Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/14 pp. 2-5
  • Ku Kasance da Hali Mai Kyau a Gaban Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Kasance da Hali Mai Kyau a Gaban Mutane
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Tunasarwa Game da Taron Yanki
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Hali Mai Kyau da Ke Girmama Allah
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Taron Gunduma da Muke Yi Suna Ba da Shaida Mai Kyau Game da Gaskiya
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Kwanaki Uku na Wartsakewa ta Ruhaniya
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 4/14 pp. 2-5

Ku Kasance da Hali Mai Kyau a Gaban Mutane

1. Me ya sa yake da muhimmanci mu nuna hali mai kyau a babban taron da ke zuwa?

1 Muna jawo hankalin jama’a a duk lokacin da muke manyan taro a kowace shekara, saboda haka, yana da muhimmanci halayenmu su nuna cewa muna wakiltar Allahn da muke yi wa ibada. (Lev. 20:26) Ya kamata halayenmu masu kyau da kuma ado da tufafinmu su nuna cewa mu mabiyan Kristi ne da gaske. Yayin da muke halartan taron yanki ko na ƙasashe, ta yaya za mu riƙa yin “al’amura na dacewa,” wato mu nuna hali mai kyau a gaban mutane kuma mu ɗaukaka Ubanmu na sama?—1 Bit. 2:12.

2. Za mu samu damar yin mene ne a lokacin babban taron?

2 Ku Nuna Halin Kirista: Irin ƙaunar da muke nuna wa juna da kuma yadda muke bi da “waɗanda ke waje” sun sha bambam da irin halayen da ke tasiri a duniya. (Kol. 3:10; 4:5; 2 Tim. 3:1-5) Ya kamata mu yi wa ma’aikatan da ke masaukinmu da kuma wuraren cin abinci kirki kuma mu yi haƙuri da su, ko sa’ad da wata matsala ta taso ma. Zai dace kuma mu ba da kyauta ga waɗanda suka taimaka mana.

3. Wace tunasarwa ce aka yi wa iyaye, kuma me ya sa?

3 Iyaye su riƙa lura da ’ya’yansu a wurin taron da wuraren cin abinci da kuma masaukai. (Mis. 29:15) Wata manajar wani masauki ta gaya ma wasu ma’aurata cewa: “Muna son mutanenku sosai. Iyalanku da yaranku suna da hankali da kuma ladabi. Dukan ma’aikatanmu suna yaba muku, kuma za mu so a ce kuna sauƙa a nan kowane ƙarshen mako.”

4. Wane irin ado da tufafi ne ya kamata mu sanya a yankin da muke halartan babban taro?

4 Tufafin da Suka Dace: Ya kamata irin tufafin da muke sakawa a taron su zama waɗanda suka dace kuma masu kyau, ba irin waɗanda suka zama gama gari a duniya ba. (1 Tim. 2:9) A lokacin da muka sauka a masaukinmu da lokacin da muke barin wurin da kuma sa’ad da muke shakatawa kafin taro ko bayan hakan, zai dace mu guji saka tufafin da ba su dace ba. Idan muka yi hakan, za mu iya sanya bajon taron kuma ba za mu ji kunyar yi wa mutane wa’azi ba idan muka sami dama. Halayenmu masu kyau da kuma ado da tufafinmu a babban taro za su jawo hankalin mutanen kirki ga saƙon Littafi Mai Tsarki kuma za su faranta wa Jehobah rai.—Zaf. 3:17.

Tunasarwa Game da Taron Yanki na 2014

◼ Lokatan Taro: Za a soma taron da kaɗe-kaɗe da ƙarfe 8:20 na safe a dukan ranaku ukun. Sa’ad da aka gabatar da kaɗe-kaɗe, ya kamata dukanmu mu zauna don a soma taron da tsari. Za a yi waƙa da kuma addu’ar kammala taron da ƙarfe 3:55 na yamma a ranar Juma’a da Asabar, kuma da ƙarfe 2:50 na yamma a ranar Lahadi.

◼ Taron Ƙasashe: Za a yi taron ƙasashe a wasu ƙasashe. Ku san cewa an riga an zaɓi ikilisiyoyi da kuma ’yan’uwa da za su halarta, kuma an yi hakan ne bayan an yi lissafin yawan kujeru da wurin faka mota da kuma masaukai da ake da su. Wurin zai iya yin cunkoso idan masu shela da ba a gayyace su ba suka halarta. Idan saboda yanayinka kana bukatar ka halarci wani babban taro dabam da wanda ikilisiyarku za ta halarta, kada ka zaɓi taron ƙasashe.

◼ Faka Mota: ’Yan atenda ne za su nuna mana wurin da ya kamata mu yi fakin. Don Allah ku bi ja-gorarsu.—1 Kor. 13:4, 5.

◼ Kama Wajen Zama: Za ku iya kama wajen zama ma waɗanda kuke tafiya tare a cikin motarku ko waɗanda kuke zama tare a gida ɗaya, ko kuma waɗanda kuke nazarin Littafi Mai Tsarki da su. An keɓe wuraren zama na musamman don tsofaffi da kuma marasa lafiya. Tun da yake waɗannan kujerun ba su da yawa, mutum ɗaya ko biyu da suke kula da tsofaffi ko masu rashin lafiyar ne kaɗai za su iya zama tare da su.

◼ Wasan Kwaikwayo: ’Yan’uwa mata da suka ɗaura irin ɗan kwali da zai iya hana waɗanda ke bayansu ganin wuri su cire su sa’ad da ake yin wasan kwaikwayo.

◼ Abincin Rana: Don Allah ku kawo abincin rana maimakon ku fita waje don sayan abinci sa’ad da ake shan iska. Za ku iya yin amfani da ƙaramar koola da za ku iya ajiyewa a ƙarƙashin kujera. Ba a yarda a kawo babbar koola da kuma tambulan a wajen taron yankin ba.

◼ Gudummawa: Za mu iya nuna godiya ga shirye-shiryen da aka yi don gudanar da taron ta wajen ba da gudummawa da son rai a wajen taron. Idan za ku ba da gudummawa ta hanyar cek, ku rubuta kalmomin nan “Watch Tower” daidai yadda suke a nan, a kan cek ɗin.

◼ Magunguna: Idan akwai maganin da kuke sha a kai a kai, don Allah ku zo da shi, tun da ba za ku sami irinsa a wurin taron ba. Idan kuna amfani da allurar ciwon sukari, ku zubar da alluran da sirinjin a inda ya dace. Kada ku saka su a kwandon sharar da ke wurin taron ko kuma a masaukinku.

◼ Rigakafi: Don Allah ku lura don ku guji samun raunuka sakamakon zamewa da kuma tuntuɓe. Kowace shekara ana samun rauni sakamakon irin takalma da ake sakawa, musamman ma masu tsini. Saboda haka, zai dace ku saka takalma da za ku ji daɗin tafiya da su kuma waɗanda ba su da tsini sosai.

◼ Keken Jarirai da Kujerun Shaƙatawa: Kada a kawo keken jarirai da kujerun shaƙatawa wurin taron. Amma, za ku iya zuwa da kujerun yara masu kāriya idan za a ajiye su kusa da wurin zaman iyayensu.

◼ Turare: Saboda waɗanda ke fama da ciwon ƙirji ko makamancin hakan, zai dace mu rage yawan amfani da turare mai ƙarfi a taron yankin. Hakan zai nuna cewa muna ƙaunar ’yan’uwanmu.—1 Kor. 10:24.

◼ Fom Ɗin Please Follow Up (S-43): Ku yi amfani da fom ɗin Please Follow Up don ba da bayani game da wani da kuka yi masa wa’azi a lokacin taron kuma ya so saƙonmu. Masu shela su riƙe fom ɗaya ko biyu a jikinsu sa’ad da suke halartan taron. Za ku iya kai fom ɗin da kuka cika Sashen Kula da Littattafai ko kuma ku ba sakataren ikilisiyarku sa’ad da kuka koma gida.

◼ Gidan Abinci da Masu Talla a Waje: Ku girmama sunan Jehobah ta wajen nuna hali mai kyau a gidajen abinci. Ku saka tufafi da za su nuna cewa ku Kiristoci na gaskiya ne. Ba zai dace mu riƙa zuwa sayan abubuwa yayin da ake taro ba.

◼ Masauki:

  1. Idan za ku kama ɗaki a hotal, don Allah kada ku kama ɗakuna fiye da waɗanda kuke bukata kuma kada ku bar mutane fiye da adadin da aka ƙayyade su kwana a ɗakin.

  2. Kada ku soke yarjejeniyar kama ɗakin da kuka yi ba gaira ba dalili, amma idan wata bukata ta gaggawa ta sa ku yin hakan, ku sanar da ma’aikatan hotal ɗin nan da nan don a ba da ɗakin ga wasu dabam. (Mat. 5:37) Idan lallai sai kun soke yarjejeniyar, ku tabbata kun rubuta takardar shaidar yin hakan. Idan kun soke yarjejeniyar amma ba ku sanar da ma’aikatan hotal ɗin kwana biyu kafin ranar da ya kamata ku shiga ɗakin ba, ba za a mayar muku da kuɗinku ba.

  3. Kada ku ɗauki abin kwashe kaya da aka tanadar idan ba ku bukatarsa, kuma idan kun ɗauka, ku mayar da zarar kun gama aiki da shi don wasu su samu su yi amfani da shi.

  4. Ku yi dahuwa a wuraren da aka amince da yin hakan ne kawai. Kada ku yi dahuwa a lokacin da ake yin taro domin hakan ba zai nuna cewa muna girmama Allah ba.

  5. Idan ana tanadar da abincin safe a inda kuka sauka, ku ɗauki daidai abincin da aka ajiye muku kawai.

  6. A kowane lokaci, ya kamata ku nuna cewa kuna bin ja-gorar ruhu mai tsarki a yadda kuke bi da ma’aikatan hotal da kuma ’yan’uwan da ke Sashen Kula da Ɗakuna. Suna kula da mutane da yawa, saboda haka, za su ji daɗi sosai idan muka nuna musu alheri da haƙuri da kuma sanin yakamata.

  7. Iyaye su riƙa kula da yaransu a kowane lokaci sa’ad da suke inda suka sauka, ko a hotal ko a wani wuri dabam.

  8. Kada ku zauna a ɗakunan da Sashen Kula da Ɗakuna ba su ba ku ba. Ku ba da haɗin kai ta wajen sauka a inda aka kama muku. Kada ku yi dare a waje, kuma kada maza su kwana a ɗakin mata ko kuma mata su kwana a ɗakin maza.

  9. Idan kuka sami matsala a inda kuka sauka, ku sanar da Sashen Kula da Ɗakuna sa’ad da kuke wurin taron don su taimake ku.

◼ Ba da Kai don Yin Hidima: Duk wanda yake son ya ba da kai ya je Sashen Kula da Hidima a wurin taron. Yara da ba su kai shekara 16 ba za su iya ba da kansu ta yin aiki tare da iyayensu ko kuma da wani da ya manyanta, wanda iyayen suka amince da shi.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba