DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Kasance da Tsabta a Ɗabi’arku
Jehobah yana so halinmu ya bambanta da na mutanen duniya (L.Fi 18:3; w19.06 28 sakin layi na 1)
Jehobah ba ya so mutum ya yi jima’i da ’yar’uwarsa ko mace ta yi jima’i da ɗan’uwanta ko jima’i ta jinsi ɗaya ko kuma jima’i da dabbobi (L.Fi 18:6, 22, 23; w17.02 20 sakin layi na 13)
Jehobah zai hallaka mutane masu halaye mara tsabta a duniya (L.Fi 18:24, 25; K. Ma 2:22; w14 9/1 7 sakin layi na 2)
Shaiɗan ba ya so mu shiga aljanna. Amma ƙa’idodin Jehobah za su kāre mu daga tarkunan Shaiɗan.
Ta yaya za mu nuna wa Jehobah cewa mun tsani lalata?