DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 110-118
“Me Zan Bayar ga Jehobah?”
Marubucin zabura ya gode wa Jehobah sosai don ya cece shi daga “igiyoyin mutuwa.” (Za 116:3) Ya tsai da shawarar bin dokokin Jehobah da kuma cika alkawuran da ya yi don ya nuna godiyarsa gare shi.
Mene ne Jehobah ya yi mini wannan makon da nake so in gode masa?
Yaya zan nuna godiyata ga Jehobah?