Tarurrukan Gunduma—Lokacin Yin Bauta da Farin Ciki
1. Ta yaya idodin Isra’ilawa suka yi kama da tarurrukan gunduma da muke yi a yau?
1 Yusufu, Maryamu, yaransu, da kuma wasu suna zuwa Urushalima a kai a kai don idi na shekara-shekara. A waɗannan lokatan, su da wasu masu bauta za su ƙyale ayyukansu na yau da kullum don su mai da hankali ga ayyuka na ruhaniya waɗanda suka fi muhimmanci a rayuwarsu. Idodin ya ba su zarafi su yi tunani da kuma magana a kan alherin Jehobah kuma su tattauna Dokarsa. Tarurrukan gundumarmu na gaba zai ba mu irin wannan zarafin na bauta wa Jehobah da farin ciki.
2. Me ya kamata mu yi don mu yi shirin halartar taron gunduma da ke zuwa?
2 Ana Bukatar Shiri: Iyalin Yesu suna bukatar yin tafiyar mil ɗari da ashirin daga Nazarat zuwa Urushalima. Ko da yake ba mu san ko ’yan’uwa nawa ne Yesu yake da su ba, amma za mu iya yin tunani a kan irin shiri da kuma ƙoƙarin da Yusufu da Maryamu suke bukatar su yi. Shin ka yi shirye-shirye da suka dace don ka samu halartar dukan kwanaki uku na taron gunduma da ke zuwa? Hakan yana bukatar ɗaukan hutu daga wurin aiki ko kuma gaya wa shugaban aikinka ko kuma malamin makarantar yaronka cewa ba zai zo makaranta waɗannan kwanaki ba. Shin ka shirya masauki idan akwai bukata? Za ka iya taimaka wa wani a cikin ikilisiyarku da ke da bukata ta musamman don ya halarci taron?—1 Yoh. 3:17, 18.
3. Ta yaya idodin Isra’ilawa ya kawo zarafin yin cuɗanya mai ƙarfafawa?
3 Tarayya Mai Ƙarfafawa: Idodin Yahudawa ya ba su zarafin su yi cuɗanya mai ƙarfafawa da ’yan’uwansu! Babu shakka, iyalin Yesu sun yi ɗokin kasancewa tare da abokansu. Sun kuma more zarafin samun sababbin abokai a cikin Yahudawa da shigaggu waɗanda za su halarci taron ko kuma sa’ad da suke zuwa Urushalima da dawowa.
4. Ta yaya za mu nuna cewa muna godiya don ’yan’uwancinmu na Kirista?
4 Dalili ɗaya da ya sa bawa mai-aminci mai-hikima ya shirya mana mu yi taro don mu saurari jawabai a tarurrukan gunduma maimakon su rubuta shi a cikin littattafai shi ne don mu ƙarfafa juna. (Ibran. 10:24, 25) Saboda haka, ka yi shirin isa wurin taron kowace rana a kan lokaci don more tarayya da wasu kafin mai kujeran sashen ya gabatar da kaɗe-kaɗen da ke nuna cewa lokaci ya yi na neman wurin zama. Maimakon barin wurin taron don neman abincin rana, ya kamata mu je wurin taron da abincinmu kuma mu kasance a wurin don mu samu damar tattaunawa da waɗanda suke zama kusa da mu. Ya kamata mu riƙa nuna godiya don ’yan’uwancinmu na Kirista domin kyauta ce daga wurin Jehobah.—Mi. 2:12.
5. Menene zai taimakemu mu amfana sosai daga tsarin ayyukan?
5 Lokacin Koyo: Tun yana ƙarami, Yesu ya yi amfani da lokacin idodi domin ya koya game da Ubansa na samaniya. (Luk 2:41-49) Menene zai taimake mu da iyalinmu mu amfana daga jawaban da za a ba da? A lokacin da ake ba da jawaban, ku zauna wuri ɗaya kuma ku daina yin maganganu. Kada ku ƙyale wayarku, pager, ko kuma wasu na’urori su dami mutane. Ku haɗa idanu da mai jawabin, kuma ku ɗan rubuta batutuwa. Ku zauna tare a matsayin iyali kuma ku tabbata cewa yaranku suna saurarawa. Da yamma, ku keɓe wasu lokaci don tattauna darussan da kuka more tare.
6. Me ya kamata mu yi la’akari da shi game da ado da tufafinmu?
6 Adonmu da Tufafi: Attajirai da suke tafiya a hanyar za su gane iyalin Yesu da wasu Yahudawa masu bauta da suke zuwa da kuma dawowa daga idin saboda tuntayen da suka sa a shafin rigarsu da kuma shuɗin zare dake saman tuntayen. (Lit. Lis. 15:37-41) Ko da Kiristoci ba sa saka tufafi na musamman, an san mu da saka tufafi mai kyau da kuma mai tsabta. Ya kamata mu kula da adonmu sa’ad da muke tafiya da dawowa daga wurin taron gundumar da kuma a garin da za a yi taron. Ko da mun canja tufafinmu bayan lokacin taron, ya kamata mu yi ado mai kyau kuma mu sa bajin taron gundumar. Idan mun yi hakan za mu fita dabam daga mutanen da ba Shaidu ba kuma za mu kafa musu misali mai kyau.
7. Me ya sa ya kamata mu yi la’akari da ba da kai don yin hidima a taron gunduma?
7 Ana Bukatan Masu Hidimomi: Ana bukatar masu hidimomi da yawa don taron gundumar ya tafi daidai. Za ka iya taimakawa kuwa? (Zab. 110:3) Aikin da ake yi a wurin taron gunduma sashen tsarkakkiyar bauta ce kuma tana ba da shaida mai kyau. Sa’ad da ya ga yadda waɗanda suka ba da kansu don su share wurin da aka yi taron gundumar hakan ya burge manajan wurin har ya rubuta: “Ina so na yi muku godiya don wannan abu mai ban al’ajabi da na gani. Na saba ji ana faɗa cewa Shaidun Jehobah mutane na musamman ne masu suna mai kyau a kamfaninmu don suna barin wurin taron da tsabta sosai fiye da yadda yake kafin su yi amfani da shi. Ku da ƙungiyarku kun sa wurin taron nan ya zama wuri mai kyau ga yankin kuma kun yi hakan da rukunin mutane mafi kyau da ba mu taɓa sha’ani da su ba.”
8. Wane zarafin ba da shaida ne za a samu a garin da za a yi taron gundumar?
8 Zarafin Ba da Shaida: Mutane da yawa a garin da ake yin taron za su ga baƙi masu ado mai kyau da suka saka bajin taron gundumar, kuma hakan zai iya ta da marmarinsu, kuma ya ba mu zarafin gaya musu game da taron gundumar. Wani yaro mai shekara huɗu ya je wani gidan abinci da sabon littafin da aka fito da shi a taron gundumar bayan tsarin ayyuka na ranar kuma ya nuna wa wata mai ba da abincin. Hakan ya ba iyayen yaron zarafin su gayyaci matar zuwa taron gundumar.
9. Ta yaya za mu yi koyi da godiyar da iyalin Yesu suke da shi ga tanadin ruhaniya na Jehobah?
9 Idodi na zamanin dā abin farin ciki ne da Yahudawa masu ruhaniya suke ɗokin halarta. (K. Sha 16:15) Iyalan Yesu sun yi farin cikin yin sadaukarwa don su halarta da kuma amfana sosai. Mu ma muna son tarurrukanmu na gunduma, kuma muna ɗaukarsa kamar baiwa daga wurin Ubanmu mai ƙauna na samaniya. (Yaƙ. 1:17) Yanzu lokaci ne na yin shiri don wannan zarafi na bauta wa Jehobah da farin ciki!
[Akwati da ke shafi na 6]
Tunasarwa Game da Taron Gunduma
◼ Lokacin da Za a Soma Tsarin Ayyuka: Za a soma taron ne da ƙarfe 9:20 na safe a dukan kwanakin uku. Sa’ad da aka gabatar da kaɗe-kaɗe, ya kamata mu duka mu sami wurin zama don taron ya soma cikin daraja. Za a kammala tsarin ayyuka na ranar Juma’a da Asabar da ƙarfe 4:55 da yamma, kuma da ƙarfe 3:40 da yamma na ranar Lahadi.
◼ Ajiye Mota: A dukan wuraren taron gunduma, ’yan atenda za su taimaka wa mutane su ajiye motarsu. Don Allah ku ba su haɗin kai.—1 Kor. 14:40.
◼ Ajiye Wajen Zama: Za ku iya ajiye wajen zama ne kawai ga waɗanda kuke tafiya tare a cikin motarku da waɗanda kuke zama tare a gida guda, da kuma waɗanda kuke nazarin Littafi Mai Tsarki da su yanzu.—1 Kor. 13:5.
◼ Abincin Rana: Don Allah ku kawo abincin da za ku ci da rana, maimakon ku fita waje don sayan abinci a lokacin shaƙatawa. Za ku iya yin amfani da abin zuba abinci ɗan ƙarami da za ku iya ajiyewa a ƙarƙashin kujera. Ba a yarda a kawo abin zuba abinci mai girma da kuma tambulan a wajen taron gundumar ba.
◼ Ba da Kyauta: Za mu iya nuna godiya ga shirye-shiryen da aka yi don gudanar da taron ta wajen ba da kyauta da son rai ga aiki na dukan duniya a Majami’ar Mulkinmu ko kuma a taron gunduma. Idan za ku ba da gudummawa ta hanyar cek a wurin taron, ku rubuta kalmomin nan biyu, “Watch Tower.”
◼ Haɗari da Jinyar Gaggawa: Idan aka sami jinyar gaggawa a wurin taro, don Allah ku sanar da ɗan atenda da ke kusa, wanda zai kai marar lafiyan zuwa Sashen Kula da Jinyar Gaggawa domin ƙwararrun ma’aikata masu jinyar gaggawa su duba irin matsalar kuma su ba da taimako.
◼ Ɗaukan Jawabi: Ka da ku haɗa abubuwan ɗaukan magana da lantarkin wurin taron ko na’urarmu na sauti, kuma ku yi amfani da shi ne kawai a yadda ba zai dame wasu ba.
◼ Keken Jarirai: Kada a kawo keken jarirai zuwa wurin taron. Amma dai, za a iya zuwa da kujerun da za a aza su kusa da iyayen.
◼ Wasan Kwaikwayo: Ba zai nuna ƙauna ba idan ’yan’uwa mata suka ɗaura babban ɗan kwali a ranar Lahadi da rana ba sa’ad da ake nuna wasan kwaikwayo, domin hakan zai kāre waɗanda ke zaune a baya. Musamman domin a yanzu ana amfani ne da Majami’un Taro da kuma Majami’un Mulki da ake faɗaɗawa da aka sauƙaƙa gininsu.—1 Kor. 10:24.
◼ Kayan Ƙamshi: Zai zama abin alheri idan muka rage shafa turare mai ƙamshi sosai da marar ƙamshi da zai dami mutanen da ke da ciwon ƙirji ko makamancin hakan.—Filib. 2:4.
◼ Gidan Abinci/Masu Sayar da Abubuwa a Waje: Ku ɗaukaka sunan Jehobah ta halinku mai kyau a gidajen abinci. Wawanci ne zuwa wajen masu abinci da masu talla a lokacin da ake taro. Idan mutum yana son ya sayi wani abu, zai dace ya sayi abin kafin a soma taron ko kuma bayan an kammala taron.
◼ Hidimar Ba da Kai: Farin cikin da muke samu don halartar taron gunduma zai ƙaru idan mun ba da kanmu don taimaka a aikin da ya kamata. (A. M. 20:35) Ya kamata duk wanda yake son yin hakan ya je Sashen Kula da Hidima a wurin taron gundumar. Yara da ba su kai shekara sha shida ba tukun za su iya ba da kansu ta yin aiki tare da iyayensu ko kuma wani babba da sashen suka zaɓa.
◼ Masaukai: (1) Ku nuna ɗiyar ruhu sa’ad da kuke karɓan masaukinku sa’ad da kuka isa wurin taron. (2) Kada ku zauna a ɗakunan da sashen Kula da Ɗakuna bai sa ku ba. Ku ba da haɗin kai ta wajen sauka a inda aka sa ku. (3) Kada ku yi dare a waje ko kuma ku kwana a ɗakunan da aka keɓe wa mata idan kai namiji ne, mace kada ta kwana inda maza suke. (4) Idan kuka sami matsala da wurin kwanan da aka ba ku, ku je ku sanar da sashen da ke kula da masauki nan da nan a wajen taron. (5) Idan a hotel kuka sauƙa, ku ba da haɗin kai ga masu kula da hotel ɗin. (6) Ku yi dahuwa a wuraren da aka amince da yin hakan ne kawai. (7) Kada ku yi dahuwa a lokacin da ake yin taro domin hakan ba ya nuna daraja ga abubuwa na ruhaniya.—Luk 10:38-42.
◼ Sufuri: Tun da rai yana da tsarki, yana da muhimmanci dukanmu mu mai da hankali ga kiyaye haɗari sa’ad da muke neman motar da za ta kai mu taron gunduma na wannan shekarar. Dattawan su tabbatar da cewa motar tana da lafiya, tayoyi masu kyau, birki, da wuta. Ko da hakan zai bukaci su biya ƙarin kuɗi, ya fi kyau a yi amfani da lafiyayyun motoci. Ku nemo direbobin da za su ba da haɗin kai a waɗannan hanyoyin: kada a labta wa motar kaya, kada ya yi mugun gudu, ya amince cewa zai huta sosai kafin washe gari da za a yi tafiyar, kuma kada ya sha giya kafin ko kuma lokacin tafiyar. Kada ku ɗauki zancen kiyaye haɗari kamar abin wasa, ku guji haɗarurruka da za a iya guje musu.—Mis. 22:3.