RAYUWAR KIRISTA
Ku Haƙura da Abin da Kuke da Shi
Idan mu talakawa ne, hakan zai iya sa a jarraba mu mu yi abin da zai ɓata dagantakarmu da Allah. Alal misali, za a iya ba mu aikin da za mu sami kuɗi sosai amma hakan zai iya sa bauta wa Allah ya zama mana da wuya. Don haka, yin tunani a kan abin da ke Ibraniyawa 13:5 zai taimaka mana.
“Ku yi nesa da halin son kuɗi”
Ku yi adduꞌa, sai ku yi tunani a kan irin muhimmancin da kuɗi yake da shi a gare ku. Ku yi tunanin a kan irin misalin da kuke kafa wa yaranku.—g-E 9/15 6.
“Ku kuma kasance da kwanciyar rai da abin da kuke da shi”
Ku kasance da raꞌayin da ya dace game da bukatunku.—w16.07 7 sakin layi na 1-2.
“Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba”
Ku gaskata cewa Jehobah zai taimaka muku ku sami abin biyan bukata idan kuka sa Mulkin Allah farko a rayuwarku.—w14 4/15 21 sakin layi na 17.
KU KALLI BIDIYON NAN YADDA ꞌYANꞌUWANMU SUKE MORE SALAMA DUK DA TALAUCI, SAI KU AMSA TAMBAYA TA GABA:
Me muka koya daga labarin Miguel Novoa?