Tambayoyi Daga Masu Karatu
Shin Ezekiel 18:20 da ta ce “ɗan ba za ya ɗauki laifin ubansa ba,” ya saɓa wa Fitowa 20:5 da ta ce Jehobah yana “kāma ’ya’ya da muguntar ubanni” ne?
Babu saɓani. Ɗaya ya mai da hankali ne ga lissafin da mutum zai ba da, ɗayan kuma ya nuna gaskiyar cewa sakamako kuskuren mutum zai iya shafan zuriyarsa.
Mahallin Ezekiel sura na 18 ya nuna cewa an nanata lissafin da mutum zai ba da ne. “Mai-rai da ya yi zunubi, shi za ya mutu,” in ji aya ta 4. Mutum ‘adali da yake kuwa aika abin da ke halal da daidai” kuma fa? “Za ya yi rai.” (Ezek. 18:5, 9) Bayan da mutum ya kai shekarar da zai iya ba da lissafin abin da ya yi, za a yi wa kowane mutum ‘shari’a bisa ga al’amuransa.’—Ezek. 18:30.
An kwatanta wannan ƙa’idar a abin da ya sami wani Balawi mai suna Kora. A lokacin da Isra’ila take tafiya cikin jeji, Kora bai gamsu kuma ba da aiki na musamman da Jehobah ya ba shi. Sa’ad da yake ƙoƙari ƙwace ayyukan firist, Kora da wasu sun yi tawaye ga wakilan Jehobah, Musa da Haruna. Jehobah ya halaka Kora da waɗanda suka yi tawaye da shi, domin girman kai da suka nuna na neman gatan da bai cancance su ba. (Lit. Lis. 16:8-11, 31-33) Amma, ’ya’yan Kora ba su yi tawayen ba. Allah bai kama su da laifi ba domin zunubin babansu. Amincinsu ga Jehobah ya sa aka ceci ransu.—Lit. Lis. 26:10, 11.
Gargaɗin da ke Fitowa 20:5 wanda sashe ne na Dokoki Goma kuma fa? Ka yi la’akari kuma da mahallin. Jehobah ya kafa Dokar alkawari da al’ummar Isra’ila. Bayan sun ji kalaman alkawarin, Isra’ilawa suka sanar a fili: “Abin da Ubangiji ya faɗi duka mu a yi.” (Fit. 19:5-8) Da haka, al’ummar gabaki ɗaya suka shiga cikin dangantaka na musamman da Jehobah. Saboda haka, dukan al’ummar ne aka yi wa kalaman da ke Fitowa 20:5.
Sa’ad da Isra’ilawa suka kasance da aminci ga Jehobah, al’ummar ta amfana kuma ta more albarka mai yawa. (Lev. 26:3-8) Amma, sa’ad da al’ummar Isra’ila ta ƙi Jehobah kuma ta bi allolin ƙarya, Jehobah ya janye albarkarsa da kāriya; al’ummar ta sha masifa. (Alƙa. 2:11-18) Hakika, da akwai wasu da suka kasance da aminci kuma suka yi biyayya ga dokokin Allah duk da cewa al’ummar ta soma bauta wa gumaka. (1 Sar. 19:14, 18) Wataƙila masu aminci sun sha wahala domin zunuban al’ummar, amma Jehobah ya nuna musu ƙauna ta alheri.
Sa’ad da Isra’ila ta taka ƙa’idodin Jehobah a fili wanda hakan ya sa sunansa ya zama abin ba’a tsakanin al’ummai, Jehobah ya ƙuduri aniyar yi wa mutanensa horo ta wajen ƙyale su a kwashe su zuwa bauta a Babila. Hakan ya ƙunshi yi wa mutane ɗaɗɗaya da kuma mutanensa a matsayin rukuni horo. (Irm. 52:3-11, 27) Hakika, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa zunubin al’ummar Isra’ila ya yi yawa sosai da har mummunan halayen kakaninsu ya shafi tsararaki uku, huɗu ko fiye da haka, kamar yadda Fitowa 20:5 ta faɗa.
Kalmar Allah tana ɗauke da labarai inda mugun halin iyaye ya shafi iyalai. Babban Firist Eli ya ɓata wa Jehobah rai ta wajen ƙyale ’ya’yansa maza lalatattu da “ba su da kirki” su ci gaba da zama firistoci. (1 Sam. 2:12-16, 22-25; Littafi Mai Tsarki) Domin Eli ya ɗaukaka ’ya’yansa fiye da Jehobah, Allah ya faɗi cewa za a yanke iyalin Eli daga tsarin babban firist, wanda ya soma daga tattaɓa-kunnensa, wato, Abiathar. (1 Sam. 2:29-36; 1 Sar. 2:27) An kwatanta ƙa’idar da ke Fitowa 20:5 da misalin Gehazi kuma. Ya yi amfani da matsayinsa na bawan Elisha a hanyar da bai dace ba domin ya sami arziki daga warkar da Naaman, Janar ɗan Suriya. Ta wurin Elisha, Jehobah ya yi shelar hukunci, cewa: “Kuturta fa ta Na’aman za ta manne maka, har da zuriyarka har abada.” (2 Sar. 5:20-27) Saboda haka, sakamakon laifin Gehazi ya shafi zuriyarsa.
A matsayin Mahalicci da Mai ba da rai, Jehobah yana da ikon ba da horo da ya yi daidai kuma ya dace. Misalai na baya sun nuna cewa yara ko zuriya suna iya fuskantar sakamakon zunubin kakanninsu. Amma, Jehobah yana jin “kukar ƙuntatattu” kuma mutanen da suka juya gare shi suna iya samun amincewarsa har kuma su sami sauƙi.—Ayu. 34:28.
[Hoton da ke shafi na 29]
Kora da waɗanda suka yi tawaye tare da shi sun ba da lissafin ayyukansu