RAYUWAR KIRISTA
Ku Sa Yaranku Su Yi Imani da Wanzuwar Mahalicci Sosai
Halittu suna ɗaukaka Jehobah. (Za 19:1-4; 139:14) Amma duniyar Shaiɗan tana ƙaryata wanzuwar Allah. (Ro 1:18-25) Ta yaya za ka taimaka wa yaranka kada su kasance da irin waɗannan ra’ayoyin a zuciyarsu? Ka taimaka musu tun suna ƙanana su yi imani cewa Jehobah ya wanzu kuma ya damu da su sosai. (2Ko 10:4, 5; Afi 6:16) Ka san ra’ayinsu game da abin da ake koya musu a makaranta kuma ka yi amfani da littattafan da za su ratsa zuciyarsu.—Mis 20:5; Yaƙ 1:19.
KU KALLI BIDIYON NAN ABIN DA TSARARKU SUKA CE—YIN IMANI DA ALLAH, SAI KA YI TAMBAYOYIN NAN:
Wace ƙarya ce ake yawan yi game da wanzuwar Allah?
Mene ne ake koyarwa a makarantarku?
Me ya sa kake da tabbaci cewa Jehobah ya wanzu?
Ta yaya za ka iya taimaka wa wani ya gaskata cewa Allah ne mahalicci?