DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | IRMIYA 25-28
Ka Yi Ƙarfin Hali Kamar Irmiya
Irmiya ya yi gargaɗi cewa za a halaka Urushalima kamar yadda aka halaka Shiloh
26:6
- Sanduƙin alkawari yana nuna cewa Jehobah na tare da Isra’ilawa, kuma a dā ana ajiye shi a Shiloh 
- Jehobah ya ƙyale Filistiyawa su kwace Sanduƙin Alkawarin kuma tun daga lokacin ba a sake ajiye shi a Shiloh ba 
Firistoci da annabawa da kuma dukan mutanen sun yi barazanar kashe Irmiya
26:8, 9, 12, 13
- Mutanen sun kama Irmiya don annabcin da ya yi game da Urushalima da kuma haikalin 
- Amma Irmiya bai karaya ba 
Jehobah ya kāre Irmiya
26:16, 24
- Irmiya ya ci gaba da kasancewa da gaba gaɗi kuma Jehobah bai yi watsi da shi ba 
- Allah ya sa Ahikam mai ƙarfin hali ya kāre Irmiya 
Da taimakon Jehobah, Irmiya ya yi shekara 40 yana shelar saƙon hukunci