DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Zai Dace Mu Gamsu da Abin da Muke da Shi Kuma Mu Zama Masu Sauƙin Kai
Annabin Allah ya ƙi ya karɓi kyaututtukan da Jeroboam ya ba shi (1Sar 13:7-10; w08 8/15 8 sakin layi na 4)
Daga baya, annabin ya yi wa Jehobah rashin biyayya (1Sar 13:14-19; w08 8/15 11 sakin layi na 15)
Rashin biyayya da annabin ya yi, ya jawo mummunar sakamako (1Sar 13:20-22; w08 8/15 10 sakin layi na 10)
Idan mun gamsu da abin da muke da shi kuma muka nemi ja-gorancin Jehobah sa’ad da muke so mu yanke shawarwari, hakan zai sa mu guji matsaloli da yawa.—1Ti 6:8-10.
KA TAMBAYI KANKA: ‘Ta yaya zan nuna na gamsu da abubuwan biyan bukata da nake da su? Ta yaya zan nuna sauƙin kai sa’ad da nake yanke shawarwari?’—K. Ma 3:5; 11:2.