DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | HOSIYA 8-14
Ka Yi Iya Ƙoƙarinka a Bautar Jehobah
14:2, 4, 9
Idan ka yi iya ƙoƙarinka a hidimar Jehobah, hakan zai sa shi farin ciki kuma kai ma za ka amfana
DANGANTAKARKA DA JEHOBAH
Ka ba Jehobah hadaya ta yabo
Jehobah zai gafarta zunubanka, ya amince da kai kuma ka zama abokinsa
Ka shaida yadda biyayya ga Jehobah take kawo albarka, kuma hakan zai sa ka ci gaba da bauta masa da dukan ƙarfinka
A wace hanya ce zan bauta wa Jehobah da dukan ƙarfina?