RAYUWAR KIRISTA
Me Za Ku Yi Idan Kuka Fuskanci Yanayi Mai Wuya?
Muna bukatar mu kasance da bangaskiya kuma mu dogara ga Jehobah. Alal misali, bangaskiya za ta taimaka mana mu dogara ga Jehobah cewa zai taimaka da kuma kula da mu. (Za 23:1, 4; 78:22) Yayin da ƙarshen duniyar nan ya kusa, Shaiɗan zai kai mana hari fiye da yadda yake yi a dā. (R. Yar 12:12) Mene ne zai taimaka mana?
KU KALLI BIDIYON NAN ME ZA KU YI IDAN KUKA FUSKANCI YANAYI MAI WUYA? SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
Ta yaya muke kama da ‘itacen’ da ke littafin Irmiya 17:8?
Mene ne ɗaya daga cikin “zafin rana” da za mu iya fuskanta?
Me ya faru da ‘itacen’ kuma me ya sa?
Mene ne Shaiɗan yake so ya gurɓata?
Ta yaya muke kama da waɗanda suka saba shiga jirgin sama?
Me ya sa yake da kyau mu ci gaba da amincewa da bawan nan mai aminci, kuma ta yaya za a gwada bangaskiyarmu?
Me ya sa ya kamata mu ci gaba da bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ko da mutane suna mana ba’a?