AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI
Mene ne Kristi zai dawo yi?
Kafin Yesu Kristi ya koma sama a shekara ta 33 kafin zamaninmu, ya yi alkawari cewa zai dawo. Ya kamanta kansa da wani basaraki da ya yi tafiya na dogon lokaci sa’an nan ya dawo a matsayin sarki. Yesu zai dawo domin ya yi sarauta bisa ’yan Adam a hanyar da ta dace.—Karanta Luka 19:11, 12.
Yesu zai sarauci ’yan Adam a hanya mai kyau
A matsayin wane irin halitta ne ya kamata Kristi ya dawo? An ta da shi daga mutuwa a matsayin halittar ruhu marar ganuwa. (1 Bitrus 3:18) Sa’an nan ya koma sama don ya zauna a hannun dama na Allah. (Zabura 110:1) Shekaru da yawa bayan haka, aka kawo Yesu gaban “Mai Zamanin Dā,” wanda ya ba Yesu ikon yin sarauta bisa ’yan Adam. Saboda haka, Yesu ba zai dawo a matsayin ɗan Adam ba, amma a matsayin Sarki da ba a ganinsa.—Karanta Daniyel 7:13, 14.
Mene ne Yesu zai yi sa’ad da ya dawo?
A lokacin da Yesu zai dawo tare da mala’ikunsa, zai shari’anta mutane, amma mutane ba za su gan su ba. Zai halaka miyagu, amma zai sa waɗanda suka amince da shi a matsayin Sarki su rayu har abada.—Karanta Matta 25:31-33, 46.
Sarautar Yesu za ta mai da duniya aljanna. Zai ta da matattu domin su ji daɗin yin rayuwa a cikin duniya da ta zama Aljanna.—Karanta Zabura 37:29; Yohanna 11:25.