Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 10/13 p. 4
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 10/13 p. 4

Gabatarwa

Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Nuwamba

“Muna ziyartar mutane a yankinku a yau. Mutane da yawa sun ce ba abin da ya fi sa su baƙin ciki kamar mutuwar wani da suke ƙauna. Kai ma ka taɓa jin hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Akwai wani abin da na karanta a nan da ya ƙarfafa ni sosai.” Ka nuna masa bangon baya na Hasumiyar Tsaro na Nuwamba-Disamba. Ku tattauna sakin layi na farko a ƙarƙashin tambaya ta ɗaya da kuma aƙalla nassi guda da aka rubuta a wurin. Ka ba shi Hasumiyar Tsaro da Awake!, kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna sakin layi na gaba.

Hasumiyar Tsaro Nuwamba–Disamba

“Muna ziyartar mutane don mu ƙarfafa su su riƙa karanta Littafi Mai Tsarki. Mun san cewa wasu suna son karanta Littafi Mai Tsarki, amma wasu ba sa sha’awarsa. Kai fa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga wani abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da kansa. [Karanta 1 Tasalonikawa 2:13.] Na san za ka yarda da ni cewa idan Allah ne mawallafin Littafi Mai Tsarki da gaske, zai dace mu karanta shi. Wannan mujallar ta ɗan tattauna abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma dalilin da ya sa ya kamata mu karanta shi.”

Awake! Nuwamba

“Muna ziyartar ku a yau domin mutane da yawa suna damuwa cewa ba a cika ɗaukan ɗabi’u masu kyau da muhimmanci kuma ba. Shin kana ganin zamani ne ya jawo hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa halayen mutane za su canja. [Karanta 2 Timotawus 3:1-5.] Wannan mujallar ta bayyana abin da ya sa za mu iya amincewa da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki game da ɗabi’a.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba