Ka Nuna Halin Da Ya Cancanci Na ’Yan Mulkin!
‘Ka yi irin zaman da ya cancanci bisharar Kristi.’—FILIB. 1:27.
MECE CE AMSARKA?
Su wane ne za su iya zama ’yan Mulkin?
Mene ne muke bukata mu yi game da yare da tarihi da kuma dokokin Mulkin?
Ta yaya ’yan Mulkin suke nuna cewa suna ƙaunar ƙa’idodin Allah?
1, 2. Ta yaya kalmomin Bulus ga ikilisiyar da ke Filibi suke da ma’ana ta musamman?
MANZO BULUS ya ƙarfafa ikilisiyar da ke Filibi su yi “irin zaman da ya cancanci bisharar Kristi.” (Karanta Filibiyawa 1:27.) Furucin nan “ku yi irin zaman da ya cancanci bisharar,” a yare na asali yana nufin cewa idan mutum yana son ya zama ɗan ƙasa yana bukatar ya yi aiki gadan-gadan. Waɗannan kalmomin suna da muhimmanci ga ikilisiyar da ke Filibi. Me ya sa? Kamar dai Filibi yana ɗaya daga cikin biranen da mazaunansu suke da ’yancin ’yan ƙasar Roma. ’Yan Filibi suna alfahari cewa suna da ’yancin ’yan ƙasar Roma domin suna morar abubuwan da ake tanadar wa waɗanda ke da wannan matsayin.
2 ’Yan ikilisiyar Filibi suna da dalilin yin alfaharin zama ’yan ƙasar Roma, amma suna da wani dalilin yin alfaharin da ya fi wannan muhimmanci. Bulus ya tuna masu cewa su ’yan Mulkin “sama” ne. (Filib. 3:20) Su ba mazaunan wata ƙasa ba ne, amma mazaunan Mulkin Allah ne. Saboda haka, suna morar kāriya da amfani da babu irin su.—Afis. 2:19-22.
3. (a) Su wane ne suke da gatan zama ’yan Mulkin Allah? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?
3 Kalmomin Bulus game da yin “zaman da ya cancanci bisharar Kristi” shawara ce ga shafaffu waɗanda suke da begen yin sarauta tare da Kristi a sama. (Filib. 3:20) Amma, kuma shawarar ta shafi waɗanda za su zama talakawa a duniya a ƙarƙashin Mulkin Allah. Me ya sa? Domin dukanmu muna bauta wa Sarki guda ne, wato Jehobah, kuma ƙa’idodin da muke bi iri ɗaya ne. (Afis. 4:4-6) A yau, mutane suna aiki tuƙuru don su samu ’yancin zama a wata ƙasa mai arziki. Zarafin zama ’yan Mulkin ya fi kome tamani! Don mu ƙara fahimtar wannan babban gatan, bari mu kwatanta abubuwan da ake bukata don samun ’yancin zama ɗan wata ƙasa da kuma zama ɗan Mulkin. Bayan haka, za mu tattauna abubuwa guda uku da suka wajaba mu yi idan muna son mu ci gaba da zama ’yan Mulkin.
ABUBUWAN DA ZA MU YI DON MU CANCANCI ZAMA ’YAN MULKIN
4. Mene ne harshe mai tsarki, kuma ta yaya muke “magana” da harshen?
4 Ka koyi yaren. Wasu gwamnatoci sun ce ya wajaba mutanen da suke son su zama ’yan ƙasarsu su koyi yaren da aka fi yi a ƙasar. Wajibi ne wasu su yi ƙoƙari sosai don su iya yaren bayan an ba su ’yancin zama ’yan ƙasa. Ba da daɗewa ba, za su koyi ƙa’idodin nahawu na yaren amma zai ɗauki lokaci kafin su ƙware a yin yaren. Hakazalika, ana bukatar ’yan Mulkin Allah su koyi yare da Littafi Mai Tsarki ya kira “harshe mai-tsarki.” (Karanta Zafaniya 3:9.) Mene ne wannan harshe mai tsarki? Koyarwar gaskiya ce game da Allah da kuma nufinsa da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Muna “magana” da harshe mai tsarki sa’ad da rayuwarmu ta jitu da dokoki da kuma ƙa’idodin Allah. ’Yan Mulkin Allah suna iya koyon ainihin koyarwar Littafi Mai Tsarki ba tare da ɓata lokaci ba kuma su yi baftisma. Duk da haka, suna bukata su ci gaba da koyon harshen don su iya “magana” da shi sosai. Ta yaya? Muna bukata mu riƙa ƙoƙarin yin rayuwa da ta jitu da abin da muke koyo daga Littafi Mai Tsarki.
5. Me ya sa ya kamata mu yi nazarin tarihin ƙungiyar Jehobah da ke duniya?
5 Ka koyi tarihin. Wasu gwamnatocin ’yan Adam suna bukatar masu son zama ’yan ƙasarsu su koyi wani abu game da tarihin ƙasarsu. Hakazalika, waɗanda suke so su zama ’yan Mulkin suna bukata su koyi duk wani abin da ya kamata su sani game da Mulkin Allah. ’Ya’yan Kora da suka yi hidima a Isra’ila ta dā sun kafa mana misali mai kyau. Sun yi sha’awar Urushalima da wurin da ake bauta kuma sun yi marmarin yin magana game da tarihinta. Ba don kyaunta ba amma don abin da birnin da wurin bautarsa suke wakilta. Urushalima “birnin Maɗaukakin Sarki” Jehobah ne kuma cibiyar bauta ta gaskiya ce. A nan ne mutane suke koyon Dokokin Jehobah. Kuma Jehobah ya nuna ƙaunarsa da yardarsa ga mutanen da ke zaune a cikinta. (Karanta Zabura 48:1, 2, 9, 12, 13.) Kana sha’awar yin nazarin tarihin ƙungiyar Jehobah da ke duniya, kamar yadda ’ya’yan Kora suka yi? Yayin da kake ƙara yin nazari game da ƙungiyar Allah da kuma yadda Jehobah yake taimakon mutanensa, Mulkin Allah zai ƙara kasancewa da tabbaci a gare ka. Za ka ƙara sha’awar yin wa’azi game da Mulkin Allah.—Irm. 9:24; Luk 4:43.
6. Me ya sa ya dace Jehobah ya bukace mu mu koyi kuma mu yi biyayya ga dokoki da ƙa’idodin Mulkin?
6 Ka san dokokin. Wajibi ne ’yan ƙasa su koyi kuma su yi biyayya ga dokokin ƙasarsu. Hakazalika, muna bukatar mu koyi kuma mu bi dokoki da ƙa’idodin Mulkin Allah. (Isha. 2:3; Yoh. 15:10; 1 Yoh. 5:3) Dokokin ’yan Adam suna da aibi kuma wani lokaci da rashin adalci. Akasin haka, “shari’a ta Ubangiji cikakkiya ce.” (Zab. 19:7) Kana jin daɗin karanta da kuma koyon dokoki da kuma ƙa’idodin da ke Kalmar Allah kowace rana? (Zab. 1:1, 2) Kowannenmu na bukatar ya yi yunƙurin nazarin dokokin Allah.
’YAN MULKIN SUNA ƘAUNAR ƘA’IDODIN ALLAH
7. Me ya sa ’yan Mulkin suke bin dokokin Allah?
7 Idan muna son mu ci gaba da kasancewa ’yan Mulkin, wajibi ne mu san kuma mu ƙaunaci ƙa’idodin Allah. Mutane da yawa suna da’awar cewa suna bin dokoki da ƙa’idodin ƙasarsu. Amma, sa’ad da suka ga cewa kiyaye wata doka tana da wuya kuma babu wanda yake kallonsu, sai su karya dokar. Hakan ya nuna cewa waɗannan “masu son faranta wa mutane rai” ne. (Kol. 3:22, Littafi Mai Tsarki) ’Yan Mulkin suna bin ƙa’idodi da suka ɗara na ’yan Adam. Muna farin cikin bin dokokin Allah, ko da babu wanda yake kallonmu. Me ya sa? Domin muna ƙaunar Mai ba da dokar.—Isha. 33:22; karanta Luka 10:27.
8, 9. Ta yaya za ka san cewa kana ƙaunar dokokin Allah da gaske?
8 Ta yaya za ka san cewa kana ƙaunar dokokin Allah? Sa’ad da aka ba ka shawara game da abin da kake gani babu takamaiman doka a kai, alal misali saka tufafi da yin ado. Kafin ka zama ɗan Mulkin, wataƙila ba ka damuwa da yadda kake yin ado ko kuma kana saka tufafin da ke nuna rashin ɗa’a. Amma, yayin da ƙaunarka ga Jehobah take ƙaruwa, sai ka fara saka tufafin da zai faranta masa rai. (1 Tim. 2:9, 10; 1 Bit. 3:3, 4) Za ka iya ɗauka cewa yanzu kana saka tufafi bisa ƙa’ida. Amma, idan wani dattijo ya gaya maka cewa tufafin da kake sakawa yana ɓata wa wasu masu shela rai kuma fa? Me za ka yi? Za ka fara ba da hujja ko kuma ka ji haushi ko kuwa za ka yi masa kunnen uwar shegu ne? Wata muhimmiyar doka ta Mulkin Allah ita ce duk ’yan Mulkin su yi koyi da Kristi. (1 Bit. 2:21) Sa’ad da Bulus yake rubutu game da misalin Kristi, ya ce: “Bari kowanen mu ya gami ɗan’uwansa wajen abin da ke nagari, zuwa ginawa. Gama Kristi kuma bai yi son kai ba.” (Rom. 15:2, 3) Don a samu zaman lafiya a cikin ikilisiya, Kirista mai ƙaunar Jehobah ba zai ji haushi ba kuma zai yi gyara don ya daina ɓata wa mutane rai.—Rom. 14:19-21.
9 Ka yi la’akari da wasu batutuwa guda biyu masu muhimmanci: yadda muka ɗauki jima’i da kuma aure. Waɗanda ba ’yan Mulkin ba za su iya amincewa da luwaɗi kuma su yi tunanin cewa kallon hotuna batsa da kuma yin zina da kashe aure ba laifi ba ne. Ko da yake wasu da suka zama ’yan Mulkin sun taɓa yin lalata a dā. Amma, yanzu sun san cewa jima’i da aure kyauta ne daga Allah kuma waɗanda suke yin lalata ba za su ci gaba da zama ’yan Mulkin ba. (1 Kor. 6:9-11) Bugu da ƙari, sun san cewa zuciya da ha’inci take. (Irm. 17:9) Saboda haka, suna godiya cewa ana ba su takamammun gargaɗi da ke taimaka musu su ci gaba da yin biyayya ga dokokin Allah.
’YAN MULKIN SUNA SAURARAR GARGAƊI
10, 11. Waɗanne gargaɗi ne Mulkin Allah yake ba da wa, kuma yaya ka ɗauki irin waɗannan gargaɗin?
10 Gwamnatocin ’yan Adam sukan ba da gargaɗi game da abinci da kuma magunguna. Ko da yake, ba dukan abinci da magunguna ba ne suke da lahani. Amma, idan wani abinci ko magani na da lahani, gwamnati tana iya ba da gargaɗi game da hakan don kāre talakawanta. Hakazalika, Mulkin Allah yana tanadar da takamammun gargaɗi game da tarbiyya da kuma dangantakarmu da Jehobah. Alal misali, mutane da yawa suna amfani da intane wajen sadarwa da neman ilimi da kuma nishaɗi. Ƙungiyar Allah tana amfani da intane kuma tana cim ma abubuwa masu kyau da shi. Amma, dandali masu yawa na intane suna da haɗari sosai kuma za su iya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Dandalin da suke yaɗa hotunan batsa suna da haɗari sosai ga ’yan Mulkin. Shekaru da yawa yanzu, bawan nan mai aminci ya sha ba da gargaɗi game da irin waɗannan dandalin. Muna godiya sosai saboda waɗannan gargaɗin!
11 A shekarun baya bayan nan, wani dandali ya fito kuma ya zama gama gari sosai, dandalin yana da amfani amma yana da haɗari har ila. Wannan shi ne dandalin hira a intane. Zai iya sa mu yin tarayya da mugayen mutane. (1 Kor. 15:33) Shi ya sa ƙungiyar Jehobah tana ba da gargaɗin da ya dace game da irin wannan dandalin. Ka karanta dukan talifofin da bawan nan mai aminci ya wallafa game da amfani da irin wannan dandalin? Zai zama da haɗari sosai idan muka ƙi karanta waɗannan talifofin kafin mu fara amfani da irin wannan dandalin!a Yin hakan yana kamar shan wani magani mai ƙarfi sosai ba tare da karanta umurni da ke jikin kwalabar ba.
12. Me ya sa yin watsi da gargaɗi ba basira ba ce?
12 Tabbas ne cewa waɗanda suke watsi da gargaɗin da bawan nan mai aminci yake bayarwa suna jawo wa kansu da ƙaunatattunsu lahani. Wasu sun shaƙu da kallon hotunan batsa ko kuma sun yi lalata kuma suna tunanin cewa Jehobah ba ya ganin abubuwan da suke yi. Idan muna tunani cewa za mu iya ɓoye wa Jehobah halinmu muna ruɗin kanmu ne! (Mis. 15:3; karanta Ibraniyawa 4:13.) Allah yana so ya taimaki irin waɗannan mutane kuma yana amfani da wakilansa da ke duniya wajen yin haka. (Gal. 6:1) Amma, Jehobah zai hana waɗanda suka ci gaba da karya dokokinsa zama ’yan Mulkin kamar yadda gwamnatocin ’yan Adam sukan soke wani daga zama ɗan ƙasa sa’ad da ya karya wasu dokoki.b (1 Kor. 5:11-13) Duk da haka, Jehobah mai jin ƙai ne. Waɗanda suka tuba kuma suka canja halinsu za su sake morar dangantaka da Jehobah kuma su ci gaba da zama ’yan Mulkin. (2 Kor. 2:5-8) Babban gata ne cewa muna bauta wa Jehobah, Sarki mai ƙauna!
’YAN MULKIN SUNA SON SAMUN ILIMI
13. Ta yaya ’yan Mulkin suke nuna cewa suna daraja ilimi?
13 Gwamnatocin ’yan Adam da yawa suna ƙoƙari su ilimantar da ’yan ƙasarsu. Suna tsara makarantu da ke koyar da karatu da sana’o’i. ’Yan Mulkin suna amfana daga waɗannan makarantun. Amma, sun fi ba da muhimmanci ga ilimin da suke samu a matsayin ’yan Mulkin. Ta wajen ikilisiyar Kirista, Jehobah yana tanadar da ilimi. Ana kuma ƙarfafa iyaye su riƙa yi wa yaransu karatu. Bawan nan mai aminci yana buga batutuwa da yawa da ke bisa Littafi Mai Tsarki a cikin Hasumiyar Tsaro a harshen Hausa kowace wata. Idan kana karanta wasu shafofi a rana, za ka ci gaba da amfana daga koyarwa da Jehobah ke tanadarwa.
14. (a) Waɗanne koyarwa muke samu? (b) Waɗanne shawarwari game da Bauta ta Iyali ne kake amfani da su?
14 ’Yan Mulkin suna samun koyarwa a taron da suke yi a ikilisiyoyi a kowane mako. Alal misali, fiye da shekaru 60 yanzu, Makarantar Hidima Ta Allah tana taimaka wa ɗaliban su ƙware a koyar da Littafi Mai Tsarki. Kai ɗalibin wannan makarantar ne? A shekaru baya bayan nan, bawan nan mai aminci ya mai da hankali sosai ga ƙarfafa Bauta ta Iyali da yamma. Wannan shirin yana sa waɗanda ke cikin iyali su ƙara kasancewa da haɗin kai. Kana amfani da shawarwarin da ke cikin littattafanmu game da wannan shirin?c
15. Wane babban gata ne muke da shi?
15 ’Yan ƙasa na gwamnatocin ’yan Adam suna yunƙurin neman sa mutane su goyi bayan wata jam’iyyar siyasa, har ma suna bin gida-gida don cim ma wannan burin. A dukan duniya, ’yan Mulkin suna ƙwazo wajen nuna cewa suna goyon bayan Mulkin Allah ta yin wa’azi gida-gida. Kamar yadda aka ambata a talifi na baya, Hasumiyar Tsaro, wadda ke shelar Mulkin Jehobah, ita ce mujallar da aka fi rarrabawa a dukan duniya! Gaya wa mutane game da Mulkin Allah babban gata ne sosai a gare mu. Kana yin wa’azin bishara da ƙwazo kuwa?—Mat. 28:19, 20.
16. Ta yaya za ka nuna cewa kai ɗan Mulkin Allah ne nagari?
16 Ba da daɗewa ba, Mulkin Allah ne kaɗai zai yi sarauta bisa duniya. Zai kula da dukan harkokinmu na yau da kullum waɗanda suka shafi bautarmu da ayyukanmu. Za ka so ka zama nagari ɗan Mulki a lokacin? Yanzu ne lokacin nuna cewa za ka so ka yi hakan. A dukan abubuwan da kake yi kowace rana, ka riƙa yin kome domin girmama Allah kuma ta hakan za ka nuna cewa kana yin abubuwan da suka cancanci na ’yan Mulkin Allah.—1 Kor. 10:31.
[Hasiya]
a Alal misali, ka duba Awake! na Yuli 2011, shafuffuka na 24-27 da Agusta na 2011, shafuffuka na 10-13 da kuma na Fabrairu 2012, shafuffuka na 3-9.
b Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 2012, shafuffuka na 30-31.
c Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta 2011, shafuffuka na 6-7 da kuma Hidimarmu Ta Mulki ta Janairu 2011, shafuffuka na 3-6.
[Bayanin da ke shafi na 14]
Kana bin gargaɗin da ke bisa Littafi Mai Tsarki game da Intane kuwa?
[Hoto a shafi na 12]
Kana sha’awar bauta ta gaskiya da kuma tarihinta kamar ’ya’yan Kora?
[Hoto a shafi na 15]
Bauta ta Iyali da yamma za ta iya taimaka maka da iyalinka ku zama ’yan Mulki masu kirki