Za Mu Sake Yin Nazarin Littafin Nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
1. (a) Wane littafi ne ya kasance mai amfani sosai idan ya zo ga yin nazarin Littafi Mai Tsarki da masu son gaskiya? (b) Me ya sa za mu sake yin nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
1 Mun daɗe muna yin amfani sosai da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? a hidimarmu, musamman sa’ad da muke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane a gidajensu. Don a taimaka wa dukan waɗanda suke cikin ikilisiya su san wannan littafin sosai, za mu sake yin nazarinsa a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya wanda za a soma a makon 1 ga Maris, 2010.
2. (a) Ta yaya za a iya yin nazari a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya ta wajen yin amfani da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? (b) Kuma me ya sa zai kasance abin daɗi a yi kalami sa’ad da ake nazarin wannan littafin?
2 Dattijon da ke gabatar da Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya a makon, zai jawo hankalin mutane zuwa ga tambayoyin da ke farkon kowane babi. Bayan haka za a gabatar da nazarin ta wajen yin amfani da tambayoyin da ke ƙarƙashin shafin. Za a karanta da kuma tattauna nassosin da suka tallafa wa ainihin batutuwan, kuma akwatin nan “Abin da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa” da ke ƙarshen kowane babi zai taimaka wajen sake bincika batun domin akwatin yana ɗauke da amsoshin daga Nassosi ga tambayoyin da ke gabatarwa na babin. Za ku ji daɗin yin kalami, domin littafin ya tattauna batutuwan ne a hanyoyi masu sauƙi, dalla-dalla, kuma masu ban sha’ayi.
3. (a) Wane abu da ke cikin littafin nan ne za mu so sosai? (b) A wace hanya ce za a iya tattauna batutuwan da ke cikin hasiyar?
3 Hasiyar da ke wannan littafin ya ba da cikakkun bayanai a kan batutuwa dabam-dabam. A wasu lokatai za a tattauna hasiyar a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. Ɗan’uwan da aka ce ya yi karatu a wannan makon ne zai karanta dukan bayanan da ke hasiyar, kuma za a iya raba talifofi masu tsawo. Hasiyar ba ta da tambayoyi na nazari. Amma dattijon da ke gabatar da Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya a wannan makon zai iya sa masu sauraro su yi kalamai ta wajen yin tambayoyin da za su fito da ainihin bayanan.
4. Menene kowannenmu za mu yi don mu amfana sosai daga nazarin littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
4 Za a buga tsarin ayyuka na Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa da za a yi nazarinsa a kowane mako a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya a cikin tsarin ayyuka na kowane mako da ke cikin Hidimarmu ta Mulki kamar yadda aka saba. Don ka amfana sosai, kana bukatan ka shirya kowane taro tun da wuri. Bugu da ƙari, ka ƙudurta kasancewa a taro a kowane mako kuma ka saka hannu sosai a nazarin da za mu yi na littafi nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?