Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 5/1 p. 3
  • Talauci Yanayin Da Ake Ciki A Yau

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Talauci Yanayin Da Ake Ciki A Yau
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Makamantan Littattafai
  • Ƙoƙarce-ƙoƙarcen Kawo Ƙarshen Talauci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Talauci—Samun Maganinsa na Dindindin
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Albishiri Ga Talakawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 5/1 p. 3

Talauci Yanayin Da Ake Ciki A Yau

SAU da yawa Vicentea yana jan amalanke cike da kaya a titunan Sāu Paulo, a Brazil. Yana kwasan kwalaye, ƙarafa marar amfani, da robobi. Idan dare ya yi sai ya shimfiɗa kwalayen a ƙarƙashin amalankensa ya kwanta ya yi barci. Ƙarar motoci a titin da yake barci daddare na faɗa masa a bayan kunne. A dā yana da aiki, gida, da kuma iyali, amma yanzu ba shi da kome. Yanzu yana aiki mai wuya a kan titi don ya samu na ci.

Abin baƙin ciki, mutane miliyoyi a dukan duniya suna zaune ne a cikin talauci kamar Vicente. A ƙasashe masu tasowa, mutane da yawa suna kwana a kan titi ko kuma bukkoki. Masu bara, guragu, makafi da mata da jariransu ke shan mama, ne ake gani a wurin. Sai ka ga yara suna gudu don su sayar da alewa idan motoci suka tsaya domin su samu ’yan kwabbai.

Yana da wuya a bayyana abin da ya sa ake irin wannan talauci. Jarida na Britaniya da ake kira The Economist ta ce: “Tsaran ’yan adam ba su taɓa yin arziki, ko kuma su sami ilimin magani, gwani na fasaha, da fahimi da ake bukata don a kawar da talauci ba.” Babu shakka, mutane da yawa sun amfana daga waɗannan iyawa da mutane a yau suke da shi. Titunan babban birane a ƙasashe masu tasowa da yawa suna cike da sababbin motoci masu ban sha’awa. Kantunan sayar da kaya suna cike da kayan zamani, kuma mutane da yawa suna sayensu. Kantuna biyu na sayar da kaya a Brazil suna tallar wasu kayayyaki na musamman. Sun yi ciniki dukan dare na ranar 23 zuwa 24 na Disamba, 2004. A ɗayan kantin an yi hayar masu rawa da za su sa masu ciniki farin ciki. Wannan ya jawo hankalin kusan mutane 500,000!

Duk da haka, mutane da yawa ba sa amfana daga arziki da wasu suke morewa. Bambancin da ke tsakanin masu arziki da matalauta ya sa mutane da yawa suka kammala cewa ana bukatar a yi ƙoƙari a kawar da talauci cikin gaggawa. Jaridar Veja ta Brazil ta ce: “A wannan shekarar ta 2005, batu mafi muhimmanci da shugabanan duniya za su tattauna shi ne yadda za a kawar da talauci.” Jaridar Veja ta kuma faɗa cewa za a yi sabon tsari kamar wanda Amirka ta kafa domin a taimaki Turai ta farfaɗo daga tattalin arziki bayan yaƙin duniya ta biyu. Amma an yi wannan sabon tsari don a taimaki ƙasashe da suka fi talauci musamman a Afirka. Amma ko da kamar za a sami cin gaba a irin waɗannan tsare-tsare, jaridar ta daɗa cewa: “Da dalilai da yawa na yin shakkar samun sakamako mai kyau. Yawancin ƙasashe suna jinkirin ba da kuɗi ga irin wannan tsarin, domin sun ga cewa ba a taimakon mutanen da suke bukatar taimako da kuɗin.” Abin baƙin ciki, domin rashawa, da kuma tsarin aikin gwamnati, mutane da suke bukatar taimako ba sa samun kuɗaɗe masu yawa da gwamnatoci, ƙungiyoyi ta ƙasashe, da kuma mutane suke bayarwa.

Yesu ya san cewa matsalar talauci za ta ci gaba. Ya ce: “Kuna da fakirai kullum tare da ku.” (Matta 26:11) Wannan yana nufin cewa za a ci gaba da talauci a duniya? Ba za a iya yin wani abu ba ne don a kyautata yanayin? Menene Kiristoci za su yi don su taimaki matalauta?

[Hasiya]

a An canja sunan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba