Kwanaki Uku na Wartsakewa ta Ruhaniya
1. Mene ne za mu more a taron gunduma na wannan shekarar?
1 A wannan duniyar Shaiɗan da babu ruhaniya, Jehobah ya ci gaba da wartsake bayinsa. (Isha. 58:11) Hanya ɗaya da Jehobah yake ƙarfafa mu ita ce ta taron gunduma na shekara-shekara. Yayin da taron gunduma na wannan shekarar take kusatowa, ta yaya za mu yi shiri don mu more da kuma ƙarfafa mutane a ruhaniya?—Mis. 21:5.
2. Waɗanne shirye-shirye ne ya kamata mu kammala?
2 Idan ba ka riga ka yi hakan ba, ka ɗauki lokaci yanzu don ka shirya ayyukanka don ka samu halartar dukan kwanaki uku na taron gundumar. Ka lissafa lokacin da za ka yi tafiya zuwa wurin taron kowacce rana don kada ka makara kuma ka samu wurin zama kafin tsarin ayyukan ya soma? Hakika, ba ma son mu ƙi cin abincin ruhaniya mai ƙarfafawa ko ɗaya da Jehobah ya shirya mana. (Isha. 65:13, 14) Shin ka kammala shirye-shirye don sufuri da kuma masauki?
3. Waɗanne shawarwari ne za su taimaka mana da iyalinmu mu amfana sosai daga tsarin ayyukan?
3 Mene ne zai taimaka maka ka saurari tsarin ayyukan sosai? Idan zai yiwu, ka yi barci sosai a kowacce dare na taron gundumar. Ka riƙa kallon mai ba da jawabin. Ka buɗe dukan nassosin da aka karanta a Littafi Mai Tsarki naka. Ka ɗan rubuta gajeren darasin da ka koya. Iyalai su yi ƙoƙari su zauna tare don iyaye su taimaki yaransu su saurara. (Mis. 29:15) Wataƙila za ku iya tattauna taƙaitawar tsarin ayyukan kowacce yamma a matsayin iyali. Domin iyalinka su ci gaba da samu wartsakewa bayan taron, za ku iya keɓe lokaci a lokacin Bauta ta Iyalinku da yamma don tattauna fitattun bayanai da iyalinku za su yi amfani da su.
4. Ta yaya za mu taimaka wa wasu a cikin ikilisiya don su samu wartsakewa ta ruhaniya?
4 Ku Taimaka wa Wasu Su Samu Wartsakewa: Muna son mutane ma su samu wartsakewa. Shin akwai tsofaffin masu shela ko kuma wasu a cikin ikilisiyarku da suke bukatar taimako don su halarci taron gundumar? Za ka iya taimaka musu kuwa? (1 Yoh. 3:17, 18) Dattawa, musamman masu kula da rukunin hidima, su tabbata cewa masu shela sun samu taimakon da suke bukata.
5. Ta yaya za mu raba takardun gayyata na taron gunduma? (Duba akwatin da ke sama ma.)
5 Kamar yadda muka saba yi a dā, za mu yi kamfen na rarraba takardar gayyata zuwa taron gundumar makonni uku kafin taron. Ya kamata ikilisiyoyi su kafa maƙasudin rarraba dukan takardun gayyata da aka aika musu kuma su kammala yankin idan zai yiwu. Ku kawo takardun gayyatarku da suka rage zuwa wurin taron don ku yi wa’azi sa’ad da kuka samu zarafin yin hakan. Za a ba da ƙarin bayani game da wannan a tsarin ayyuka na ranar Jumma’a. Ku ba ’yan atenda takardun gayyatar da ba za ku iya yin amfani da su ba da zarar kun shiga majami’ar taron. Don Allah ku ajiye kofi ɗai-ɗai, tun da za ku yi amfani da ita a jawabin ƙarshe a ranar Lahadi.
6. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya nuna ɗabi’a mai kyau a taron gunduma?
6 Ɗabi’a Mai Kyau Tana Wartsakewa: A lokacin da mutane da yawa suna “son kansu” kuma ba sa kula da yadda wasu suke ji, yana da ban wartsakewa sosai mu kasance cikin ’yan’uwanmu Kiristoci waɗanda suke ƙoƙarin nuna ɗabi’a mai kyau! (2 Tim. 3:2) Muna nuna ɗabi’a mai kyau idan mun natsu sa’ad da muke shiga da kuma fita daga majami’ar taron, kuma idan muka adana wurin zama don waɗanda muke gida ɗaya tare ko waɗanda muke cikin mota tare da su ko waɗanda muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su yanzu. Ya dace mu bi ja-gorar mai kujerar sa’ad da ya ce mu nemi wurin zamanmu don mu saurari kaɗe-kaɗe. Za mu nuna ɗabi’a mai kyau idan mun saita wayarmu ko pagermu yadda ba zai damu kowa ba sa’ad da ake tsarin ayyuka. Muna kuma nuna ɗabi’a mai kyau idan ba ma yin taɗi ko aika saƙo ta waya ko yin ciye-ciye ko kuma yawace-yawace sa’ad da ake tsarin ayyukan.
7. Ta yaya za mu iya samun wartsakewa kuma mu sa wasu su yi hakan sa’ad da muke cuɗanya da ’yan’uwanmu?
7 Tarayya Mai Wartsakewa: Taron gunduma yana ba mu zarafi mai kyau na more haɗin kai mai wartsakewa da kuma ’yan’uwanci. (Zab. 133:1-3) Zai dace ku rifta zarafi don “buɗe zuciyarku” kuma ku haɗu da ’yan’uwa maza da mata da suka zo daga wasu ikilisiyoyi. (2 Kor. 6:13) Za ku iya ƙuduri cewa za ku san aƙalla mutum ko iyali guda a kowacce rana. Shaƙatawa na rana zai ba da zarafi mai kyau na yin hakan. Saboda haka zai dace ku kawo abincin da za ku ci da rana kuma ku ci a wurin taron don ku yi cuɗanya da ’yan’uwanku maimakon ku fita neman abinci a waje ko gidan abinci. Hakan zai iya sa a samu sababbin abokai nagari.
8. Me ya sa zai dace mu ba da kai don yin aiki a lokacin taron gunduma, kuma yaya za mu iya yin hakan?
8 Yin tsarkakkiyar hidima tare da ’yan’uwanmu tana ba da wartsakewa sosai! Za ku iya ba da kanku don taimaka wa wani sashe ko kuma taimaka sa’ad da ikilisiyarku za ta share majami’ar? (Zab. 110:3) Idan ba a riga an ba ka aikin da za ka yi ba, za ka iya tuntuɓar Sashen Hidimar Ba Da Kai a taron gundumar. Aikin da mutane da yawa suka saka hannu zai kasance mai sa farin ciki da kuma sauƙi.
9. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga ɗabi’armu da kuma adonmu a ranakun taron gundumar?
9 Ɗabi’armu Tana Wartsake Masu Kallonmu: Mu ’yan’uwa ne da suka halarci taron a dukan kwanaki ukun, ba a lokacin tsarin ayyukan kaɗai ba. Ya kamata waɗanda suke kallonmu sa’ad da muke garin da ake taron su ga bambanci mai kyau tsakanin Shaidu da waɗanda ba Shaidu ba. (1 Bit. 2:12) Ya kamata tufafinmu da kuma adonmu a majami’ar taron da masaukinmu da kuma gidan abinci su ɗaukaka Jehobah. (1 Tim. 2:9, 10) Waɗanda suke kallonmu za su iya sanin cewa mu Shaidun Jehobah ne, idan mun saka bajonmu. Hakan zai iya ba mu zarafin ba su ƙarin bayani game da taron gundumar da kuma yi musu wa’azi sosai.
10. Ta yaya za a iya tabbata cewa ma’aikatan hotal da gidan abinci sun samu ra’ayi mai kyau game da taronmu?
10 Ta yaya za mu iya ba da haɗin kai ga ma’aikatan masauki da kuma gidan dafa abinci? Bai kamata mu karɓi fiye da ɗakunan da za mu yi amfani da su ba, tun da yin hakan zai hana wasu su samu ɗakuna kuma za a kori abokan cinikin masu hotal ɗin. Idan ma’aikatan hotal ɗin sun shagala da aiki sa’ad da muke son mu karɓi ɗaki ko kuma mayar musu da makullinsu, ya kamata mu yi haƙuri kuma kada mu yi musu baƙar magana. (Kol. 4:6) Za mu iya ba da kyauta ga ma’aikatan da suka ɗauki jakarmu da share ɗakinmu da kuma yi mana wasu ayyuka.
11. Waɗanne labarai ne suka nuna yadda ɗabi’armu mai kyau take ba da shaida?
11 Ta yaya ɗabi’armu mai kyau a lokacin taron gunduma take shafar wasu? Wata jarida ta faɗa cewa wani manaja ɗin wani masaukin da Shaidu suke amfani da shi ya ce: “Mutanen suna da kirki sosai. Muna farin cikin marabtarsu kowacce shekara.” Wani mutum da ba Mashaidi ba ne ya ɓatar da walat ɗinsa a hotal da ’yan’uwan da suka halarci taro bara suka sauka. Sa’ad da aka mayar wa manajan walat ɗin babu abin da ya ɓace a ciki, sai manajan ya gaya wa mai shi: “Ka yi sa’a tun da yake wurin da Shaidun Jehobah suke taron gundumarsu bai da nisa daga nan, kuma su ne suka cika hotal ɗin nan. Da ba don hakan ba, wataƙila ba za ka taɓa ganin walat ɗin ba.”
12. Yayin da taron yake kusatowa, mene ne ya kamata ya zama maƙasudinmu, kuma me ya sa?
12 Taron gunduma na wannan shekarar yana daɗa kusatowa. An yi sa’o’i da yawa don shirya tsarin ayyukan kuma a sa wurin taron ya kasance mai wartsakewa. Ka sa ya zama maƙasudinka ka halarci dukan kwanaki uku na taron, kuma ka yi shirin more abin da Jehobah da kuma ƙungiyarsa suka shirya maka. Ka ƙuduri cewa za ka wartsake wasu da ɗabi’arka mai kyau da tarayya mai wartsakewa da kuma halin kirki. Kuma kai da wasu za ku ji kamar wani da ya halarci taron gunduma bara wanda ya rubuta, “Ban taɓa samun wartsakewa kamar wannan ba!”
[Bayanin da ke shafi na 1]
Kamar yadda muka saba yi a dā, za mu yi kamfen na rarraba takardar gayyata zuwa taron gundumar makonni uku kafin taron
[Bayanin da ke shafi na 3]
Ya kamata tufafinmu da kuma adonmu a majami’ar taron da masaukinmu da kuma gidan abinci su ɗaukaka Jehobah
[Bayanin da ke shafi na 4]
Ka ƙuduri cewa za ka wartsake wasu da ɗabi’arka mai kyau da tarayya mai wartsakewa da kuma halin kirki
[Akwati a shafi na 2-4]
Tunasarwa Game da Taron Gunduma na Shekara ta 2011
◼ Lokacin da Za a Soma Tsarin Ayyuka: Za a soma taron ne da ƙarfe 9:20 na safe a dukan kwanaki uku. Sa’ad da aka gabatar da kaɗe-kaɗe, ya kamata mu duka mu sami wurin zama don taron ya soma cikin daraja. Za a kammala tsarin ayyuka na ranar Juma’a da Asabar da ƙarfe 4:55 da yamma, kuma da ƙarfe 3:40 da yamma na ranar Lahadi.
◼ Ajiye Mota: A dukan wuraren taron gunduma, ’yan atenda za su taimaka wa mutane su ajiye motarsu. Don Allah ku ba su haɗin kai.—1 Kor. 14:40.
◼ Ajiye Wajen Zama: Za ku iya ajiye wajen zama ne kawai ga waɗanda kuke tafiya tare a cikin motarku da waɗanda kuke zama tare a gida ɗaya, da kuma waɗanda kuke nazarin Littafi Mai Tsarki da su yanzu.—1 Kor. 13:5.
◼ Abincin Rana: Don Allah ku kawo abincin da za ku ci da rana, maimakon ku fita waje don sayan abinci a lokacin shaƙatawa. Za ku iya yin amfani da abin zuba abinci ɗan ƙarami da za ku iya ajiyewa a ƙarƙashin kujera. Ba a yarda a kawo abin zuba abinci mai girma da kuma tambulan a wajen taron gundumar ba.
◼ Ba da Kyauta: Za mu iya nuna godiya ga shirye-shiryen da aka yi don gudanar da taron ta wajen ba da kyauta da son rai ga aiki na dukan duniya a Majami’ar Mulkinmu ko kuma a taron gunduma. Idan za ku ba da gudummawa ta hanyar cek a wurin taron, ku rubuta kalmomin nan biyu, “Watch Tower.”
◼ Haɗari da Jinyar Gaggawa: Idan aka sami jinyar gaggawa a wurin taro, don Allah ku sanar da ɗan atenda da ke kusa, wanda zai kai marar lafiyan zuwa Sashen Kula da Jinyar Gaggawa domin ƙwararrun ma’aikata masu jinyar gaggawa su duba irin matsalar kuma su ba da taimako.
◼ Magunguna: Idan kuna bukatar maganin da kuke sha a kai a kai, don Allah ku taho da naku, tun da ba za mu ba da wannan a wurin taron gundumar ba.
◼ Takalma: Don hana yin rauni, ya fi dacewa a zaɓi takalma masu kyau da ba su da tsini sosai da za su ƙyale mutum ya yi tafiya da sauƙi.
◼ Wasan Kwaikwayo: Ba zai nuna ƙauna ba idan ’yan’uwa mata suka ɗaura babban ɗan kwali a ranar Lahadi da rana ba sa’ad da ake nuna wasan kwaikwayo, domin hakan zai kāre waɗanda ke zaune a baya. Waɗanda suke zaune a bayansu su samu ganin abin da ke faruwa a dakalin yin magana, musamman a yanzu da ake amfani da Majami’un Taro da kuma Majami’un Mulki da ake faɗaɗawa.—Filib. 2:4.
◼ Kayan Ƙamshi: Zai zama abin alheri idan muka rage kayan ƙamshi da zai dami mutanen da ke da ciwon ƙirji ko makamancin hakan.—1 Kor. 10:24.
◼ Fom Ɗin Please Follow Up (S-43): Ku yi amfani da fam ɗin nan Please Follow Up (S-43) don ba da bayani game da wa’azin da kuka yi wa mai marmari a lokacin taron. Masu shela su taho da fam ɗin guda ɗaya ko biyu zuwa wurin taron. Za ku iya ba da fam ɗin ga Sashen Littafi don su yi aiki a kai ko kuma ku ba sakataren ikilisiyarku sa’ad da kuka koma gida.—Duba Hidimarmu Ta Mulki ta Nuwamba 2009, shafi na 4.
◼ Gidan Abinci da Masu Sayar da Abubuwa a Waje: Ku ɗaukaka sunan Jehobah ta halinku mai kyau a gidajen abinci. Ba zai dace ba mu riƙa zuwa wajen masu abinci da masu talla a lokacin da ake taron. Idan mutum yana son ya sayi wani abu, zai dace ya yi hakan kafin a soma taron ko kuma bayan an kammala taron.
◼ Masaukai: (1) Ku nuna ɗiyar ruhu sa’ad da kuke karɓan masaukinku sa’ad da kuka isa wurin taron. (2) Kada ku zauna a ɗakunan da sashen Kula da Ɗakuna bai sa ku a ciki ba. Ku ba da haɗin kai ta wajen sauka a inda aka sa ku. (3) Kada ku yi dare a waje ko kuma ku kwana a ɗakunan da aka keɓe wa mata idan kai namiji ne, mace kada ta kwana inda maza suke. (4) Idan kuka sami matsala da wurin kwanan da aka ba ku, ku je ku sanar da sashen da ke kula da masauki nan da nan a wajen taron. (5) Idan a hotal kuka sauka, ku ba da haɗin kai ga masu kula da hotal ɗin. (6) Ku yi dahuwa a wuraren da aka amince da yin hakan ne kawai. (7) Kada ku yi dahuwa a lokacin da ake yin taro domin hakan ba ya nuna daraja ga abubuwa na ruhaniya.—Luk 10:38-42.
◼ Hidimar Ba da Kai: Farin cikin da muke samu don halartar taron gunduma zai ƙaru idan mun ba da kanmu don taimaka a aikin da ya kamata. (A. M. 20:35) Ya kamata duk wanda yake son yin hakan ya je Sashen Kula da Hidima a wurin taron gundumar. Yara da ba su kai shekara sha shida ba tukun za su iya ba da kansu ta yin aiki tare da iyayensu ko kuma wani babba da sashen suka zaɓa.
[Akwati a shafi na 2]
Ta Yaya Za Mu Rarraba Takardar Gayyatar?
Ya kamata mu taƙaita kalamanmu don mu samu mu rarraba takardun a yankin baki ɗaya. Za mu iya cewa: “Barka dai. Muna rarraba takardar gayyata a dukan duniya. Ga kofi guda. Za ka samu ƙarin bayani a cikin takardar gayyatar.” An wallafa takardar don ta jawo hankalin masu gida, saboda haka, ka miƙa wa masu gida takardar a hanyar da za su ga hoton da ke gaban takardar. Ka kasance da daɗaɗawa. Ku rarraba takardun gayyatar tare da mujallu a ƙarshen mako, idan hakan ya dace.