Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 11/13 p. 1
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Hosiya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Hosiya
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Annabcin Yusha’u Yana Taimakonmu Mu Bi Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Darussa Daga Littafin Hosea
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Ka Bi Allah, Ka Sami Alheri
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • “Hanyoyin Ubangiji Masu Gaskiya Ne”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 11/13 p. 1

Ku Bi Gurbin Annabawa—Hosiya

1. Wace tambaya ce mai yiwuwa ka taɓa yi wa kanka?

1 ‘Wane irin sadaukarwa ne zan iya yi saboda Jehobah?’ Wataƙila ka taɓa yi wa kanka wannan tambayar bayan da ka yi bimbini a kan alheri da kuma jin ƙan Jehobah. (Zab. 103:2-4; 116:12) Hosiya ya yi abin da Jehobah ya umurce shi ya yi da son rai, ko da yake hakan ya bukaci ya yi sadaukarwa. Ta yaya za mu iya yin koyi da Hosiya?

2. Ta yaya za mu bi misalin Hosiya wajen dāgewa a yin wa’azi?

2 Ku Ci Gaba da Yin Wa’azi Har Ma a Lokacin Masifa: Hosiya ya idar da saƙonsa ne musamman ga ƙabilu goma na Isra’ila, inda kusan kowa yake bauta wa allolin ƙarya. Sarki Yerobowam na Biyu ya yi zunubi sosai a gaban Jehobah kuma ya ci gaba da ɗaukaka bautar ɗan maraki da Yerobowam na Ɗaya ya kafa. (2 Sar. 14:23, 24) Sarakunan da suka yi sarauta bayansu sun ci gaba da ƙarfafa bautar gumaka a yankunan da ƙabilu goman nan suke, har zuwa lokacin da aka halaka su a shekara ta 740 kafin zamaninmu. Amma duk da bautar gumaka da ta zama ruwan dare, Hosiya ya ci gaba da yin annabci har tsawon aƙalla shekaru 59. Shin mu ma mun ƙudura cewa za mu ci gaba da yin wa’azi ko da mutane sun ƙi da saƙonmu ko kuma sun yi hamayya da mu?—2 Tim. 4:2.

3. Ta yaya rayuwar Hosiya ta nuna cewa Jehobah mai jin ƙai ne?

3 Ku Riƙa Tuna da Jin Ƙan Jehobah: Jehobah ya umurci Hosiya ya auri mace mai “fasikanci.” (Hos. 1:2) Matarsa Gomer ta haifa masa ɗa, amma daga baya ta je ta haifi ’ya’ya biyu ma wani dabam. Duk da haka, Hosiya ya gafarta wa matarsa kuma hakan ya kwatanta irin jin ƙan da Jehobah yake nuna wa Isra’ilawa masu taurin kai bayan sun tuba. (Hos. 3:1; Rom. 9:22-26) Shin za mu iya sadaukar da wasu abubuwa da muke so a rayuwa don mu sanar da jin ƙan Jehobah ga dukan mutane?—1 Kor. 9:19-23.

4. Waɗanne sadaukarwa ne za mu iya yi saboda Jehobah?

4 Wasu bayin Jehobah sun ƙi da aikin da ake biyan albashi mai tsoka don su ƙara ƙwazo a yin wa’azi. Wasu sun ƙi yin aure ko kuma haifan ’ya’ya don su yi hidimar Jehobah a hanyoyi dabam-dabam. Sa’ad da muke tunani a kan rayuwar Hosiya, muna iya cewa, ‘Ba zan iya yin abin da ya yi ba.’ Amma yayin da muka ci gaba da nuna godiya ga Jehobah don alherinsa kuma muka dogara ga ruhunsa mai tsarki, Jehobah zai yi amfani da mu a hanyar da ba mu tsammani ba, kamar yadda ya yi da Hosiya.—Mat. 19:26; Filib. 2:13.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba