Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Maris p. 7
  • Yin Tambayoyi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yin Tambayoyi
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Ratsa Zukatan Mutane
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Yin Amfani da Kalmar Allah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Ka Amince da Taimakon Jehobah ta Wurin Yin Addu’a
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Ka Taimaka wa Dalibanka Su Zama Aminan Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Maris p. 7
Wasu ma’aurata Shaidu suna ba wani mutum warka sa’ad da suke wa’azi da amalanke a wani tashar jirgin kasa.

KA YI WA’AZI DA KWAZO | YADDA ZA KA DAƊA JIN DAƊIN WA’AZI

Yin Tambayoyi

Jehobah, “Allah mai farin ciki” yana so mu ji daɗin wa’azi. (1Ti 1:​11, New World Translation) Za mu daɗa jin daɗin hidimarmu idan muka kyautata yadda muke wa’azi. Yin tambayoyi zai sa mutane su so saƙonmu kuma hakan hanya ce mai kyau na soma tattaunawa da mutane. Tambayoyi sukan sa mutane su yi tunani a kan batutuwa. (Mt 22:​41-45) Idan muka yi tambayoyi kuma muka saurara da kyau, yana kamar muna gaya ma ɗalibinmu cewa, ‘Kana da muhimmanci a gare ni.’ (Yaƙ 1:19) Amsar da mutumin ya bayar za ta taimaka mana mu san batun da za mu tattauna da shi.

KU KALLI BIDIYON NAN ZA KU JI DAƊIN ALMAJIRTARWA IDAN KUN INGANTA YADDA KUKE WA’AZI​—KU RIƘA YIN TAMBAYOYI, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan ‘Za Ku Ji Dadin Almajirtarwa Idan Kun Inganta Yadda Kuke Wa’azi​—Ku Rika Yin Tambayoyi.’ Rose ta ce wata tsohuwa ta zauna a wurin zamanta a jirgin kasa.

    Waɗanne halaye masu kyau ne Rose ta nuna?

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan ‘Za Ku Ji Dadin Almajirtarwa Idan Kun Inganta Yadda Kuke Wa’azi​—Ku Rika Yin Tambayoyi.’ Anita ta mika hannu don su gaisa da Rose kuma ta gaya mata sunanta.

    Ta yaya Anita ta nuna cewa ta damu da Rose?

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan ‘Za Ku Ji Dadin Almajirtarwa Idan Kun Inganta Yadda Kuke Wa’azi​—Ku Rika Yin Tambayoyi.’ Rose ta amsa tambayar da Anita ta yi mata.

    Ta yaya Anita ta yi tambayoyi don ta ƙara jan hankalin Rose ga wa’azinmu?

  • Wani hoto da aka dauko daga bidiyon nan ‘Za Ku Ji Dadin Almajirtarwa Idan Kun Inganta Yadda Kuke Wa’azi​—Ku Rika Yin Tambayoyi.’ Anita ta yi wa Rose tambaya bayan da suka karanta wani nassi.

    Ta yaya Anita ta yi amfani da tambayoyi don ta sa Rose ta yi tunani kuma ta fahimci batun?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba