Gabatarwa
Hasumiyar Tsaro Satumba–Oktoba
“Mutane da yawa suna mamaki ko zai yiwu mu faranta wa Allah rai duk da kasawarmu da kuma ajizancinmu. Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa. Karanta Misalai 27:11.] Talifin da ya soma daga shafi na 12 ya ba da misalan mutanen da suka faranta wa Allah rai duk da kasawarsu.”
Awake! Oktoba
“Mun kawo muku ziyara ne don mutane da yawa suna mamaki a kan dalilin da ya sa Allah ya bar mu mu riƙa shan wahala. A ganin ka ya dace mu yi irin wannan tunanin kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ayuba ma ya taɓa so ya yi wa Allah tambaya. [Karanta Ayuba 23:3-5.] Wannan mujallar ta tattauna tambayoyi uku da mutane za su so su yi wa Allah idan sun sami dama da kuma amsoshi masu gamsarwa da Littafi Mai Tsarki ya bayar.”