DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Sulemanu Ya Yi Addu’a da Dukan Zuciyarsa
Sa’ad da ake keɓe haikalin, Sulemanu ya yi addu’a a gaban mutanen da dukan zuciyarsa (1Sar 8:22; w09 11/15 9 sakin layi na 9-10)
Sulemanu ya yabi Jehobah kuma bai sa mutane su mai da hankali ga abin da ya cim ma ba (1Sar 8:23, 24)
Sulemanu ya kasance da tawali’u sa’ad da yake addu’a (1Sar 8:27; w99 2/1 15 sakin layi na 7-8)
Ya kamata waɗanda suke addu’a ga jama’a su yi koyi da Sulemanu. Zai dace mu mai da hankali ga yadda Jehobah yake ɗaukan abubuwan da muke faɗa a addu’ar, maimakon mu yi ƙoƙarin burge mutane.