DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | EZEKIYEL 46-48
Albarkar da Isra’ilawa Za Su Mora Bayan Sun Koma Ƙasarsu
Wahayin Ezekiyel game da haikali ya ƙarfafa Isra’ilawan da suke zama bauta kuma ya sa sun ƙara gaskata da annabcin da aka yi cewa za su koma ƙasarsu. Mutanen da Jehobah ya albarkace su za su ɗauki bauta ta gaskiya da muhimmanci sosai.
A wahayin, an yi alkawari cewa za su kasance da tsari da haɗin kai da kuma kwanciyar hankali
47:7-14
Ƙasar za ta yi albarka sosai
Kowace iyali za ta sami gādo
Kafin a ba mutanen filin, za a “keɓe” wani fili na musamman a matsayin “hadaya” ga Jehobah
48:9, 10
Ta yaya zan nuna cewa bauta wa Jehobah ce ta fi muhimmanci a rayuwata? (w06 4/15 27-28 sakin layi na 13-14)