Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 9/1 pp. 4-10
  • Idanun Allah Suna Kanka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Idanun Allah Suna Kanka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Koyi da Jehobah a Sha’aninka da ’Yan’uwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Ka Bi Umurnin Allah A Dukan Abu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • ‘Misali’ da Ke da Ma’ana a Gare Mu
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Sun Haifi Da!
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 9/1 pp. 4-10

Idanun Allah Suna Kanka

‘Gama idanunsa suna duban tafarkun mutane, Yana kuwa ganin dukan hanyoyinsu.’—AYUBA 34:21.

ABIN DA KE SA WASU SHAKKA: Wani binciken da aka yi kwanan nan ya nuna cewa damin taurarin da ke ɗauke da duniyarmu yana da aƙalla taurari biliyan ɗari. Saboda girmar samaniya da abubuwan da ta ƙunsa, mutane suna yin tambayar nan cewa, ‘Me ya sa Mahalicci mai iko duka zai mai da hankali ga ayyukan mutane da ba su isa kome ba a cikin wannan mitsitsin duniya?’

ABIN DA KALMAR ALLAH TA CE: Allah bai ba mu Littafi Mai Tsarki kawai sa’an nan ya fita sha’aninmu ba. Akasin haka, Jehobah ya ba mu tabbaci cewa: “Da idona a kanka zan ba ka shawara.”—Zabura 32:8.

Ka yi la’akari da misalin wata ’yar ƙasar Masar mai suna Hajaratu. Ta rayu ne a ƙarni na 20 kafin zamaninmu. Saraya uwargijiyarta ta wulaƙantar da ita don ta yi mata rashin hankali, sai Hajaratu ta gudu zuwa cikin jeji. Shin Allah ya fita sha’anin Hajaratu ne don kuskuren da ta yi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mala’ikan Ubangiji ya iske ta.” Wannan mala’ikan ya ƙarfafa Hajaratu da cewa: “Ubangiji ya ga ƙuncinki.” Sai Hajaratu ta ce ma Jehobah: “Kai Allah mai-gani ne.”—Farawa 16:4-13.

Hakazalika, idanun “Allah mai-gani” suna kanka. Alal misali, mahaifiya mai ƙauna tana lura da ƙananan yaranta sosai, domin irin kulawar da iyaye suke ba yara ya dangana ga shekarunsu. Hakanan ma, Allah yana kula da mu sosai, musamman ma a lokacin da muka karaya ko kuma muke cikin haɗari. Jehobah ya ce: “Ina zaune a wuri maɗaukaki mai-tsarki, tare da shi wanda ya ke da karyayyen ruhu mai-tawali’u, domin in wartsakar da ruhun masu-tawali’u, in wartsakar da masu-karyayyen zuciya.”—Ishaya 57:15.

Duk da haka, kana iya yin tunani: A wace hanya ce idanun Allah suke kaina? Yana kimanta ni bisa ga siffata ne, ko kuma yana kallon zuciyata don ya san ko wane irin mutumi ne ni?’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba