Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 5/15 pp. 6-7
  • Me Ya Sa Za a Girmama Tsofaffi?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Za a Girmama Tsofaffi?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • Jehobah Yana Kula Da Bayinsa Tsofaffi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ku Girmama Tsofaffi da ke Tare da Ku
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Kula Da Tsofaffi Hakki Ne Na Kirista
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Kana A Kan Gaba Wajen Girmama ’Yan’uwa Masu Bi Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 5/15 pp. 6-7

Me Ya Sa Za a Girmama Tsofaffi?

DAB da tekun da ke Kalifoniya, a ƙasar Amirka, akwai wani itace da aka fi ɗaukan hotonsa a duniya. Ana kiransa itacen Fir. Bisa rahoto, wannan itacen ya fi shekara ɗari biyu da hamsin. Domin haƙurinsa, wannan kyakkyawan itacen ya sami kulawa a hanyoyi dabam-dabam. Alal misali, an kewaye shi da wayoyi da kuma duwatsu a tushensa.

Itacen Fir zai iya tunasar da mu da tsofaffi Kiristoci da suke tsakaninmu, waɗanda suka nuna gagarumar jimiri. Fitacciyar hanya guda da suka nuna wannan ita ce ta wurin shelar bishara. Annabi Joel ya annabta cewa “tsofaffi” za su yi shelan saƙon Littafi Mai Tsarki. (Joel 2:28-32; A. M. 2:16-21) Ka ɗan yi tunani a kan sa’o’i da yawa da irin waɗannan suke yi da ƙwazo domin su taimaka wa wasu su koya game da ‘bishara ta mulki’! (Mat. 24:14) Wasu daga cikin waɗannan masu shelar Mulki sun jimre tsanani ko kuma wasu wahaloli. Idan an san itacen Fir da jimrewa kuma an kewaye shi da duwatsu da kuma wayoyi, tsofaffi da suke tsakaninmu sun cancanci a amince da su kuma a girmama su!

Jehobah Allah ya ƙarfafa mutanensa na dā: “Za ka tashi tsaye a gaban mai-furfura, a bada girma ga fuskar dattijo.” (Lev. 19:32) A cikin bayin Jehobah a yau, akwai misalan mutane masu aminci da suke yin ‘tafiya tare da Allah’ shekaru da yawa. (Mi. 6:8) Yayin da suka ci gaba da yin amfani da ƙa’idodin Nassi, furfurarsu zai zama “rawanin daraja.”—Mis. 16:31.

Manzo Bulus ya gargaɗi matashi Timotawus: “Kada ka tsauta wa dattijo.” Amma ya kamata Timotawus ya yi “roƙonsa kamar uba” kuma “dattijai mata . . . kamar uwaye.” (1 Tim. 5:1, 2) Wato, an bukaci Timotawus ya “tashi tsaye” a gaban mai furfura. A bayyane yake cewa, Jehobah yana bukatan furcinmu ya kasance da irin wannan ban girma.

“Kuna gabatar da juna cikin bangirma,” in ji Romawa 12:10. Babu shakka, masu kula a ikilisiya za su nuna bangirma ga tsofaffi Kiristoci. Amma dukanmu na bukatan mu riga nuna ban girma ga juna.

Hakika, waɗanda suke cikin iyali suna da hakki na musamman ga iyayensu da kuma kakanninsu. A batun itacen Fir, mutane sun nemi hanyoyi da yawa da za su rayar da shi, kuma sun ci gaba da yin hakan. Hakika fa, ya kamata mu nemi hanyoyin da za mu ci gaba da nuna bangirma ga iyayenmu da kakanninmu tsofaffi. Alal misali, yin sauraro da kyau zai hana mu nace a yin abu a namu hanya ba tare da jin ra’ayinsu ba.—Mis. 23:22; 1 Tim. 5:4.

Tsofaffi da ke tsakaninmu suna da tamani a gaban Jehobah. Bai yashe su ba. (Zab. 71:18) Allah na gaskiya da gaske yana ƙarfafa su su ci gaba da bauta masa da aminci. Bari mu ma mu ci gaba da tokara da kuma girmama tsofaffi.

[Hotuna da ke shafi na 7]

Kamar yadda itacen Fir yake bukatar tokarawa, tsofaffi ma suna bukatan a bi da su da daraja da kuma ban girma

[Inda Aka Ɗauko]

American Spirit Images/age fotostock

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba