DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ISHAYA 11-16
Sanin Jehobah Zai Cika Duniya
11:6-9
Yadda wannan annabcin ya cika a kan Isra’ilawa
Isra’ilawa ba su ji tsoron namomin daji ko mugayen mutane sa’ad da suke dawowa daga bauta a Babila ko kuma sa’ad da suke ƙasarsu ba.—Ezr 8:21, 22
Yadda wannan annabcin yake cika a zamaninmu
Sanin Jehobah ya canja halayen mutane. Mutanen da ke son faɗa sosai a dā sun zama masu son kwanciyar hankali. Sanin Allah ya kuma sa mu kasance cikin yanayin salama a ƙungiyar Jehobah
Yadda wannan annabcin zai cika a nan gaba
Duniya gabaki ɗaya za ta zama aljanna kuma salama za ka kasance a ko’ina yadda Allah ya so tun asali. ‘Yan Adam da kuma dabbobi ba za su tayar da hankula ba
Sanin Allah ya sa Bulus ya canja salon rayuwarsa
Kafin Saul ya zama Bulus, yana da mugayen halaye kamar dabba.—1Ti 1:13
Amma sanin Allah ya sa ya canja halayensa.—Kol 3:8-10