RAYUWAR KIRISTA
Me Ya Sa Kake Son Bauta ta Gaskiya?
Wahayin Ezekiyel game da haikali ya ƙarfafa Isra’ilawan da suke Babila domin ya sa sun kasance da bege cewa za a maido da bauta ta gaskiya. A zamaninmu, an ɗaukaka bauta ta gaskiya “bisa kan tuddai” kuma muna cikin waɗanda suke gangarowa wurinta. (Ish 2:2) Kana bimbini a kan gatan da kake da shi na koya game da Jehobah da kuma bauta masa?
ALBARKAR DA MUKE SAMU DON BAUTA TA GASKIYA:
Muna da tanadodin da suke sa mu san amsoshin muhimman tambayoyi na rayuwa, da ƙa’idodin da ya kamata mu bi, kuma suna sa mu kasance da bege.—Ish 48:17, 18; 65:13; Ro 15:4
Muna da ’yan’uwa masu ƙauna a faɗin duniya.—Za 133:1; Yoh 13:35
Muna da gatan yin wa’azin bishara.—A. M. 20:35; 1Ko 3:9
Muna da ‘salama ta Allah’ wadda take taimaka mana mu jimre da wahala.—Fib 4:6, 7
Muna da lamiri mai kyau.—2Ti 1:3
Muna da dangantaka mai kyau da Jehobah.—Za 25:14
A waɗanne hanyoyi ne zan nuna cewa ina son bauta ta gaskiya?