AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI
Mene ne Yesu zai yi a nan gaba?
A shekara ta 33 a zamaninmu, Yesu ya mutu, bayan haka ya tashi daga mutuwa kuma ya koma sama. Daga baya can sai aka naɗa shi Sarki. (Daniyel 7:13, 14) A nan gaba, Yesu zai ɗauki mataki a matsayin Sarki don ya kawo zaman lafiya a duniya kuma ya kawar da talauci.—Karanta Zabura 72:7, 8, 13.
A matsayin Sarkin ’yan Adam, Yesu zai yi abubuwa masu ban mamaki sosai. Zai yi amfani da ikon da Ubansa ya ba shi don ya mai da ’yan Adam kamilai. Za su ji daɗin zama a duniya kuma ba za su tsufa ko su mutu ba.—Karanta Yohanna 5:26-29; 1 Korintiyawa 15:25, 26.
Mene ne Yesu yake yi yanzu?
A yanzu haka, Yesu yana yi wa mabiyansa na gaskiya ja-gora yayin da suke yin wa’azi a faɗin duniya. Suna ziyartar mutane don su nuna musu abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da Mulkin Allah. Yesu ya ce zai ci gaba da tallafa wa almajiransa har sai wannan Mulkin ya kawar da sarautar ’yan Adam.—Karanta Matta 24:14; 28:19, 20.
Ta wajen ikilisiyar Kiristoci na gaskiya, Yesu yana ja-gorar mutane zuwa hanyar rayuwa mafi kyau. Zai ci gaba da yi musu ja-gora har bayan halakar wannan duniya don su zauna a cikin sabuwar duniya da ya yi alkawarinta.—Karanta 2 Bitrus 3:7, 13; Ru’ya ta Yohanna 7:17.