Ka Karɓa da Godiya Ka Bayar da Zuciya Ɗaya
JEHOBAH Ubanmu na samaniya mai ƙauna, yana damuwa da mu. Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa yana kula da dukan bayinsa sosai. (1 Bit. 5:7) Hanya ɗaya da Jehobah yake nuna cewa yana kula da mu ita ce ta wajen taimakonmu a hanyoyi dabam dabam don mu bauta masa da aminci. (Isha. 48:17) Musamman sa’ad da muke fuskantar matsaloli da suke sa mu baƙin ciki, Jehobah yana son mu amfana daga taimako da yake tanadinsa. Dokar Musa ta nuna cewa hakan gaskiya ne.
A ƙarƙashin Dokar, Jehobah cikin ƙauna ya tabbata cewa za a taimaki “masu-mayata,” kamar maraya, gwauruwa, da baƙo. (Lev. 19:9, 10; K. Sha 14:29) Ya san cewa wasu cikin bayinsa za su bukaci taimako daga ’yan’uwansu masu bi. (Yaƙ. 1:27) Shi ya sa, bai kamata wani daga cikin bayinsa ya yi jinkirin karɓan taimako daga waɗanda Jehobah ya motsa su ba da irin wannan taimakon ba. Amma, sa’ad da muka samu taimako ya kamata mu yi hakan da halin kirki.
Duk da haka, Kalmar Allah ta nanata cewa mutanen Allah suna da zarafin bayarwa. Ka tuna da labarin “gwauruwa kuma matalauciya” wadda Yesu ya lura da ita a haikali a Urushalima. (Luk 21:1-4) Mai yiwuwa ta amfana daga tanadin da Jehobah ya yi cikin ƙauna don gwauraye kamar yadda aka ambata a Dokar. Ko da yake ita matalauciya ce an tuna da wannan gwauruwa, ba a matsayin wadda ta karɓa ba amma a matsayin wadda ta bayar. Babu shakka, halinta na bayarwa ya sa ta farin ciki, domin kamar yadda Yesu ya ce: “Bayarwa ta fi karɓa albarka.” (A. M. 20:35) Domin wannan, yaya za ka riƙa ‘bayarwa’ kuma ka yi farin ciki don hakan?—Luk 6:38.
“Me Zan Bayar ga Ubangiji?”
Mai zabura ya yi tunani: “Me zan bayar ga Ubangiji sabili da dukan alherinsa a gareni?” (Zab. 116:12) Wane amfani ne ya samu? Jehobah ya kiyaye shi a lokacin “wahala da baƙinciki.” Bugu da ƙari, Jehobah ya “ceci ran[sa] daga mutuwa.” Yanzu yana son ya “bayar” ga Jehobah ta wata hanya. Menene mai zabura zai iya yi? Ya ce: “In cika alkawarina ga Ubangiji.” (Zab. 116:3, 4, 8, 10-14) Ya tsai da shawarar ya cika dukan alkawuran da ya yi ga Jehobah kuma ya cika farillansa a gare shi.
Kai ma za ka iya yin hakan. Ta yaya? Ta wajen bin tafarkin rayuwa da ya yi daidai da dokokin Allah da ƙa’idodinsa a dukan lokaci. Saboda haka, ka tabbata cewa bautarka ga Jehobah ita ce abu mafi muhimmanci a rayuwarka kuma kana barin ruhun Allah ya yi maka ja-gora a dukan abubuwa da kake yi. (M. Wa. 12:13; Gal. 5:16-18) Hakika, ba za ka taɓa gama biyan Jehobah don dukan abubuwa da ya yi maka ba. Har ila yana ‘faranta zuciyar Jehobah’ ya ga cewa kana ba da kanka da dukan zuciyarka a hidimarsa. (Mis. 27:11) Gata ne mai ban al’ajabi ka faranta wa Jehobah rai a wannan hanyar!
Ka Daɗa ga Zaman Lafiya Ikilisiya
Babu shakka, za ka yarda cewa ka amfana daga ikilisiyar Kirista a hanyoyi da yawa. Ta wurin ikilisiya, Jehobah ya yi tanadin abinci na ruhaniya a yawalce. Ka koyi gaskiya da ta ’yantar da kai daga kuskure na addini da kuma duhu na ruhaniya. (Yoh. 8:32) A taron ikilisiya, manyan taro, da taron gunduma da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yake shiryawa, kana samun sani da zai sa ka samu rai madawwami a cikin aljanna a duniya da babu azaba da wahala. (Mat. 24:45-47) Ba za ka iya soma ƙirga dukan amfanin da ka samu da kuma har ila za ka samu ta wurin ikilisiyar Allah ba. Menene za ka iya bayar ga ikilisiyar?
Manzo Bulus ya rubuta: “Dukan jiki, haɗaɗe kuwa ta wurin taimakon kowace gaɓa, bisa ga aikin kowane yanki gwargwadon ma’auni nasa, yana sa ƙaruwar jiki zuwa ginin kansa cikin ƙauna.” (Afis. 4:15, 16) Ko da yake wannan nassi ainihi ga rukunin shafaffu Kiristoci ne, ƙa’idar da ke ciki ta shafi dukan Kiristoci a yau. Hakika, kowane mutum da ke cikin ikilisiya zai iya daɗa ga zaman lafiya da ƙaruwar ikilisiyar. A waɗanne hanyoyi?
Muna iya yin hakan ta wajen ƙarfafawa da kuma wartsake mutane a hidimarmu ga Allah a dukan lokaci. (Rom. 14:19) Muna iya daɗa ga “ƙaruwar jiki” ta wajen kasancewa da ɗiyan ruhun Allah a dukan sha’aninmu da ’yan’uwa masu bi. (Gal. 5:22, 23) Bugu da ƙari, muna iya neman zarafin “aika nagarta zuwa ga dukan mutane, tun ba waɗanda su ke cikin iyalin imani.” (Gal. 6:10; Ibran. 13:16) Dukan waɗanda ke cikin ikilisiya, ’yan’uwa maza da mata, yara da manya, suna iya sa hannu wajen ƙarfafa mutane ‘cikin ƙauna.’
Ƙari ga haka, muna iya yin amfani da iyawarmu, kuzarinmu, da dukiyoyinmu don mu sa hannu a aikin ceton rai da ikilisiya ke yi. Yesu Kristi ya ce: “Kyauta kuka karɓa.” Menene ya kamata mu yi? “Ku bayas kyauta” in ji shi. (Mat. 10:8) Saboda haka, ka yi iyakar ƙoƙarinka a aiki mai muhimmanci na wa’azin Mulki da almajirantarwa. (Mat. 24:14; 28:19, 20) Kana da wasu kasawa ne? Ka tuna da gwauruwa matalauciya da Yesu ya ba da misalinta. Abin da ta bayar kaɗan ne sosai. Duk da haka, Yesu ya ce ta ba da fiye da dukan sauran mutanen. Ta ba da dukan abin da yanayinta ya ƙyale ta ta bayar.—2 Kor. 8:1-5, 12.
Karɓan Taimako da Hali Mai Kyau
Duk da haka, da akwai lokacin da za ka bukaci samun taimakon ikilisiya. Kada ka yi jinkirin karɓan taimakon da ikilisiya za ta iya bayarwa sa’ad da kake fama ka jimre da matsi na wannan zamanin. Jehobah ya yi tanadin maza masu kula da suka manyanta su “yi kiwon ikilisiyar” su taimake ka sa’ad da kake fuskantar gwaji da tsanantawa. (A. M. 20:28) Ya kamata dattawa da waɗanda suke cikin ikilisiya su ƙarfafa, su tallafa, kuma su kāre ka lokacin da kake fuskantar yanayi mai wuya.—Gal. 6:2; 1 Tas. 5:14.
Amma, ka tabbata cewa sa’ad da ka samu taimako da kake bukata, za ka yi hakan da hali mai kyau. A koyaushe, ka riƙa nuna godiya don taimakon da ka samu. Ka ɗauki irin wannan taimako da ’yan’uwa masu bi suka yi maka a matsayin alheri daga Allah. (1 Bit. 4:10) Me ya sa hakan yake da muhimmanci? Domin ba ma son mu karɓi taimako yadda mutane da yawa a duniya suke yi ba tare da nuna godiya ba.
Ka Kasance da Daidaitaccen Ra’ayi da Sanin Ya Kamata
A wasiƙar da ya rubuta wa ikilisiyar da ke Filibbi, Bulus ya ce game da Timoti: “Ba ni da kowa wanda hankalinsa ya yi daidai da nasa ba, wanda zai yi tattalin zamanku da gaskiya.” Amma Bulus ya daɗa: “Su duka biɗa ma kansu suke yi, ba na Yesu Kristi ba.” (Filib. 2:20, 21) Ta wurin tuna da wannan abin da Bulus ya lura da shi, ta yaya mu a yau za mu guji shagala ainun da ‘biɗan’ namu abubuwa?
Bai kamata mu riƙa yawan biɗan abubuwa sa’ad da muke son wasu a cikin ikilisiya su yi amfani da lokacin da kulawansu su taimake mu magance matsalolinmu. Me ya sa? Ka yi tunanin wannan: Babu shakka za mu yi godiya sosai idan wani ɗan’uwa ya ba mu gudummawa don ya taimake mu idan muna da bukata na gaggawa. Amma za mu taɓa biɗar wannan taimakon abubuwan biyan bukata? A’a. Hakanan ma, ko da yake ’yan’uwanmu a koyaushe suna farin ciki su taimake mu, ya kamata mu kasance da daidaita da kuma sanin ya kamata a yawan lokacinsu da muke so su ba mu. Ballantana ma, ko menene ’yan’uwa masu bi suka yi don su taimake mu mu jimre da lokacin wahala, za mu so su yi hakan da yardan rai.
Ka tabbata cewa ’yan’uwanka maza da mata za su kasance a shirye da yardan rai a koyaushe su ba ka taimako. Har ila, a wani lokaci ba za su iya biyan dukan bukatarka ba. Idan hakan ya faru, ka tabbata cewa Jehobah zai kiyaye ka, yadda ya yi wa mai zabura, a dukan gwaji da kake fuskanta.—Zab. 116:1, 2; Filib. 4:10-13.
Saboda haka, kada ka ƙi karɓan kowane tanadi da Jehobah ya yi maka, musamman a lokacin baƙin ciki da matsala. (Zab. 55:22) Yana son ka yi hakan. Amma yana son ka zama “mai-bayarwa da daɗin rai.” Saboda haka, ka aika bisa yadda ka ‘annita a zuciyarka’ ka ba da ko menene yanayinka ya ƙyale ka wajen tallafa wa bauta ta gaskiya. (2 Kor. 9:6, 7) A wannan hanyar, za ka iya nuna godiya sa’ad da ka sami taimako da kuma sa’ad da ka bayar da dukan zuciyarka.
[Akwati/Hotunan da ke shafi na 31]
“Me zan bayar ga Ubangiji sabili da dukan alherinsa a gareni?”—Zab. 116:12
▪ Ka nemi zarafin “aika nagarta zuwa ga dukan mutane”
▪ Ka zama mai ba da ƙarfafa da kuma wartsakewa a ruhaniya ga wasu
▪ Ka yi aikin almajirantarwa yadda yanayinka ya ƙyale ka