Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb18 Fabrairu p. 4
  • “Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka”
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Makamantan Littattafai
  • Mene ne Ake Nufi da ‘Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka’?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ka Girmama Wanda Ya Cancanci Girmamawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Me Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Kula da Iyaye da Suka Tsufa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
mwb18 Fabrairu p. 4

RAYUWAR KIRISTA

“Ka Girmama Mahaifinka da Mahaifiyarka”

Sa’ad da Yesu yake duniya, ya nanata muhimmancin umurnin nan: “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.” (Fit 20:12; Mt 15:​4, Littafi Mai Tsarki) Hakika, Yesu bai ji kunyar faɗan haka ba domin ya yi wa iyayensa “biyayya” sa’ad da yake matashi. (Lu 2:51) Da ya girma, ya nemi wanda zai kula da mahaifiyarsa bayan ya mutu. ​—⁠Yoh 19:​26, 27.

A yau ma, Kiristoci matasa suna girmama iyayensu idan suna ma iyayensu biyayya kuma suna musu magana da daraja. Kuma umurnin da aka ba mu na girmama iyayenmu ba shi da iyaka. Ko da iyayenmu sun tsufa sosai, ya kamata mu ci gaba da girmama su ta wurin saurarar shawararsu. (Mis 23:22) Ƙari ga haka, muna daraja iyayenmu da suka tsufa ta wajen kula da su da kuma taimaka musu. (1Ti 5:8) Ko da mu matasa ne ko manya, ya kamata mu riƙa tattaunawa da kyau da iyayenmu domin hakan zai nuna cewa muna girmama su.

KU KALLI BIDIYON ZANEN ALLON NAN YADDA YA KAMATA KA YI MAGANA DA IYAYENKA SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Me ya sa zai iya yi maka wuya ka tattauna da iyayenka?

  • Ta yaya za ka girmama iyayenka sa’ad da kake magana da su?

    Wani yaro ya rubuta wasika ma iyayensa, yana tattauna da iyayensa, yana buga wasan kwallo da babansa
  • Me ya sa yake da kyau ka tattauna da iyayenka? (Mis 15:⁠22)

    Iyaye suna taimaka ma yaronsu don ya iya magance matsaloli da zai iya fuskanta a nan gaba

    Idan kana tattaunawa da iyayenka, hakan zai sa ka yi nasara a rayuwa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba