ABIN DA KE SHAFIN FARKO: ABIN DA MUKA KOYA DAGA MUSA
Wane Ne Musa?
Me yake zuwa zuciyarka sa’ad da aka ambaci sunan nan Musa? Kana tunanin:
wani jaririn da mahaifiyarsa ta saka a cikin kwando kuma ta ɓoye shi a kogin Nilu?
yaron da ’yar Fir’auna ta yi rainonsa cikin annashuwa amma bai manta cewa shi ɗan Isra’ila ne ba?
mutumin da ya yi shekara 40 a ƙasar Midian a matsayin makiyayi?
mutumin da ya yi magana da Jehobaha kusa da kurmi mai cin wuta?
mutumin da ya je wurin sarkin Masar kuma ya gaya masa da gaba gaɗi cewa ya ’yantar da Isra’ilawa?
mutumin da Allah ya umurce shi ya sanar da aukuwar Annoba Goma bisa ƙasar Masar bayan sarkin ya ƙi bin umurnin Allah na gaskiya?
mutumin da ya ja-goranci Isra’ilawa sa’ad da suke fitowa daga Masar?
mutumin da Allah ya yi amfani da shi don ya raba Jan Teku?
mutumin da Allah ya ba shi Dokoki Goma don ya ba wa Isra’ilawa?
MUSA ya yi dukan waɗannan abubuwan da aka ambata har ma fiye da haka. Shi ya sa Kiristoci da Yahudawa da kuma Musulmai suna girmama shi sosai!
Hakika, Musa annabi ne da ya aikata abubuwa masu “ban razana mai-girma.” (Kubawar Shari’a 34:10-12) Ya yarda Allah ya yi amfani da shi a hanya mai girma. Amma shi mutum ne kamar mu. Kamar annabi Iliya da ya bayyana a gefen Musa cikin wahayi a lokacin da Yesu yake duniya, Musa mutum ne mai “tabi’a kamar tamu.” (Yaƙub 5:17; Matta 17:1-9) Musa ya fuskanci irin ƙalubale da muke fuskanta a yau, kuma ya sha kansu.
Za ka so ka san yadda ya yi hakan? Bari mu tattauna halaye masu kyau guda uku da Musa ya nuna da kuma abin da za mu iya koya daga misalin da ya kafa.
a Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.