DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Jehobah Allah Ne Mai Yin La’akari da Yanayinmu
Sama’ila ya ɗauka cewa Eli ne yake kiransa (1Sam 3:4-7; w18.09 24 sakin layi na 3)
Jehobah ya sa Sama’ila ya san cewa Shi ne yake kiransa (1Sam 3:8, 9)
Jehobah ya yi la’akari da yanayin Sama’ila (1Sam 3:15-18; w18.09 24 sakin layi na 4)
KA TAMBAYI KANKA: ‘A Waɗanne hanyoyi ne zan riƙa la’akari da yanayoyin manya da yara? Ta yaya zan riƙa la’akari da yanayin ’yan’uwa a ikilisiya?’