Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/1 pp. 16-18
  • Sa’ad da Miji ko Mata Ya ko Tana da Bukata ta Musamman

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sa’ad da Miji ko Mata Ya ko Tana da Bukata ta Musamman
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi La’akari da Juna
  • Ka Kasance da Daidaitaccen Tsari
  • Ku Ƙoƙarta Ku Kasance da Tunani Mai Kyau
  • Yadda Za Ka Daraja Matarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yadda Za a Yi Nasara a Shekara ta Farko na Aure
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Magance Matsaloli
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ku Nemi Taimakon Allah don Ku Ji Daɗin Aurenku
    Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/1 pp. 16-18

Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali

Sa’ad da Miji ko Mata Ya ko Tana da Bukata ta Musamman

Tun da aka gano cewa ina da ciwon yawan gajiya mai tsanani, mijina ne kadai yake yin dukan ayyuka. Amma bai taba tattauna batun kuɗi da ni ba. Me ya sa ba ya tattauna batun kuɗi da ni? Hakan ya sa ina tunani cewa dukiyarmu ta soma taɓarɓarewa sosai kuma ya san cewa zan yi fushi idan na sani.—Salamatu.a

AURE yana da ƙalubale sosai, amma sa’ad da miji ko matar take rashin lafiya mai tsanani, matsalar tana iya daɗuwa.b Kana kula da aboki ko abokiyar aure marar lafiya ne? Idan haka ne, shin ɗaya daga cikin waɗannan tambayoyin tana damun ka kuwa: ‘Yaya zan jimre idan ciwon ya daɗa tsanani sosai? Yaya zan ci gaba da kulawa da aboki ko abokiyar aure ta ko na kuma in dinga yin dahuwa, wanke-wanke, da wasu ayyuka? Me ya sa nake jin cewa da wannan ciwon ya same ni ba abokiya ko abokin aure na ba?’

A wani ɓangaren kuma, idan kai ne marar lafiyar, za ka iya yin tunani: ‘Ta yaya zan iya girmama kaina sa’ad da na kasa ɗaukan nauyi na na iyali? Shin abokiya ko abokin aure na yana ko tana ƙyama ta saboda ba ni da lafiya? Shin farin cikinmu a matsayin ma’aurata ya ƙare kenan?’

Abin baƙin ciki, an kashe wasu aure saboda ciwo mai tsanani. Duk da haka, hakan baya nufin cewa aurenka zai rabu.

Ma’aurata da yawa suna rayuwa kuma suna yin nasara duk da ciwo mai tsanani. Alal misali, ka yi la’akari da Yoshiaki da Kazuko. Raunin da Yoshiaki ya samu a kashin bayansa ya sa bai iya yin ko ɗan motsi ba tare da taimako ba. Kazuko ta bayyana: “Mijina yana bukatar taimako a komai. A sakamakon kula da shi, wuya na, kafaɗa na, da hannaye na suna mini ciwo, kuma ni ma ina zuwa asibitin ƙashi kullum. Nakan ji cewa kula da mutum yana da wuya sosai.” Duk da wahalolin, Kazuko ta ce: “Gaminmu a matsayin ma’aurata ya daɗa ƙarfi.”

Menene asirin farin ciki a irin wannan yanayin? Abu na ɗaya shi ne, waɗanda suke da gamsuwa da wadar zuci a aurensu suna ɗaukan ciwo kamar farmaki ne ga su biyu ba ga wanda yake da ciwon ba. Ballantana ma, idan ɗaya bai da lafiya, zai shafi dukansu biyu, ko da a hanya dabam dabam ne. An bayyana wannan dangantaka ta taimakawa juna da ke tsakanin miji da mata a Farawa 2:24: ‘Mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa, ya manne wa matatasa: za su zama nama ɗaya kuma.’ Saboda haka, idan miji ko mata yana ko tana da ciwo, yana da wuya sosai su biyun su yi aiki tare don magance ƙalubalen.

Ƙari ga hakan, bincike ya nuna cewa ma’aurata da suka kasance da dangataka mai kyau sa’ad da ciwo mai tsanani ya taso suna karɓar abin da ya faru kuma su nemi mafita. Hanyoyin jurewa masu yawa da suka koya sun jitu da waɗanda suke cikin Littafi Mai Tsarki. Ka yi la’akari da waɗannan shawarwari guda uku.

Ku Yi La’akari da Juna

“Gwamma biyu da ɗaya,” In ji Mai-Wa’azi 4:9. Me ya sa? Domin, aya ta 10 ta bayyana, “idan sun faɗi, ɗaya za ya ɗaga ɗan’uwansa.” Kuna ‘ɗaga aboki ko abokiyar aurenku sama kuwa’ ta wajen nuna godiya?

Kuna neman hanyar da za ku taimaka wa juna? Yong, wanda matarsa ta ɗan naƙasa, ya ce: “Ina ƙoƙarin yin la’akari da matata a kowane lokaci. Duk lokacin da nake jin ƙishirwa, ina tunani cewa ita ma tana jin ƙishirwa. Idan ina so na fita waje don na duba mahalli mai kyau, nakan tambaye ta ko za ta so mu je tare. Muna shan azabar da kuma jure wa yanayin tare.”

A wani ɓangaren kuma, idan aboki ko abokiyar aurenka tana kula da kai, shin da akwai wasu abubuwa da za ku iya yi wa kanku ba tare da sa lafiyarku a haɗari ba? Idan haka ne, za ka iya daɗa wa kanka ko kanki daraja kuma hakan zai iya sa ku ci gaba da ba da taimako.

Maimakon yin tunanin cewa ka san yadda ya kamata ka bi da abokiyar aurenka, zai fi dacewa ka tambaye ta abin da ta fi so? Salamatu, wacce aka ambata da farko, ta gaya wa mijinta yadda take ji domin bata san yanayin dukiyarsu ba. Yanzu mijinta yana tattauna wannan batun da ita.

KA GWADA WANNAN: Ku lissafa hanyoyin da kuke ganin cewa aboki ko abokiyar aure za ta iya kyautata yanayin da kuke ciki a yanzu, kuma ka sa shi ko ita ta yi hakan. Sai ku musanya takardar lissafin. Kowannenku ya zaɓi shawara ɗaya ko biyu da za ku iya yin amfani da ita.

Ka Kasance da Daidaitaccen Tsari

“Ga kowane abu akwai nasa kwanaki,” in ji Sarki Sulemanu. (Mai-Wa’azi 3:1) Amma, zai iya kasance da wuya a kasance da daidaitaccen tsari, saboda matsaloli da ciwo mai tsanani ke tattare da su. Menene za ka yi don ka samu daidaita?

Za ku iya yin hutu tare a wasu lokatai ba tare da yin tunani game da neman magani ba. Za ku iya more wasu abubuwan da kuke yi tare kafin ciwon ya fara? Idan ba zai yiwu ba, waɗanne abubuwa ne za ku iya yi? Za ku iya yi wa juna karatu ko kuma koyon sabon harshe. Yin abubuwa da ciwon ba zai hana ku yi ba tare zai ƙarfafa dangantakarku na “nama ɗaya,” kuma zai daɗa farin cikinku.

Wani abin da zai taimaka shi ne kasance da daidaita sa’ad da kuke tare da wasu. Littafi Mai Tsarki ya ce a Misalai 18:1: “Wanda ya ware kansa dabam, muradin kansa ya ke biɗa, yana kuwa hauka gāba da sahihiyar hikima duka.” Ka lura cewa a cikin ayar an ce ware kai zai iya shafar tunanin mutum a mummunar hanya? Akasin haka, yin tarayya da wasu a wasu lokatai zai iya daɗaɗa ka ya kuma taimake ka ka daidaita tunaninka. Me zai hana ka gayyatar wani ya ziyarce ka?

A wasu lokatai, daidaituwa yakan zama matsala ga wanda ko wadda yake ko take kula da aboki ko abokiyar aure. Wasu sukan soma aikace-aikace da yawa, kuma hakan yakan gajiyar da su, ya kuma raunana lafiyarsu. Daga baya, sukan iya ƙasa ci gaba da kula da abokin ko abokiyar aurensu. Saboda haka, idan kana ko kina kula da aboki ko abokiyar aure da ke da ciwo mai tsanani, kada ka watsar da bukatun kanka ko kanki. Ku keɓe lokaci a kai a kai a inda babu surutu don ku huta.c Wasu sukan ga amfanin yin magana game da alhininsu a wasu lokatai ga amini ko aminiyarsu da ke jinsi ɗaya da su.

KA GWADA WANNAN: Ku lissafa a takarda ƙalubalen da kuke fuskanta don kula da aboki ko abokiyar aure. Sai ku rubuta abubuwan da za ku yi don ku magance su ko kuma ku jimre su sosai. Maimakon cika bayyana su, ku tambayi kanku, ‘Mecece hanya mafi sauƙi na daidaita yanayin?’

Ku Ƙoƙarta Ku Kasance da Tunani Mai Kyau

Littafi Mai Tsarki ya ba da gargaɗi: “Kada ka tambaya, Don me kwanakin dā sun fi na yanzu kyau?” (Mai-Wa’azi 7:10) Saboda haka, ku daina tunani game da yadda rayuwarku za ta kasance da a ce ciwon bai taso ba. Ku tuna cewa a wannan duniyar, dukan farin ciki yana da abin da ke ɓata shi a wasu hanya. Asirin shi ne ku karɓi yanayin da kuke ciki, kuma ku nemi yadda za ku jimre.

Menene zai iya taimaka wa kai da abokiyar aurenka a wannan batun? Ku tattauna albarkarku tare. Ku yi farin ciki idan kun samu lafiya ko da ɗan kaɗan ne. Ku nemi abubuwan za ku so ku gani a nan gaba, kuma ku kafa makasudai da za ku iya cim ma tare.

Ma’aurata biyu masu suna Shoji da Akiko sun yi amfani da waɗannan shawarwari, kuma sun samu sakamako mai kyau. Sa’ad da aka bayyana cewa Akiko tana da ciwo mai suna fibromyalgia, sai suka daina hidima ta musamman a matsayin masu hidima na cikakken lokaci na Kirista. Sun yi sanyin gwiwa kuwa? E. Duk da haka, Shoji ya ƙarfafa duk waɗanda suke cikin irin wannan yanayin: “Kada ku samu sanyin gwiwa ta yin tunani akan abin da ba ku iya yi kuma ba. Ku kasance da daidaitaccen ra’ayi. Ko da ku biyun kuna da begen komawa yanayinku na dā, ku mai da hankali ga yanayinku na yanzu. Ni kuwa, hakan yana nufin mai da hankali ga matata da kuma taimaka mata.” Irin wannan shawara mai amfani za ta iya taimaka idan aboki ko abokiyar aurenka tana da bukata na musamman.

[Hasiya]

a An canja wasu sunaye.

b Wannan talifin ya tattauna yanayin da miji ko mata take rashin lafiya. Amma dai, ma’aurata da suke jimre wa matsaloli na zahiri saboda haɗari ko kuma matsalar motsin rai kamar baƙin ciki za su iya samun taimako ta yin amfani da wannan talifin.

c Dangane da yanayinku, zai iya kasance da amfani ku samu taimako a wasu lokatai daga masu kiwon lafiya, ko masu ba da taimako a unguwa.

KA TAMBAYI KANKA . . .

Menene aboki ko abokiyar aure na take bukata yanzu?

▪ Ku yi magana sosai game da ciwon

▪ Kada ku cika magana game da ciwon

▪ Kada ku cika damuwa

▪ Ku yi la’akari da juna sosai

▪ Ku yi wasu ayyukan da ba su shafi ciwon ba

▪ Ku yi cuɗanya da wasu

▪ Ku kafa wa juna makasudai

[Hoton da ke shafi na 18]

Don ku samu daidaita a rayuwarku, zai yiwu ku more wasanni tare kuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba