Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb16 Nuwamba p. 5
  • Yadda Za a Yi Amfani da Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za a Yi Amfani da Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Taimaka Wa Mutane Su Yi Biyayya Da Abin Da Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Za Mu Sake Yin Nazarin Littafin Nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Ka Yi Amfani da Sassa Dabam-dabam na Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Yadda Ya Dace
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Ku Koyar da Gaskiya
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
mwb16 Nuwamba p. 5

RAYUWAR KIRISTA

Yadda Za a Yi Amfani da Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?

Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?

Littattafan nan Me Za Mu Koya da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? iri ɗaya ne. Muna amfani da dukansu a wa’azi kuma yadda aka tsara su iri ɗaya ne. Amma Me Za Mu Koya yana da sauƙin karatu da kuma fahimta. An wallafa shi don mutanen da ba za su iya fahimtar Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ba. An saka ƙarin bayani a Me Za Mu Koya maimakon rataye. Ƙarin bayanin ya bayyana wasu batutuwa da ke cikin babin a hanyar da za a fahimce su da sauƙi. Babu tambayoyi a farkon babin ko kuma akwatin bita a ƙarshen babin. Amma, an kammala kowane babi da taƙaita wasu muhimman darussan da aka bayyana a babin. Za mu iya ba da littafin Me Za Mu Koya yadda muke ba da Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? ko da ba shi ake rarraba a watan ba. Ta yaya za mu yi amfani da littafin Me Za Mu Koya wajen yin nazari da mutane?

Takaitawar littafin Me Za Mu Koya

TAƘAITAWA: Yawancin mutane za su fi amfana daga yadda muke yin nazari da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, wato yadda muke karanta sakin layi da kuma yin tambaya. Amma idan mutumin ba ya jin yaren sosai ko kuma bai iya karatu ba fa? Ta yaya za a iya taimaka masa? Za a iya yin amfani da littafin nan Me Za Mu Koya. Idan hakan ne, za a iya amfani da taƙaitawar don yin nazarin kuma bayan an gama, a ce wa ɗalibin ya karanta sakin layin a nasa lokaci. Za a iya koyar da kowane darasi cikin minti 15. Da yake taƙaitawar ba ta ɗauke da cikakken bayanai da ke babin, zai dace malamin ya yi la’akari da yanayin ɗalibinsa kuma ya yi shiri da kyau. Amma idan malamin ya yi amfani da sakin layin wajen yin nazarin, zai dace ya yi amfani da taƙaitawar don bita.

Karin bayani da ke littafin Me Za Mu Koya

ƘARIN BAYANAI: An jera kalmomi da kuma batutuwan da ke ƙarin bayanin ɗaya bayan ɗaya yadda yake a babin. Mai gudanar da nazarin zai iya tsai da shawarar tattauna ƙarin bayani da ke littafin Me Za Mu Koya sa’ad da yake nazari.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba