Sarauniya Sheba ta ziyarci fadar Sarki Sulemanu
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Ta Nuna Tana Daraja Hikima
Sarauniyar Sheba ta yi tafiya mai nisa da kuma wuya don ta ga Sulemanu (2Tar 9:1, 2; w99-E 11/1 20 sakin layi na 4; w99-E 7/1 30 sakin layi na 4-5)
Hikimar Sulemanu da arzikinsa sun sa ta riƙe baki da mamaki (2Tar 9:3, 4; w99-E 7/1 30-31; ka duba hoton shafin farko)
Abin da ta gani ya sa ta yabi Jehobah (2Tar 9:7, 8; bm sashe na 10, sakin layi na 5)
Sarauniyar Sheba tana son hikima sosai har ta yi sadaukarwa sosai don ta samu.
KA TAMBAYI KANKA, ‘Ina a shirye in nemi hikima kamar yadda zan nemi dukiya da take a ɓoye?’—K. Ma 2:1-6.