Za A Rarraba Bisharar Mulki ta 38 a Watan Janairu!
1. Mene ne mutane suka kasa sani game da matattu, kuma me za a yi a watan Janairu da zai taimaka musu?
1 Mutuwa rigar kowa ce, ko da wane addini ne mutumin yake bi. (1 Kor. 15:26) Mutane da yawa ba su san inda matattu suke ba kuma suna tunani ko zai yiwu su sake ganinsu. Saboda haka, ’yan’uwa a duk faɗin duniya za su yi wata guda suna rarraba Bisharar Mulki ta 38 mai jigon nan Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa? Za a soma wannan kamfen na musamman a ranar 1 ga watan Janairu. Bayan an gama wannan kamfen, za a ci gaba da yin amfani da Bisharar Mulki ta 38 a matsayin warƙa sa’ad da ake wa’azi.
2. Yaya aka tsara Bisharar Mulki ta 38?
2 Yadda Aka Tsara Ta: An tsara Bisharar Mulki ta 38 a hanyar da idan ka ninka ta, za ka iya ganin bangon gaban da ke ɗauke da jigo mai ban sha’awa tare da kalmomin nan, “Mece ce amsarka . . . e? a’a? ko wataƙila?” Sa’ad da mai karatu ya buɗe wannan Bisharar Mulki, zai ga amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da a kan tambayar da kuma abin da zai iya mora idan ya gaskata da alkawuran Littafi Mai Tsarki. Zai kuma ga dalilan da suka sa zai iya gaskatawa da Littafi Mai Tsarki. A bangon baya na wannan Bisharar Mulki, an rubuta wata tambaya da ya kamata mutumin ya yi tunani a kai kuma an gayyace shi ya yi ƙoƙari ya sami ƙarin bayani.
3. Yaya za a rarraba Bisharar Mulki ta 38?
3 Yadda Za A Rarraba Ta: Za a yi wannan kamfen kamar yadda aka saba yin kamfen na gayyatar mutane zuwa taron Tuna mutuwar Yesu da kuma taron gunduma. Dattawa za su ba da ja-gora a kan yadda za a rarraba ta a dukan yankunan ikilisiyar bisa ga wasiƙar 1 ga Afrilu, 2013 da aka aika musu. Ikilisiyoyi da suke da ƙaramin yanki suna iya taimaka wa ikilisiyoyi da suke da babban yanki. Sa’ad da kuke karɓan Bisharar Mulki ta 38, zai dace ku karɓi daidai waɗanda za ku iya rarrabawa a cikin mako guda kawai. Bayan an gama rarraba Bisharar Mulki gida-gida, za a iya rarraba ta a duk inda jama’a suke a yankin. Idan an gama rarraba dukansu kafin ƙarshen watan, sai a ba da littattafai da ya kamata a rarraba a watan Fabrairu. A Asabar ta farko, za mu yi wannan kamfen na musamman maimakon soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. A ƙarshen mako, za mu iya ba da mujallu a duk lokacin da ya dace. Shin za ku tsara ayyukanku da kyau don ku yi wannan kamfen na musamman tare da ’yan’uwa?