DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ku Yabi Jehobah don Hikimarsa
Jehobah ya ba wa Sulemanu hikima sosai (1Sar 10:1-3; w99-E 7/1 30 sakin layi na 6)
Sarauniyar Sheba ta yi mamakin irin hikimar da Jehobah ya ba wa Sulemanu (1Sar 10:4, 5; w99-E 11/1 20 sakin layi na 6)
Sarauniyar Sheba ta yabi Jehobah don yadda ya naɗa Sulemanu ya zama sarki (1Sar 10:6-9; w99-E 7/1 30-31)
Kamar sarauniyar Sheba, za mu iya nuna godiya don hikimar da Jehobah yake bayarwa. Ta yaya za mu yi hakan? Hanya ɗaya ita ce, ta wajen bin koyarwar Yesu da kuma yin iya ƙoƙari mu bi misalinsa a rayuwarmu. (Mt 12:42; 1Bi 2:21) Wata hanya kuma ita ce, taimaka wa mutane su sami hikimar Allah sa’ad da muke wa’azi.