Hali Mai Kyau da Ke Girmama Allah
1. Me ya sa mutane suke saurin sanin cewa muna halartan taron gunduma?
1 A duk lokacin da muke halartan taron gunduma, mutane suna saurin sanin cewa muna taro. A wurare da yawa da ake taron, kafofin yaɗa labarai sukan sanar da mutane a yankin cewa Shaidun Jehobah suna gudanar da taro. A yawancin lokaci, mutane da yawa suna ganin ’yan’uwanmu da yawa sanye da bajojin taron gunduma a hotal da kuma gidajen cin abinci. Ga wasu abubuwa da za su taimaka mana mu nuna hali mai kyau da zai girmama Allah sa’ad da muke halartan taron gunduma.—1 Bit. 2:12.
2. Ta yaya za mu girmama Allah ta wajen sanya tufafi da suka dace a garin da muke taron gunduma?
2 Ado da Tufafi da Suka Dace: Tufafi masu kyau da muke sakawa sa’ad da muke halartan taron sukan burge mutane. Amma irin ado da muka yi sa’ad da muke sauka a masaukinmu ko sa’ad da muke cin abinci a hotal da ke unguwar ko sa’ad da muke sayayya ko kuma yin wani abu dabam, yana da tasiri sosai don zai iya sa mutane su ɗauke mu da mutunci ko kuma su raina mu. Ko da yake a wannan lokacin za mu iya saka tufafi dabam da waɗanda za mu saka domin taron, zai dace mu saka tufafi masu kyau da za su girmama Allah amma ba kaya marasa fasali ba. Zai yi kyau mutane da suke kallon mu su ga bambanci da ke tsakanin mu da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah. (Rom. 12:2) Ƙari ga haka, zai dace mu saka bajojinmu domin hakan zai sa ’yan’uwanmu da suke halartan taron su gane mu, mutane za su san cewa Shaidun Jehobah suna taro kuma hakan zai ba mu damar yin wa’azi.
3. Ta yaya za mu nuna haƙuri da ladabi?
3 Haƙuri da Ladabi: A wannan lokaci da mutane da yawa a duniya sun cika nuna son kai da rashin godiya, mutane kamar ma’aikatan hotal da gidajen abinci za su yi farin ciki idan muka bi da su cikin haƙuri da ladabi. (2 Tim. 3:1-5) Sa’ad da muke kama kujera ko kuma karɓan sababbin littattafan da aka fitar, ya kamata mu kyautata wa mutane kuma kada mu nuna son kai. (1 Kor. 10:23, 24) Wani mutum da ya halarci taron gundumarsa na farko, ya ce, “Ban tuna da jawaban da aka yi a ranar ba, amma hali mai kyau na Shaidun Jehobah da na gani ya burge ni sosai.”
4. Me ya sa ya kamata mu yi tunanin ba da kai don taimakawa a taron gunduma idan yanayinmu zai ba mu damar yin haka?
4 Masu Ba da Kai da Son Rai: Ba da kai hali ne da aka san Kiristoci da shi. (Zab. 110:3) Shin za ka ba da kai don ka taimaka a taron gunduma? A wani taron gunduma, ’yan’uwa wajen 600 sun ba da kai don su tsabtace inda za a yi taron. Wani ma’aikaci a wurin ya ce: “Ban taɓa ganin irin wannan abin al’ajabi ba! Abin mamaki ne cewa duk waɗannan mutanen sun ba da kai da son ransu ne.” Muna marmarin zuwan taron gunduma ta shekara ta 2013 don zai ba mu zarafin koyon abubuwa daga wajen Allah kuma za mu sami damar ɗaukaka sunansa.