaskiya mun sani cewa hadayu zalla ba sa faranta wa Allah rai. Hakika, ba ma ba da hadayu na dabbobi ga Jehobah. Duk da haka muna “yabon Allah ta wurinsa, sadakar da muke miƙawa ke nan, wato mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa.” (Ibraniyawa 13:15) Yana da muhimmanci kada mu zama kamar Isra’ilawa masu zunubi na zamanin Yusha’u, muna tunanin cewa za mu iya biyan laifuffukanmu ta wajen ba da hadayu na ruhaniya ga Allah. Ka yi la’akari da misalin wata matashiya da take yin fasikanci a ɓoye. Daga baya ta ce: “Na ƙara ayyukata a hidimar fage, ina tunanin cewa wannan zai biya laifin da na yi.” Wannan ya yi kama da abin da Isra’ilawa ’yan tawaye suka yi ƙoƙarin yi. Amma, Jehobah zai amince da hadayarmu ta yabo ce kawai idan muka miƙa ta da zuciyar kirki da kuma halaye masu kyau.

Jehobah Yana Baƙin Ciki Sa’ad da Masu Bauta Masa Suka Bar Shi

14. Menene Annabcin Yusha’u ya bayyana game da yadda Allah yake ji?

14 Darasi na uku da muka koya daga Yusha’u sura ta 6 zuwa ta 9 shi ne yadda Jehobah yake ji sa’ad da masu bauta masa suka juya masa baya. Allah ne da yakan yi fushi kuma yakan yi farin ciki. Yana farin ciki matuƙa da kuma juyayi game da waɗanda suka tuba daga zunubansu. Amma sa’ad da mutanensa suka ƙi tuba, yana ɗaukan mataki mai tsanani. Domin Allah yana damuwa da lafiyarmu, yana farin ciki idan muka bi shi cikin aminci. Zabura 149:4 ta ce: “Ubangiji yana jin daɗin jama’arsa.” Amma yaya Allah yake ji sa’ad da bayinsa suka zama marasa aminci?

15. Bisa ga Yusha’u 6:7, ta yaya wasu Isra’ilawa suke aikatawa?

15 Da yake magana game da Isra’ilawa marasa aminci, Jehobah ya ce: “Sun ta da alkawarina kamar Adamu, sun ci amanata.” (Yusha’u 6:7) Kalmar Ibrananci da aka fassara ‘cin amana’ tana kuma nufin “yaudara, rashin aminci.” A Malakai 2:10-16, an yi amfani da wannan kalmar Ibrananci don a kwatanta ayyukan rashin aminci na Isra’ilawa da suke rashin aminci ga matansu. Game da yin amfani da wannan furci a Yusha’u 6:7, wani bincike da aka yi ya nuna cewa “tana kwatanta aure ne na alama da kuma halaye na dangantaka . . . A irin wannan yanayin ne aka ci amanar ƙauna.”

16, 17. (a) Ta yaya Isra’ila ta aikata game da alkawarinta da Allah? (b) Me ya kamata mu tuna game da ayyukanmu?

16 Jehobah ya ɗauki Isra’ila matarsa ce ta alama domin alkawarinsa da al’ummar. Saboda haka, sa’ad da mutanensa suka ƙeta wannan alkawari, kamar dai sun yi zina ne. Allah kamar maigida ne mai aminci, amma mutanensa sun fice daga wurinsa!

17 Mu kuma fa? Allah yana damuwa da ko za mu bi shi ko za mu ƙi yin haka. Yana da muhimmanci mu tuna cewa “Allah ƙauna ne” kuma abin da muke yi yakan shafe shi. (1 Yahaya 4:16) Idan muka bi mugun tafarki, muna iya sa Jehobah baƙin ciki. Tuna wannan zai kasance kāriya ce mai kyau a lokacin da aka jarabce mu.

Yadda Za Mu Sami Alheri

18, 19. Wace ƙa’ida take cikin Yusha’u 8:7, kuma yaya hakan ya kasance gaskiya ga Isra’ilawa?

18 Bari mu bincika darasi na huɗu daga annabcin Yusha’u, wato yadda za mu sami alheri. Game da Isra’ilawa da kuma wautarsu da kuma wautar tafarkinsu na rashin aminci, Yusha’u ya rubuta: “Sun shuka iska don haka za su girbe guguwa.” (Yusha’u 8:7) A nan mun sami mizani da ya kamata mu riƙa tunawa: Akwai dangantaka tsakanin abin da muke yi yanzu da abin da zai faru mana nan gaba. Ta yaya wannan mizanin ya tabbata ga Isra’ilawa marasa aminci?

19 Ta yin zunubi, waɗannan Isra’ilawa suna shuka abin da ke mugu. Za su ci gaba da yin haka ne ba tare da sun sami sakamakon aikinsu ba? Hakika, ba za su tsira wa hukunci mai tsanani ba. Yusha’u 8:13 ta ce: “Ubangiji zai tuna da muguntarsu, zai hukunta su saboda zunubansu.” Yusha’u 9:17 ta ce: “Allahna zai ƙi su domin ba su yi masa biyayya ba. Za su zama masu yawo cikin al’ummai.” Jehobah zai hukunta Isra’ilawa domin zunubansu. Domin sun shuka mugunta, za su girbe mugunta. Hukuncin Allah ya zo a shekara ta 740 K.Z., sa’ad da Assuriyawa suka ci masarautar ƙabila goma ta Isra’ila kuma suka kwashi mazauna cikinta zuwa bauta.

20. Menene abin da ya faru da waɗannan Isra’ilawa ya koya mana?

20 Abin da ya faru da waɗannan Isra’ilawa ya koya mana wata gaskiya mai muhimmanci: Za mu girbe abin da muka shuka. Kalmar Allah ta yi mana gargaɗi: “Kada fa a yaudare ku, ai, ba a iya zambatar Allah. Duk abin da mutum ya shuka, shi zai girba.” (Galatiyawa 6:7) Idan muka shuka abin da ke mugu, za mu girbe abin da ke mugu. Alal misali, waɗanda suke bin tafarkin rayuwa ta lalata za su girbe sakamako mai tsanani. Mugu da ya ƙi tuba zai samu sakamako ta baƙin ciki.

21. Ta yaya za mu girbe abin da ke mai kyau?

21 To, ta yaya za mu girbe abin da ke mai kyau? Za a amsa wannan tambayar da misali mai sauƙi. Idan manomi yana so ya girbe alkama, zai shuka sha’ir ne? A’a! Dole ne ya shuka abin da yake so ya girba. Hakazalika, idan muna so mu girbe abin da yake mai kyau, dole ne mu shuka abin da ke mai kyau. Kana so ka ci gaba da girbe abin da ke mai kyau, wato, rayuwa ta farin ciki a yanzu da kuma begen rai madawwami a sabuwar duniya ta Allah? Idan haka ne, dole ne ka ci gaba da shuka abin da ke mai kyau ta wajen bin Allah da kuma rayuwa cikin jituwa da mizanansa na adalci.

22. Waɗanne darussa muka koya daga Yusha’u sura ta 6 zuwa ta 9?

22 Daga sura ta 6 zuwa ta 9 na Yusha’u mun koyi darussa huɗu da za su taimake mu mu bi Allah: (1) Tuba ta gaskiya tana bayyana ta wurin ayyuka; (2) hadayu zalla ba sa faranta wa Allah rai; (3) Jehobah yana baƙin ciki idan bayinsa suka juya masa baya; da kuma (4) domin mu girbe abin da ke mai kyau, dole ne mu shuka abin da yake mai kyau. Ta yaya surori biyar na ƙarshe na wannan littafi cikin Littafi Mai Tsarki zai taimake mu mu bi Allah?

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Ta yaya ake nuna tuba ta gaskiya?

• Me ya sa hadayu zalla ba sa faranta wa Ubanmu na samaniya rai?

• Yaya Allah yake ji sa’ad da masu bauta masa suka bar shi?

• Menene dole ne mu shuka idan za mu girbe abin da ke mai kyau?

[Hoto a shafi na 9]

Kamar gajimare na safe, ƙauna ta aminci ta Isra’ila ta ɓace

[Hoto a shafi na 9]

Mugun muradi na Isra’ila ya yi zafi kamar tanda

[Hoto a shafi na 10]

Me ya sa Jehobah ya ƙi hadayun mutanensa?

[Hoto a shafi na 11]

Domin mu girbe abin da ke mai kyau, dole ne mu shuka abin da ke mai kyau

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba