Taron Gunduma da Muke Yi Suna Ba da Shaida Mai Kyau Game da Gaskiya
1. Waɗanne muhimman abubuwa ne Isra’ilawa suka samu damar tattaunawa kuma suka yi tunani a kai sa’ad da suka halarci idin shekara-shekara?
1 A kowace shekara, Isra’ilawa na dā suna yin taro sau uku domin idi. Ko da yake dokar ta bukaci mazaje ne kawai su halarci taron, sau da yawa iyalai gaba ɗaya suna yin tafiya zuwa Urushalima don su halarci wannan taron da ke sa farin ciki. (K. Sha 16:15, 16) Waɗannan bukukuwa suna ba Isra’ilawa damar tattauna muhimman batutuwa kuma su yi tunani a kansu. Mene ne waɗannan abubuwan? Na ɗaya, Jehobah mai ƙauna ne kuma yana biya mana bukatunmu a yalwace. (K. Sha 15:4, 5) Na biyu kuma za mu iya dogara ga Allah domin ya yi mana ja-gora kuma ya kāre mu. (K. Sha 32:9, 10) Isra’ilawan suna kuma iya tuna cewa a matsayin mutanen da Jehobah ya kira su shaidunsa, dole ne su yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idodinsa. (K. Sha 7:6, 11) A yau, mu ma muna amfana sosai daga taron gunduma da muke yi a kowace shekara.
2. Ta yaya tsarin taron gunduma mai zuwa zai ƙara bayyana mana Kalmar Allah?
2 Abubuwa da Ake Tattaunawa Suna Bayyana Gaskiya: A taron gunduma da muke yi, muna jin jawabai, muna kallon wasan kwaikwayo da gwaji, muna kuma sauraron ganawa. Dukan abubuwan nan suna taimaka mana mu ƙara fahimtar Kalmar Allah kuma mu yi amfani da ƙa’idodinta a rayuwa. (Yoh. 17:17) A yanzu haka, an riga an yi nisa a shirya abubuwan da za a gudanar a taron gunduma mai zuwa. Ƙungiyar Jehobah tana shirya abubuwan da za su taimaka wa ’yan’uwa da kuma mutane a faɗin duniya su jure ko kuma magance matsalolin da suke fuskanta a yanzu. (Mat. 24:45-47) Shin kuna marmarin morar waɗannan abubuwan da ake shiryawa?
3. Mene ne ya kamata mu yi domin mu amfana daga taron?
3 Hakika, za mu amfana sosai idan mun halarci taron kuma mun kasa kunne sosai a duk ranaku uku na taron. Ku gaya wa shugaban wurin aikinku cewa kuna neman zarafi don halartan taron idan ba ku riga kun yi hakan ba. Ku huta sosai a ƙarshen kowace rana domin ku mai da hankali a lokacin taron. ’Yan’uwa da yawa sun ga cewa kallon mai jawabi da kuma rubuta muhimman bayanai yana taimaka musu su kasa kunne sosai. Kada ku bari wayarku ko peja ta raba hankalinku ko ta dame wasu. Bai dace a riƙa yin surutu ko aika saƙonnin tes ko kuma yin ciye-ciye sa’ad da ake taro ba.
4. Ta yaya iyaye za su taimaka wa ’ya’yansu su amfana a lokacin taron?
4 A shekarun da aka keɓe don Assabaci, sa’ad da Isra’ilawa suka taru don su saurari Dokar Allah a lokacin Idin Bukkoki, suna kawo yaransu ‘ƙanana’ su zauna tare ‘domin su ji, kuma su koyi’ Kalmar Allah. (K. Sha 31:12) Muna yin farin ciki sa’ad da muka ga iyalai suna zaune tare a wurin taro kuma yaransu ƙanana suna mai da hankali sosai don su ji abin da ake faɗa. Don Allah ku sake karanta abin da kuka rubuta kuma ku ɗan tattauna su tare a kowace yamma a ƙarshen taron, idan da hali. Ya kamata iyaye su kula da yaransu ƙanana da matasa a lokacin shakatawa da kuma a masaukinsu maimakon su ‘ƙyale’ su, domin “wauta tana nan ƙunshe a zuciyar yaro.”—Mis. 22:15; 29:15.
5. Ta yaya nuna hali mai kyau a inda muka sauka zai sa mutane su girmama Allah?
5 Hali Mai Kyau Yana Girmama Allah: Hali mai kyau da muke nunawa a garin da ake taron yana girmama Allah. (Tit. 2:10) Mutanen da muka sauka a wurinsu suna jin daɗi sa’ad da muka bi umurninsu kuma muka bi su da haƙuri. (Kol. 4:6) A bara, sa’ad da ’yan’uwa daga ofishin reshe suke tattaunawa da wata ma’aikaciya a hotal, ta gaya musu cewa: “Muna jin daɗi idan mutanenku sun sauka a hotal ɗinmu domin suna da kirki. Suna da ladabi, suna girmama ma’aikatanmu sosai kuma suna kula da hotal ɗin da kyau.”
6. Ta yaya za mu girmama Allah ta wajen adon da muke yi a garin da muka je halartan taron?
6 Idan mun saka bajonmu na taron gunduma, hakan zai jawo hankalin mutane ga taron. Ƙari ga haka, zai ba da shaida ga mutane kuma wasu ’yan’uwa da suka zo taron za su san cewa mu ma Shaidu ne. A garin da ake taron, mutane za su lura cewa waɗanda suke sanye da bajo sun yi ado mai kyau, ba kamar mutanen duniya da suke saka tufafi marasa fasali ko kuma na yayi da ba su dace ba. (1 Tim. 2:9, 10) Saboda haka, ya kamata mu saka tufafin da suka dace sa’ad da muke garin da ake taron gunduma da kuma sa’ad da muka je inda za mu sauka. Ba zai dace mu saka guntun wando da T-shat sa’ad da muke zuwa ba. Ya kamata mu saka tufafi masu kyau sa’ad da muke zuwa wurin taron ko da a Majami’ar Taro ne ko kuma Majami’ar Mulki da ake Faɗaɗawa. Idan za mu canja tufafinmu bayan an tashi daga taro da yamma don mu fita cin abinci, ya kamata mu tuna cewa mun zo halartan taro ne. Saboda haka, kada mu saka tufafi marasa fasali.
7. Ta yaya za mu amfana daga yin tarayya da ’yan’uwanmu a taro?
7 Isra’ilawa suna jin daɗin tarayya da bayin Jehobah daga wasu ɓangarorin ƙasarsu har ma da wasu ƙasashe a duniya, sa’ad da suka halarci bukukuwa, kuma hakan yana sa su kasance da haɗin kai. (A. M. 2:1, 5) A lokacin taron gunduma, mutane sukan lura da yadda muke nuna ƙauna ga juna duk da cewa mun fito ne daga wurare dabam-dabam. Wannan dangantaka mai kyau da ke tsakaninmu Shaidu tana burge mutane. (Zab. 133:1) Maimakon zuwa sayan abincin rana a cikin gari, zai dace mu zo da abincinmu don mu samu zarafin yin taɗi da ’yan’uwa maza da mata da suka zauna kusa da mu sa’ad da ake hutun rana!
8. Me ya sa ya kamata mu taimaka da yin aiki a wurin taro in da hali?
8 Yadda muke tsara taronmu yana burge mutane sosai, musamman idan suka san cewa ba biyan ’yan’uwa ake yi ba amma da son rai suke yin aikin. Shin, kuna iya ‘ba da kanku da son rai’ don yin wasu ayyuka a taro? (Zab. 110:3) Don su koya wa yaransu yadda za su riƙa taimaka wa mutane, iyalai sukan ba da kai don yin aiki a wurin taro. Idan kai mai kunya ne, taimakawa da ayyuka a taron hanya ce mai sauki na sanin ’yan’uwa. Wata ’yar ’uwa ta ce: “Ban san mutane da yawa a taron ba sai iyalina da abokaina kaɗai. Amma, da na taimaka da shara, sai na san ’yan’uwa maza da mata da yawa. Kuma hakan ya sa ni farin ciki sosai!” Idan muka yi ƙoƙari muka san ’yan’uwa dabam-dabam sa’ad da muka taimaka da aiki a taro, za mu yi farin ciki sosai. (2 Kor. 6:12, 13) Idan ba ka taba taimaka wajen yin aiki a taro ba, ka fada wa dattawa su gaya maka abin da za ka yi don ka cancanta.
9. Ta yaya za mu gayyaci mutane zuwa taron gundumar?
9 Ku Gayyaci Mutane Su Zo Su Ji Maganar Allah: Kamar yadda muka saba yi a shekarun baya, makonni uku kafin taron gunduma, za mu yi kamfen don gayyatar mutane zuwa taron. ’Yan’uwa za su yi ƙoƙari su gayyaci dukan mutanen da ke yankinsu in da hali. (Duba akwatin nan “Yadda Za Mu Ba da Takardar Gayyatar.”) Idan akwai wasu takardun gayyata da suka rage, ka zo da su wurin taron gundumar. Za a yi amfani da su wajen yin wa’azi a duk inda aka samu zarafi a garin da ake taron.
10. Ka ba da labarin da ya nuna cewa kamfen da muke yi na ba da takardun gayyata yana da amfani.
10 Mutane suna amsa wannan gayyatar ne? Wani ɗan atenda ya ba wa wasu ma’aurata wurin zama a wani taron gunduma. Sai suka gaya masa cewa sun yi tafiya mai nisan mil 200 da wani abu don su halarci taron. Abin da suka gani a takardar gayyata da aka ba su ne ya nuna musu alama cewa “taron zai yi daɗi sosai!” Wani misali kuma shi ne, wata ’yar’uwa da ta fita wa’azi ta gayyaci wani mutumin da ya nuna yana so ya san abin da ake yi a wurin taron. Sai ta yi amfani da takardar gayyatar don ta bayyana masa abin da ake yi a wurin taron. ’Yan kwanaki bayan haka, da ta je taron sai ta ga mutumin da abokinsa suna riƙe da ɗaya daga cikin sababbin littattafan da aka ba da a taron!
11. Me ya sa halartan taron gunduma kowace shekara yake da muhimmanci?
11 Bukukuwa da Isra’ilawa suke yi tanadi ne mai kyau daga wurin Jehobah don ya taimaka wa Isra’ilawa su “bauta masa cikin sahihanci da cikin gaskiya.” (Josh. 24:14) Hakazalika, halartan taron gunduma a kowace shekara yana da muhimmanci a bautarmu ga Allah kuma yana taimaka mana mu yi “tafiya cikin gaskiya.” (3 Yoh. 3) Ubangiji zai albarkaci dukan masu ƙaunar gaskiya yayin da suke ƙoƙari don su halarci taron kuma su amfana sosai!
[Bayanin da ke shafi na 2]
Nuna hali mai kyau a garin da ake taron gundumar yana girmama Allah
[Bayanin da ke shafi na 3]
Mako uku kafin mu halarci taron gunduma, za mu yi kamfen don gayyatar mutane zuwa taron
[Akwati a shafi na 2-4]
Tunasarwa Game Da Taron Gunduma Na Shekara Ta 2012
◼ Lokatan Taro: Za a soma taron ne da ƙarfe 9:20 na safe a dukan kwanaki uku. Sa’ad da aka gabatar da kaɗe-kaɗe, ya kamata dukanmu mu zauna don a soma taron da tsari. Za a kammala tsarin ayyuka na ranar Juma’a da Asabar da ƙarfe 4:55 da yamma, kuma da ƙarfe 3:40 da yamma na ranar Lahadi.
◼ Ajiye Mota: A dukan wuraren taron gunduma, ’yan atenda za su nuna wa mutane inda za su ajiye motocinsu. Don Allah ku ba su haɗin kai.—Kor. 13:4, 5.
◼ Ajiye Wajen Zama: Za ku iya kama wajen zama ne kawai ga waɗanda kuke tafiya tare a cikin motarku da waɗanda kuke zama tare a gida ɗaya, da kuma waɗanda kuke nazarin Littafi Mai Tsarki da su yanzu.—1 Kor. 13:5.
◼ Abincin Rana: Don Allah ku kawo abincin da za ku ci da rana, maimakon ku fita waje don sayan abinci a lokacin shaƙatawa. Za ku iya yin amfani da abin zuba abinci ɗan ƙarami da za ku iya ajiyewa a ƙarƙashin kujera. Ba a yarda a kawo abin zuba abinci mai girma da kuma tambulan a wajen taron gundumar ba.
◼ Ba da Kyauta: Za mu iya nuna godiya ga shirye-shiryen da aka yi don gudanar da taron ta wajen ba da kyauta da son rai a Majami’ar Mulki ko kuma a taron gunduma don tallafa wa aikin wa’azi da ake yi a dukan duniya. Idan za ku ba da gudummawa ta hanyar cek a wurin taron, ku rubuta kalmomin nan biyu, “Watch Tower.”
◼ Haɗari da Jinyar Gaggawa: Idan aka sami jinyar gaggawa a wurin taro, don Allah ku sanar da ɗan atenda da ke kusa, wanda zai kai marar lafiyar zuwa Sashen Kula da Jinyar Gaggawa domin ƙwararrun ma’aikata masu jinyar gaggawa su duba abin da yake damunsa kuma su ba da taimako.
◼ Magunguna: Idan kuna da wani maganin da kuke sha a kai a kai saboda rashin lafiya, don Allah ku taho da shi, tun da ba za a tanadar da shi a wurin taron gundumar ba. Idan kuna karɓan allura saboda ciwon sukari, ya kamata ku zubar da allurar da kuma sirinji a inda ya dace amma ba a kwandon sharar da ke wurin taron gundumar ko kuma a inda kuka sauka ba.
◼ Takalma: Saboda guje wa rauni, ya kamata a saka takalma da za a ji daɗin tafiya da su kuma waɗanda ba su da tsini sosai.
◼ Turare: Muna nuna ƙauna ga waɗanda ke da ciwon ƙirji ko makamancin hakan ta wajen rage yadda muke amfani da turare a taron gundumar.—1Kor. 10:24
◼ Fom Ɗin Please Follow Up (S-43): Ku yi amfani da fom ɗin nan Please Follow Up (S-43) don ba da bayani game da wa’azin da kuka yi a lokacin taron. Masu shela su taho da fom ɗin guda ɗaya ko biyu zuwa wurin taron. Za ku iya kai fom ɗin zuwa Sashen Kula daLittattafai don su yi aiki a kai ko kuma ku ba sakataren ikilisiyarku sa’ad da kuka koma gida.—Duba Hidimarmu Ta Mulki ta Mayu 2011, shafi na 3.
◼ Gidan Abinci da Masu Sayar da Abubuwa a Wajen Taro: Ku girmama sunan Jehobah ta hali mai kyau a gidajen abinci. Ba zai dace mu riƙa zuwa wajen masu abinci da masu talla a lokacin da ake taron ba.
◼ Masauki: Ku nuna ɗiyar ruhu sa’ad da ’yan Sashen Kula da Ɗakuna ko kuma ma’aikatan hotal suke ba ku masauki. (Gal. 5:22, 23) Da yake suna kula da baƙi da yawa, idan muka nuna alheri da haƙuri da sanin ya kamata, za su yi farin ciki. Ku yi la’akari da yadda za ku yi hakan ta wurin bincika abubuwan da aka ambata a gaba:
(1) Don Allah kada ku kama ɗakuna fiye da kima kuma kada mutanen da suke kwana a ɗaki su wuce adadin da aka umurta.
(2) Kada ku bar ɗakin aka ba ku ba gaira ba dalili amma idan wata bukatar gaggawa ta taso, ku sanar da ma’aikatan hotal ɗin ba tare da ɓata lokaci ba.—Mat. 5:37.
(3) Ku yi dahuwa a wuraren da aka amince da yin hakan ne kawai. Kada ku yi dahuwa a lokacin da ake yin taro domin hakan ba zai nuna cewa muna girmama Allah ba.—Luk 10:38-42.
(4) Iyaye su riƙa kula da yaransu a kowane lokaci sa’ad da suke inda suka sauka, ko a hotal ko a wurin taro.
(5) Kada ku zauna a ɗakunan da ’yan Kula da Sashen Ɗakuna ba su ba ku ba. Ku ba da haɗin kai ta wajen sauka a inda aka sa ku. Kada ku yi dare a waje ko kuma ku kwana a ɗakunan da aka keɓe wa mata idan kai namiji ne, mace kuma kada ta kwana inda maza suke.
(6) Idan kuka sami matsala a inda kuka sauka, ku je ku sanar da Sashen Kula da Ɗakuna sa’ad da kuke wurin don ku samu taimako.
◼ Ba da Kai don Yin Hidima: Ya kamata duk wanda yake son ba da kai ya je Sashen Kula da Hidima a wurin taron gundumar. Yara da ba su kai shekara sha shida ba tukun za su iya ba da kansu ta yin aiki tare da iyayensu ko kuma da wani babba da iyayen suka amince da shi.
[’Yan rubutu na ba da bayani a shafi na 4]
Yadda Za Mu Ba da Takardar Gayyatar
Zai dace mu taƙaita abin da za mu faɗa don mu iya rarraba takardun gayyata a dukan unguwoyi. Za mu iya ce: “Sannu. Muna rarraba waɗannan takardun gayyata a dukan duniya. Ga naka kofi. Za ka samu ƙarin bayani a ciki.” Ku kasance da fara’a sa’ad da kuke yin hakan. Kuna iya ba da mujallu a duk lokacin da ya dace sa’ad da kuke rarraba takardar gayyatar a ƙarshen mako.