Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 11/1 p. 3
  • Me Ya Sa Zai Dace Ka San Game da Mulkin Allah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Zai Dace Ka San Game da Mulkin Allah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Makamantan Littattafai
  • “Mulkinka Shi Zo”​—Addu’ar Da Miliyoyin Mutane Suke Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Abin da Yesu Ya Koyar Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Fada Game da Mulkin Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
  • Mene ne Mulkin Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2020
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 11/1 p. 3

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | MULKIN ALLAH—TA YAYA ZAI AMFANE KA?

Me Ya Sa Zai Dace Ka San Game da Mulkin Allah?

Miliyoyin mutane a faɗin duniya suna dogara da Mulkin Allah. Suna bin gurbin Yesu, wanda ya koya wa almajiransa su yi addu’a, suna cewa: ‘Mulkinka ya zo. Abin da kake so, a yi shi, cikin duniya.’—Matta 6:10.

Abin mamaki, duk da cewa mutane da yawa suna sha’awar Mulkin Allah, yawancin addinai suna banza da shi. Wani ɗan tarihi mai suna H. G. Wells ya ce duk da yadda Yesu ya ba da “fifiko . . . ga koyarwar abin da ya kira Mulkin Sama,” wannan koyarwar “ba ta da wani muhimmanci ga . . . yawancin cocin Kiristoci.”

Akasin waɗannan coci-cocin, Shaidun Jehobah suna ɗaukan Mulkin Allah da muhimmanci sosai. Ka yi la’akari da wannan: Ana buga wannan mujallar da kake karantawa, wadda ita ce mujallarmu ta musamman, a harsuna 220. A kowace fitowarta, ana buga kwafi kusan miliyan 46, shi ya sa ta zama mujallar da aka fi rarrabawa a duniya. Amma, mene ne ainihin saƙon wannan mujallar? Ka lura cewa jigonta shi ne: Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah.a

Me ya sa Shaidun Jehobah suke iyakacin ƙoƙarinsu su sanar ko kuma su yi shelar Mulkin Allah haka? Wani dalilin shi ne, mun gaskata cewa Mulkin Allah ne ainihin batun da littafi mafi muhimmanci a duniya ya fi yin bayani a kai. Wannan littafin shi ne Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, mun tabbata cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance matsalolin ’yan Adam.

Misalin Yesu ne Shaidun Jehobah suke bi yayin da suke ƙoƙarin jawo hankalin mutane ga Mulkin Allah. A lokacin da Yesu yake duniya, Mulkin Allah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa kuma shi ne Yesu ya fi yin wa’azinsa. (Luka 4:43) Me ya sa Yesu ya ɗauki Mulkin da muhimmanci sosai? Ta yaya Mulkin zai amfane ka? Don Allah ka bincika amsoshin da Littafi Mai Tsarki ya bayar a kan waɗannan tambayoyin a talifofin da ke biye.

a Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah ne sunan Allah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba