Ka Kusaci Allah
“Mai-Jin Addu’a”
1 LABARBARU 4:9, 10
SHIN Jehobah Allah yana amsa sahihan addu’o’in masu bauta masa da aminci kuwa? Labarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki na wani mutum mai suna Jabez wanda abubuwa kaɗan ne kawai muka sani game da shi ya nuna cewa Jehobah “Mai-Jin Addu’a” ne. (Zabura 65:2) An samo wannan gajeren labarin ne a inda ba za ka taɓa tsammani ba, wato, a tsakiyar jerin sunayen zuriyoyi da ya buɗe littafin Labarbaru na Ɗaya. Bari mu bincike 1 Labarbaru 4:9, 10.
Dukan abubuwan da muka sani game da Jabez yana rubuce ne a cikin waɗannan ayoyin biyu. In ji aya ta 9, mahaifiyarsa “ta kira sunansa Jabez, tana cewa, da baƙinciki [“wahala” NW] na haife shi.”a Me ya sa ta zaɓi irin sunan nan? Ta yi naƙuda fiye da kima a lokacin da take son ta haifi wannan ɗan ne? Ko kuwa ita gwauruwa ce, tana baƙin cikin cewa mijinta ya riga ya mutu kafin ta haifi ɗansu? Littafi Mai Tsarki bai ce ba. Amma wata rana wannan uwar za ta samu dalilin yin alfahari sosai da ɗanta. Mai yiwuwa ’yan’uwan Jabez maza ne masu aminci, amma “Jabez ya fi ’yan’uwansa daraja.”
Jabez mutumi ne mai yin addu’a. Ya soma add’uarsa ne da neman albarkar Allah. Ya roƙi abubuwa guda uku da suka nuna cewa yana da bangaskiya sosai.
Na farko, Jabez ya roƙi Allah, yana cewa: “Ka yalwatadda rabona.” (Aya ta 10) Wannan mutumin mai daraja ba mai ƙwacen ƙasa ba ne, wanda ke kwaɗayin kayan ɗan’uwansa. Wannan roƙon da ya yi da zuciya ɗaya wataƙila ya shafi mutane ne fiye da ƙasa. Wataƙila yana roƙon faɗaɗa iyakar yankinsa ne cikin salama don ta ɗauki ƙarin mutane masu bauta wa Allah na gaskiya.b
Na biyu, Jabez ya roƙi “hannun” Allah ya kasance da shi. Hannun Allah na alama shi ne ikon da yake nunawa, wanda yake amfani da shi ya taimaki masu bauta masa. (1 Labarbaru 29:12) Don ya samu bukatun da ke zuciyarsa, Jabez ya dogara da Allahn da hannunsa bai gajarta ba ga waɗanda suka yi imani da shi.—Ishaya 59:1.
Na uku, Jabez ya yi add’ua: ‘Ka kiyaye ni daga mugunta, kada ta ciwuce ni!’ Furcin nan “kada ta ciwuce ni” mai yiwuwa yana nufin cewa Jabez ya yi addu’a ne, ba don ya tsira daga bala’i ba, amma domin ya kauce wa yin baƙin ciki ko kuma sakamakon mugunta ya sha kansa.
Addu’ar Jabez ta nuna yadda ya damu da bauta ta gaskiya da kuma bangaskiyarsa da dogararsa ga Mai jin addu’a. Mene ne Jehobah ya yi? Wannan gajeren labarin ya kammala da kalmomin nan: “Allah fa ya yarda masa da abin da ya roƙa.”
Mai jin addu’a bai canja ba. Yana farin cikin jin addu’o’in masu bauta masa. Waɗanda suka ba da gaskiya kuma suka dogara da shi suna iya kasancewa da wannan tabbacin: “Idan mun roƙi komi daidai da nufinsa, yana jinmu.”—1 Yohanna 5:14.
[Hasiya]
a Sunan nan Jabez ya samo asali ne daga kalmar da ke nufin “azaba.”
b Targums, wanda fassara ne na Yahudawa na Nassosi Masu Tsarki, ya fassara kalmomin Jabez kamar haka: “Ka albarkace ni da yara, kuma ka faɗaɗa yankina da almajirai.”