Samun Tagomashin Allah Yana Kai Ga Samun Rai Na Har Abada
“Za ka albarkaci mai-adalci; Ya Ubangiji, da tagomashi za ka kewaye shi kamar da garkuwa.”—ZAB. 5:12.
1, 2. Mene ne Iliya ya roƙa daga gwauruwa a Zarefat, kuma wane tabbaci ne ya ba ta?
MATAR da ɗanta da kuma annabin Allah suna jin yunwa. Yayin da gwauruwa a Zarefat take shirin yin girki, annabi Iliya ya gaya mata ta ba shi ruwa da abinci. Tana a shirye ta ba shi ruwa ya sha, amma iyakar abin da take da shi, shi ne “tāfin gāri cikin tukunya, da mai kaɗan a cikin kurtu.” Ta gaya masa haka ne don tana jin ba ta da isashen abinci da za ta ba annabin.—1 Sar. 17:8-12.
2 Iliya ya nace: “Ki fara yi mani ɗan waina tukuna, ki kawo mani ita, daga baya ki yi wa kanki da ɗanki. Gama haka nan Ubangiji ya faɗi, Allah na Isra’ila, Tukunyar gāri ba za ta sare ba, kurtun mai kuma ba za ya sare ba.”—1 Sar. 17:13, 14.
3. Wane batu mai muhimmanci ne yake gabanmu?
3 Batun da ke gaban gwauruwar ya fi muhimmanci da tsai da shawara a kan abin da za ta yi da ɗan abincinta da ya rage. Shin za ta dogara ga Jehobah don ya cece ta da ɗanta, ko za ta saka bukatunta a gaba fiye da samun amincewa da kuma yin abuta da Allah? Ya kamata mu ma mu tsai da irin wannan shawarar. Shin za mu fi damuwa da samun abin duniya fiye da samun amincewar Jehobah? Muna da kowane dalili na dogara ga Allah da kuma bauta masa. Kuma da akwai matakai da za mu iya ɗauka don mu biɗa kuma mu samu amincewarsa.
‘Kai Ne Mai-Isa Ka Karɓi Bauta’
4. Me ya sa Jehobah ya cancanci mu bauta masa?
4 Jehobah yana da iko ya bukaci ’yan Adam su bauta masa yadda yake so. Rukunin bayinsa na samaniya sun tabbatar da hakan da haɗin kai, suna cewa: “Kai ne mai-isa ka karɓi ɗaukaka da daraja da iko, ya Ubangijinmu da Allahnmu: gama kai ka halicci dukan abu, saboda nufinka kuma suka kasance, saboda nufinka aka halicce su.” (R. Yoh. 4:11) Domin shi ne Mahalicci, Jehobah ya cancanci mu bauta masa.
5. Me ya sa ya kamata ƙaunar Allah ta motsa mu mu bauta masa?
5 Wani dalili kuma da ya sa za mu bauta wa Jehobah shi ne cewa babu wanda yake ƙaunarmu kamarsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah fa ya halicce mutum cikin kamaninsa, cikin kamanin Allah ya halicce shi; na miji da ta mace ya halicce su.” (Far. 1:27) Allah ya ba wa ’yan Adam ’yancin yin tunani da kuma tsai da shawarwari. Ta wajen ba mu rai, Jehobah ya zama Uba ga ’yan Adam. (Luk 3:38) Kamar mahaifi mai kirki, ya yi kome don ya yi tanadin abin da yaransa maza da mata suke bukata don su more rayuwa. “Ya kan sa ranatasa ta fito” kuma ya “aiko da ruwa,” don Duniya ta ba da abinci a yalwace a kyakkyawan mahalli.—Mat. 5:45.
6, 7. (a) Wace illa ce Adamu ya jawo wa dukan zuriyarsa? (b) Mene ne hadayar Kristi za ta yi wa waɗanda suke biɗan amincewar Allah?
6 Jehobah ya kuma cece mu daga mugun sakamako na zunubi. Ta wajen yin zunubi, Adamu ya zama ɗan caca da ya yi sata daga iyalinsa don ya yi caca. Ta wajen yin tawaye da Jehobah, Adamu ya hana yaransa abin da ya kamata su more, wato, farin ciki na har abada. Son kansa ya sa ’yan Adam cikin bauta a ƙarƙashin shugaba azzalumi, wato ajizanci. Saboda haka, dukan ’yan Adam suna rashin lafiya, suna baƙin ciki, kuma a ƙarshe su mutu. ’Yantar da bawa na bukatar biyan kuɗi, kuma Jehobah ya biya wani abu don ya cece mu daga waɗannan mugayen sakamako. (Karanta Romawa 5:21.) Ta aikatawa daidai da nufin Ubansa, Yesu Kristi ya ba da “ransa kuma abin fansar mutane dayawa.” (Mat. 20:28) Ba da daɗewa ba, waɗanda suka samu amincewar Allah za su samu cikakken amfanin wannan fansa da aka ba da.
7 Mahaliccinmu, Jehobah ya yi abubuwa fiye da kowane mutum don ya sa mu yi rayuwa mai ma’ana da farin ciki. Ta samun amincewarsa, za mu iya ganin yadda yake yin abubuwa don ya kawar da dukan ɓarna da aka yi wa ’yan Adam. Jehobah zai nuna wa kowannenmu yadda ya zama “mai-sākawa ne ga dukan waɗanda ke biɗarsa.”—Ibran. 11:6.
‘Mutanenka Za Su Ba da Kansu Hadaya da Yardan rai’
8. Mene ne abin da Ishaya ya fuskanta ya koya mana game da bauta wa Allah?
8 Samun amincewar Allah ya ƙunshi yin amfani da ’yancinmu yadda ya dace. Domin Jehobah ba ya tilasta wa kowa ya bauta masa. A zamanin Ishaya, Ya yi tambaya: “Wa zan aika, kuma wanene za ya tafi domin mu?” Jehobah ya daraja annabin ta wajen ba shi damar tsai da shawara. Ka yi tunanin gamsuwar da Ishaya ya yi sa’ad da ya amsa: “Ga ni; ka aike ni.”—Isha. 6:8.
9, 10. (a) Da wane ra’ayi ne ya kamata mu bauta wa Allah? (b) Me ya sa ya dace mu bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu?
9 ’Yan Adam suna da ’yancin bauta wa Allah ko kuma su ƙi yin hakan. Jehobah yana son mu bauta masa da yardan rai. (Karanta Joshua 24:15.) Allah ba ya amince da duk wanda ya ƙi bauta masa; kuma ba zai karɓi bautar waɗanda ainihin muradinsu shi ne su faranta wa ’yan Adam rai ba. (Kol. 3:22) Idan muna yin tsarkakkiyar hidima da ‘jinkiri’ ta wurin barin abubuwan duniya su shiga tsakanin bautarmu ga Allah, ba za mu samu amincewar Allah ba. (Fit. 22:29) Jehobah ya san cewa yana da kyau mu bauta masa da dukan zuciyarmu. Musa ya aririce Isra’ilawa su zaɓi rai ‘ta wajen ƙaunar Ubangiji Allahnsu, ta jin muryarsa, da kuma manne masa.’—K. Sha 30:19, 20.
10 Sarki Dauda na Isra’ila ta dā ya rera waƙa ga Jehobah: “Mutanenka suna bada kansu hadaya da yardan rai cikin ranar ikonka: Cikin jamalin tsarki, daga cikin cikin safiya, Kana riƙe da raɓar ƙuruciyarka.” (Zab. 110:3) Mutane da yawa a yau suna saka arziki da jin daɗi farko a rayuwarsu. Amma, ga waɗanda suke ƙaunar Jehobah, tsarkakkiyar hidimarsu ita ce ke kan gaba da kome. Yadda suke wa’azin bishara da himma ya nuna abin da ya fi muhimmanci a gare su. Suna da cikakken tabbaci cewa Jehobah zai iya tanadar da bukatunsu na kullum.—Mat. 6:33, 34.
Hadayu da Allah Yake Amincewa da Su
11. Wane amfani ne Isra’ilawa suka yi begen samu ta wajen miƙa hadayu ga Jehobah?
11 A ƙarƙashin Dokar alkawari, mutanen Allah suna miƙa hadayu da suka dace don su samu amincewarsa. Levitikus 19:5 ya ce: “Sa’anda za ku miƙa hadayu na salama ga Ubangiji, sai ku miƙa ta yadda za a karɓe ku.” Wannan littafin ya kuma ce: “Sa’anda ku ke yanka hadaya ta godiya ga Ubangiji, sai ku yi irin da za a karɓe ku.” (Lev. 22:29) Sa’ad da Isra’ilawa suka miƙa hadayun da suka dace na dabba a kan bagadin Jehobah, hayaƙin da ke tashiwa yana kama da “shesheƙi mai-ƙamshi.” (Lev. 1:9, 13) Ya yi farin ciki kuma ya karɓa waɗannan alamar ƙauna daga mutanensa. (Far. 8:21) A waɗannan fannoni na Dokar, mun samu ƙa’ida da ta shafe mu a yau. Waɗanda suke miƙa hadayu da Jehobah yake karɓa suna samun amincewarsa. Waɗanne hadayu ne yake amincewa da su? Ka yi la’akari da wurare biyu na rayuwa: halinmu da furcinmu.
12. Waɗanne ayyuka ne za su sa ‘miƙa jikunanmu hadaya’ ya ɓata wa Allah rai?
12 A wasiƙarsa zuwa ga Romawa, manzo Bulus ya rubuta: “Ku miƙa jikunanku hadaya mai-rai mai-tsarki, abin karɓa ga Allah, bautarku mai-ruhaniya ke nan.” (Rom. 12:1) Samun amincewar Allah yana bukatar mutum ya sa jikinsa ya zama abin karɓa ga Allah. Idan zai ɓata kansa da sigari da tauna betel nut [wata ’ya’yar itace mai bugarwa] da shan ƙwaya, ko kuma yin maye, wannan hadaya ba za ta kasance da amfani ba. (2 Kor. 7:1) Bugu da ƙari, tun da yake “mai-aikin fasikanci yana yi wa jiki nasa zunubi,” kowane irin lalata yana sa hadayarsa ta ɓata wa Jehobah rai. (1 Kor. 6:18) Don ya faranta wa Allah rai, dole ne mutum ya ‘zama mai-tsarki cikin dukan tasarrufinsa.’—1 Bit. 1:14-16.
13. Me ya sa ya dace mu yabi Jehobah?
13 Wata hadaya da Jehobah yake farin ciki da ita ta ƙunshi furcinmu. Waɗanda suke ƙaunar Jehobah a ko da yaushe suna magana mai kyau game da shi a fili da kuma sa’ad da suke su kaɗai a gidajensu. (Karanta Zabura 34:1-3.) Ka karanta Zabura 148 zuwa 150, kuma ka lura yawan yadda waɗannan zabura uku suka ƙarfafa mu mu yabi Jehobah. Hakika, “yabo ya dace ga masu-gaskiya.” (Zab. 33:1) Kuma wanda muke bin misalinsa, Yesu Kristi ya nanata muhimmancin yabon Allah ta wajen wa’azin bishara.—Luk 4:18, 43, 44.
14, 15. Hosiya ya aririce Isra’ilawa su miƙa waɗanne irin hadayu, kuma wace amsa ce Jehobah ya ba da?
14 Ta yin wa’azi da ƙwazo, muna nuna cewa muna ƙaunar Jehobah kuma muna son amincewarsa. Alal misali, ka yi la’akari da yadda annabi Hosiya ya gargaɗi Isra’ilawa da suka soma bautar ƙarya kuma sun yi rashin amincewar Allah. (Hos. 13:1-3) Hosiya ya gaya musu su yi roƙo: “[Jehobah] ka kawasda dukan saɓo, ka karɓi abin da ke nagari; da haka nan za mu kawo hadayun leɓunanmu misalin bajimai.”—Hos. 14:1, 2.
15 Bijimi dabba ce da ta fi tsada da Ba’isra’ila zai iya miƙa ga Jehobah. Amma, “leɓunanmu misalin bajimai,” yana nuni ga kalamai da muka yin tunaninsu da kyau kafin mu furta su da suke yabon Allah na gaskiya. Mene ne Jehobah ya faɗa ga waɗanda suke miƙa irin waɗannan hadayu? Ya ce: “Zan ƙaunace su a yalwace.” (Hos. 14:4) Jehobah yana gafarta wa waɗanda suke miƙa irin waɗannan hadayu na yabo, suna samun amincewarsa, da kuma abotarsa.
16, 17. Sa’ad da bangaskiya ga Allah ta motsa mutum ya yi wa’azin bishara, yaya Jehobah yake amincewa da yabon wannan mutum?
16 Yabon Jehobah a fili a ko da yaushe sashe ne mai muhimmanci a bauta ta gaskiya. Ɗaukaka Allah na gaskiya yana da muhimmanci ga mai zabura da har ya roƙi Allah: “Ina roƙonka, ka karɓi hadayu na yardan rai daga bakina, ya Ubangiji.” (Zab. 119:108) Yau kuma fa? Da yake magana game da taro mai girma a zamaninmu, Ishaya ya yi annabci: “Za su kawo bisharar yabon Ubangiji. . . . Za su kawo [kyautarsu] bisa kan bagadin [Allah].” (Isha. 60:6, 7) Wannan ya samu cikawa don mutane miliyoyi suna miƙa “hadaya ta yabo ga Allah kullayaumi, watau, ’ya’yan leɓunan da su ke shaida sunansa.”—Ibran. 13:15.
17 Kai kuma fa? Kana miƙa wa Allah hadayu da zai amince da su? Idan ba haka ba, za ka iya yin canje-canje da ake bukata kuma ka soma yabon Jehobah a fili? Sa’ad da bangaskiya ta motsa ka ka soma yin wa’azin bishara, hadayarka za ta “kuwa gami Ubangiji gaba da bajimi.” (Karanta Zabura 69:30, 31.) Ka kasance da tabbaci cewa “Shesheƙi mai-ƙamshi” na hadayarka na yabo zai kai wurin Jehobah kuma zai ba ka amincewarsa. (Ezek. 20:41) Sa’annan za ka yi farin ciki da babu kamarsa.
‘Jehobah Zai Albarkaci Kowanne Mai Adalci’
18, 19. (a) Yaya mutane da yawa a yau suke ɗaukan bauta wa Allah? (b) Rashin amincewar Allah yana kai ga mene ne?
18 A yau mutane da yawa suna kammalawa yadda wasu suka yi a zamanin Malakai: “Banza ne a bauta ma Allah; me ne amfaninsa a garemu kuwa da muka kiyaye umurninsa.” (Mal. 3:14) Da yake suna sha’awar abin duniya, suna ganin cewa ba za a iya yin nufin Allah ba kuma bin dokokinsa tsohon yayi ne. A gare su, wa’azin bishara ɓata lokaci ne kuma yana ɓata wa mutane rai.
19 Irin wannan halin ya soma a lambun Adnin. Shaiɗan ne ya rinjayi Hauwa’u ta rena amfanin rai mai ban al’ajabi da Jehobah ya ba ta kuma ta ƙi amincewarsa. A yau, Shaiɗan a kai a kai yana rinjayar mutane su gaskata cewa ba za a samu kowacce riba ba ta wurin yin nufin Allah. Amma, Hauwa’u da mijinta sun gano cewa rashin amincewar Allah yana nufin rashin rayuwarsu. Ba da daɗewa ba, waɗanda suka bi mugun misalinsu za su gane cewa rashin amincewar Allah zai sa su rasa ransu.—Far. 3:1-7, 17-19.
20, 21. (a) Mene ne gwauruwa a Zarefat ta yi, kuma wane sakamako ne ta samu? (b) Ta yaya za mu yi koyi da gwauruwar Zarefat kuma me ya sa?
20 Ka yi tunanin bambanci mugun sakamakon abin da Adamu da Hauwa’u suka yi da sakamakon abubuwa da aka ambata ɗazu game da Iliya da gwauruwa a Zarefat. Bayan da ta ji kalaman ƙarfafawa na Iliya, matar ta soma dafa abinci kuma ta fara ba annabin abincin, ko da yake abincin kaɗan ne. Sai Jehobah ya cika alkawarin da ya yi ta bakin Iliya. Labarin ya ce: “Da shi da ita, da gidanta, suka ci kwanaki da yawa. Tukunyar hatsi ba ta shace ba, tulun mai kuma ba ya sare ba, bisa ga maganar Ubangiji da ya faɗi ta bakin Iliya.”—1 Sar. 17:15, 16.
21 Gwauruwa a Zarefat ta yi abin da mutane kalilan cikin biliyoyi da suke da rai yanzu za su yi. Ta dogara gabaki ɗaya ga Allah mai ceto, kuma ya taimaka mata. Wannan da kuma wasu cikin labaran Littafi Mai Tsarki sun tabbatar mana cewa Jehobah ya cancanci mu dogara a gare shi. (Karanta Joshua 21:43-45; 23:14.) Rayuwar Shaidun Jehobah na zamani ta ba da ƙarin tabbaci cewa ba zai taɓa yasar da waɗanda suke da amincewarsa ba.—Zab. 34:6, 7, 17-19.a
22. Me ya sa yake da gaggawa mu biɗi amincewar Allah babu ɓata lokaci?
22 Ranar hukuncin Allah a kan “dukan mazaunan fuskar duniya,” ta kusa. (Luk 21:34, 35) Ba za su tsira ba. Babu arziki ko kuma abin duniya da zai taɓa kasancewa da amfani kamar jin Alƙalin da Allah ya naɗa yana cewa: “Ku zo, ku masu-albarka na Ubana, ku gaji mulkin da an shirya dominku.” (Mat. 25:34) Hakika, ‘Jehobah da kansa zai albarkaci mai-adalci; da tagomashi zai kewaye su kamar da garkuwa.’ (Zab. 5:12) Shin bai kamata mu biɗi amincewarsa ba?
[Hasiya]
a Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 2005, shafi na 13, sakin layi na 15; 1 ga Agusta, 1997, shafuffuka na 20 zuwa 25, na Turanci.
Ka Tuna?
• Me sa ya Jehobah ya cancanci mu bauta masa da dukan zuciyarmu?
• Waɗanne hadayu ne Jehobah yake amincewa da su a yau?
• Mene ne furcin nan “leɓunanmu misalin bajimai” yake nufi, kuma me ya sa za mu miƙa su ga Jehobah?
• Me ya sa za mu biɗi amincewar Allah?
[Hoton da ke shafi na 13]
Annabin Allah ya gaya wa wata uwa matalauciya ta tsai da wace shawara?
[Hoton da ke shafi na 15]
Wane amfani ne muke samu domin muna miƙa hadayar yabo ga Jehobah?
[Hoton da ke shafi na 17]
Ba za ka taɓa cizon yatsa ba idan ka dogara ga Jehobah sosai